Tuggun tagiya
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Tuggun tagiya

dimbin Haurobiyan da ke birnin Dabo inda ba a dabo, an yi musu wala-wala da yawon dara, a majigin jar tagiya, inda Gwamna Gwarangwam Gandun-aiki ya yi karon batta da tsohon Gwamna Gwaramgwam Mai-kwarankwatsa aiki. A wannan karon dai kowa ya ga wallen Marsa da Daushe goriya ’yan ujile, inda ’yan adawa suka fasko jirgin su a tsakar rana suna takun saka.
Wannan majigi da makarantarmu ta dodanni ke nusar da mu a farfajiyar Dodorido da ke Amintacciyar jaridar Haurobiya sabon shiri ne da aka nuna wa duniya kwanan nan. Mun dai fasko cewa, takun sakar mahukuntan ya raba kan ’ya’yan jam’iyya mai maganin zogi da radadin ciwon kururungu. Batun wannan gumurzu ba sabon al’amari ba ne a kafafen yada kwakwazo, tunda mun ji, mun gani a akwatunan magana da mai hoto, har ma da mujallu da makalu; kai hatta masu mu’amala da kafafen giza-gizan sadarwa, musamman shafukan Fuskantar-bokoko da Tukin Tuwon-titi a mashakatar lilo da tsallake-tsalleken na’ura mai kwanya.
Mafi yawan abin da aka fi ruwaitowa, musamman a akwatin magana mai jini, shi ne an fara turka-turkar gumurzun ne tsakanin jiga-jigan jagorancin al’umma a wajen ta’aziyyar mahaifiyar Gwamnan Jihar Tumbin-giwa mai ci, inda mai kwarankwatsintsiya ya jijjiga ’yan jagaliya, su kuwa suka yi wa Gandun aiki aika-aika, ta hanyar suka da bursatsen maganganu, musamman inda suka nuna fifikon gwarzon su a kan gwamna mai ci yanzu.
Batu na ingarman kwangiri, shi ne, tun lokacin da tsohon gwamna ya mika ragama a hannun abokin tafiyarsa a wasan Samson-siya-siya, wajen gudanar da tsarin dama-dama-da-kurda-kurdar siyasa, aka zare makamai a yayin raba mukamai; wutar da ta ci gaba ruruwar har zuwa lokacin da aka yi wa Gwamna Gandun aiki rashi.
Ko ma dai mene ne ya haifar wannan takaddama tsakanin wadannan jiga-jigan jigata talakawa, ni dai ina ganin “YADDA dILLIN TAKAN YI dILLIN, HAKA MA dILLIN TAKAN dILLIN.” Kun ga ke nan idan mu ne ’yan dugwi-dugwi, sai mu ce ‘yadda kaza takan yi kwan nan, haka ma kwan nan yakan yi kaza. Ko kuma a karairaye-karairayen maganganun Malam mai yaren Hau-hau wajen hawan sa, ba tare da sa-in-sa ba, cewa: “Babu kira me ya ci gawayi?”
Masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a wannan katafariyar makaranta, na sha nusar da mu cewa, akwai bukatar lallai jigo a jagorancin al’umma  ya kasance mai sadaukar da kai don tabbatar da adala da kawar da juhala, sabanin yadda a yau muke da jam’in jiga-jigan jigata jama’a, wadanda masalahar kan su kawai suka sani, amma ba tsilli-tsillin matsalolin da suka addabi al’umma ba.
Ganin irin wannan badakala da jagororin al’umma suka tsuwurwurta a birnin Dabo, lallai kada mu bari su yi mana dabo, inda ma har suka jajirce kamat aya yi talakawa su yi musu kabo da adabo ko da bokokon su ya zarta na kowa wajen iya bobo da kwambo. Muna fatan kamfanin jar tagiya zai koma can kasar Kolombo, don ya rika tara taro sisi da kwabo. Idan kuwa ba tarin’yan matsabbai ba ne kudurin wadannan jiga-jigan al’umma, to su himmatu wajen kyautata rayuwar gama-garin al’umma, musamman wadanda ke fama da tsumma. Domin kowa ya gaji da tuggun tagiyar masu mulkin mulaka’u.
Ni dai a ganina, kuma a matsayina na Direban allin makarantar Dodorido, tunda tsohon Gwamna mai kwarankwatsintsiya ya kwankwatsa aiki wajen kawata birnin Dabo, lallai akwai bukatar shi kuma Gandun aiki ya himmatu ka’in da na’in wajen inganta karkara, don kada a bar mazauna wadannan yankuna sun karke da kararen dangar danni. Kuma aiki ko na Shekararren mutumin Jihar Tumbin-giwa ne aka fara ba a karkare ba, wajibi ne Gandun aiki ya karkare shi, musamman ma ganin al’ummar birnin Dabo ne za su karu, kuma watsi da aikin na iya sanya al’umma ta kwaru.
Na kuma yi wannan tsokaci ne a kan turka-turkar mahukunta masu jar tagiya, ba don su ‘’yan Turkiyya ba ne, sai dai kawai don su Haurobiyawa ne da aka dora wa alhakin tarairayyar rayuwar al’ummar Jihar Tumbin-giwa. Kuma na ji wai Baban-burin-huriyya ya shiga tsakani don taka wa wannan gumurzu burki. A da  dai ban so wani babba ya tsoma musu baki ba, domin mu tabbatar ko ba su da tabi a kwanyar su; mu gano ko suna yi ne don al’umma ta fita daga cikin kangin rayuwa. Haurobiyawa, wanda duk ya yi gaban kansa don son handama da babakere ko danniya da murdiyya, tabbas zamani zai tafi da shi, kuma a yi wurgi da shi a cikin kwandon sharar kundin labaran da, da na yanzu.
Yau ina Fir’auna da Hamana, wadanda suka tafka tsiyaku a doron kasa, zamani ya tafi da su. Mahalicci Mai kowa Mai-komai shi ya san yadda zai hukunta su, musamman sanin yadda suka azabtar da al’ummar su. Kuma ina Gamji giji-gijin masu bobo da kwambon bokoko; ina Na Tafawa balewa Firiyimiyan farko a kasar Haurobiya? Wadannan sun shiga kundin labaran da, da na yanzu don sun aikata kyakkyawa, kuma za su ga kyakkyawa har a bayan rayuwarsu.
A nan nike karkare darasin wannan makon da amsa tambayar da jaridar Hawan san Ladar-shafi ta bijiro da ita a makon da ya arce, cewa: Mece ce makomar wasan Samson-siya-siya a birnin Dabo? Tun kafin ’yan dukan ta-mola su amsa da soki-burutsun su, sai in yi hanzarin cewa: Motsa muka-muki a wajen tauna Marsa da Daushen goriyar dan ujile, sannan wujijjiga al’umma a hannun wuju-wuju. Sai dai kada a kakaba wa kurungu tagiyar Malam Mantau, domin ‘yadda dillin takan yi dillin haka ma dillin takan yi dillin.’ Muna fatan Mai duka ya sanya a dilliro mana ayyukan raya kasa, amma ba aika-aika ba. Mu masu kallon majigi mun gaji da ganin Tuggun tagiyar tumurmusa talaka. Ya kamata a sake mana wannan sabon majigi domin mu ji dadin baje na-mujiyar mu a gaban allon silima, domin Kululu mai tuwo matar Lado ta bayyana wa Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya cewa, tun kafin Marigayi mai Shatawa da rera wakoki ya waketa, tun tana ‘’yar karama in ana so a aiketa sai an rera mata wakar wannan gwarzo nata, wato inda ya taba ya yi wa silmar da ta taba konewa da mutane a birnin Dabo: “SILIMAL EL-DUNIYA MAkARAR DANDI!’

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited