Yau za a fara bukukuwan cika shekara 40 naAku-Uka na Wukari
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Yau za a fara bukukuwan cika shekara 40 naAku-Uka na Wukari

Yau Juma’a ce za a fara bukukuwan cika shekara 40 a gadon sarauta na Aku-Uka na Wukari kuma Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jihar Taraba, Malam Shekarau Angyu Masa Ibi Kubyo II.
Wata sanarwa dauke da sanya hannun Shugaban Kwamitin Shirye-Shiryen bikin, Mai martaba Andoma na Doma Alhaji Ahmadu Aliyu Oga Onawo ta ce, bikin wanda za fara da misalin karfe 9:00 na safe a Dandalin Aku-Uka da ke Jami’ar Kwararrafa a Wukari Jihar Taraba, ana sa ran Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ne zai kasance Babban Bako.
Sauran manyan baki sun hada da daukacin gwamnonin jihohin Arewa, yayin da Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar zai shugabancin bikin. Mai martaba Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ne zai kasance uban biki yayin da Gwamnan Jihar Taraba Mista Darius Ishaku zai kasance mai masaukin baki.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited