Asirin lauyan bogi ya tuno a kotu
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Asirin lauyan bogi ya tuno a kotu

A ranar Litinin da ta gabata ce asirin wani lauyan bogi da ake kira da Easy Kurna ya tonu a daidai lokacin da yake kare wadansu mutane a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kurna a karamar Hukumar Fagge da ke Jihar Kano.
Wani lauya makwabcin lauyan bogin ne ya shaida wa alkalin kotun cewa Easy Kurna ba lauya ne na gaskiya ba ne, kuma nan take Alkalin Kotun Mai shari’a Salisu Muhammad ya yi wa lauyan bogin tambayoyi inda ya gamsu cewa lauyan bogin ne, kuma ya umarci ’yan sanda su gurfanar da shi gaban wata kotun kan wannan zargi.
Wani lauya da Aminiya ta zanta da shi a harabar kotun da ya nemi a boye sunansa ya nuna mamaki kan karfin halin lauyan bogi Easy Kurna. “Na yi mamakin wannan abu, saboda mun sha haduwa da shi a kotuna daban-daban. Mun hadu da shi a wata kotu a Gwagwarwa mun hadu a nan kotun Kurna kuma mun hadu da shi a kotun Nomanslan. Ina yin hulda da shi kamar yadda nake yi da sauran lauyoyi abokan aikina. Ban taba tunanin ba lauya ne na gaskiya,” inji shi.
Washegari Talata ’yan sandan sun gurfanar da lauyan bogin a gaban Kotun Majistare ta Filin Jiragen saman na Kano. Kuma Aminiya ta gano cewa a wannan kotu da aka gurfanar da lauyan bogin yana da shari’o’i uku da yake karewa, don haka lokacin da aka karanta masa takardar tuhuma bai musanta laifin da ake zarginsa da shi ba na yin sojan gona.
Alkalin Kotun Mai shari’a Talatu Makama ta bayar da umarnin sakaya lauyan bogin a kurkuku zuwa yau Juma’a don yanke masa hukunci.
A wani labarin kungiyar Lauyoyi ta kasa reshen Jihar Kano ta nesanta kanta da lauyan bogin inda Sakataren kungiyar Barista Sagir Sulaiman Gezawa ya ce kungiyar za ta nemi hakkinta a gaban shari’a game da bata mata suna da lauyan bogin ya yi.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited