Sakonnin makaranta(90)
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Sakonnin makaranta(90)

A wannan makon mun jero sakonnin ’yan makarantar Dodorido. A sha karatu  cikin natsuwa. Ga batutuwean nan na jero su.

Wayyo na-kwadi
Assalamu alaikum, bayan sallama da salama, dukkan salati ya kai ga dan Aminatu baki sili, ba tare da bata lokaci ba zance na ingarman doki shi ne zan yi magana akan na kwadi ba wai na kududdifi ba, ko in ce rafi ba.  Ina  magana ne akan wanda ake sha don kwan-kwada domin kashe kishi. Sanin kowa ne har kirari ake yi masa na kwadi abokin aiki.  A Jihar Tumbin giwa, yau, makonni kofar hanci ana kwan-kwadarsa a kan Hauro sili da zagaye, akasin babban lauje da aka sanshi a da. A nan ina tambaya laifin waye ne ‘yan makaranta? Sanin kowa ne shekaru aru-aru ni sam-sam ban san wani na kwadi a leda ba, ko a wani mazubi ba, na san shi a randa ko a kwatanniya mai dan Karen sanyi, Jama’a ina kira da mahankalta ba masu hankali a hannun riga da su yi dubi da irin wannan yanayi da al’umma ke ciki na rashin… ooo ba sai na karasa ba, Iidan ban manta a shekarar da ta arce an so a kwatanta irin wannan lokacin gwamna mai sunan sassan jikin dan Adam na garin masu Madubi, da ya ji za su daka yaji akan karin Hauron na kwadi  sai ya yi musu tsawa, kuma sun ji  ina  kira da masu fada aji a wannan jiha da su dubi Mai-duka domin samun sauki, kuma ina kira ga al’umma da mu mika al’amuranmu kacokan ga Mai-duka da  ya ba mu damina mai albarka jama’a ku ce min amin… . Daga: Aliyu  Mukhtar Sa’idu Jami’in hulda da jama’a na kasa 08034332200. This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Tattaba na zomon Bala  
Bayan sallama irin ta masu kadaita Mai-duka sili dukkan yabo da jinjina da kirari ya kai ga dan Aminatu cika makin Annabawa, Ina mika gaisuwa ga Diraban allin wannan makaranta  mai albarka ta Dodorido, idan ‘yan makaranta ba su manta ba  a shekarar da ta arce malam ya yi sharhi a wannan makaranta a shafi mai albarka   akan yaran bala na ‘yan kura. To a yau zan yi magana ne akan tattaba na zomon Bala na ‘yan kura don yanzu sun yi kururuwa, sun tarwatsa a cikin babban gari irin na birnin dabo don yanzu har dabo-dabo suke yi lungu da sako don wafce wa al’umma abin hannu suke yi, musamman masu baburido masu tako-tako kofar hanci da zarar direban  wannan mai baburido da ya dan makala kurtun maganarsa domin ya samu caji hatta a dan fantarin baburidon, idan su ajiye dan Hauro sai su lallabo su zare ka ga sun sa shi aji ke nan, domin sai ya sake laliabowa don cike wannan gibi. Wasu kuma idan sun hau sai su ba su Hauro kamar bugun Harubja  mara kyau, su ce a ba su canji, kai mai kan-kat idan al’muru ya kawo kai idan zabi ta bugar mat aka biyo ta ‘yan huluna a cikin karamar Hukumar birni  da sauran wurare za a ce Hauro ko kurtun magana , jama’a wa Ankara huuu.. Daga:dalibin makaranta na Jihar dakin-kara Sani Y. Muhammad 07037881271

Sakon Makaranta
TA’AZIYYA    
Assalamu alaikum ga daukacin daliban wannan makaranta mai albarka ta Dodorido Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, muna sanar da ku rasuwar mahaifin shagaban wannan makaranta  mai albarka UNCLE BASH 07037133338, a makonni karamin lauje  da suka arce a Jihar da Fillo-ke-damawa. Mai-duka ya kyautata makwanci.  A madadin shugabanci na kasa. Daga: Aliyu  Mukhtar Sa’idu Jami’in hulda da jama’a na kasa 08034332200.

GAISUWA
Gaisuwa ga Direban alli, Assalamu alaikum yabo da godiya ga abin Kadaitawa da bauta,salati ga dan Aminatu shagaban masu Kadaita abin bauta tilo. Gaisuwa da jinjina ga shagaba farfesa kuma matukin Alli shehin malami, wato Sheikh Dodo mijin Dodanniya Uban Dodanni. Da fatan kowa na cikin koshin ingancin uwar jiki, Bissalam. Daga karamin dalibi na garin Sanyi Jihar dakin-kara, Usman Ibrahim Nadabo 08141816056.

Adon- gari da Iyayen-giji
Bayan sallama da salama ina sallau da salamatu ko sun  ketara kasar Santulisiya domin samun sabon salon tafiyar  da harkokin yau da gobe na cikin gida, domin ba sa gajiyawa, tunda  su ahalin gidan su Magajiya ne  da dan Magaji ehe. Mata a kan ce su ne iyayen giji sai dai kuma muzgunawar da ake yi musu a zamantakewar rayuwa na daukar salo iri-iri kama daga wariya a gida ko wurin aiki ko kuma cin zarafi da tauye musu hakkokinsu na yau da kullum.  
Sili, wariya a gida na nufin a ware iyayen giji, ta hanyar hana su kayan masarufi isasshe ko in ce kwange; ko mijin ya rika yi mata hannun jarirai, musamma idan tana da kishiya (a bokiyar zama) ita kuma dayar a rika dumbuza mata.
karamin lauje, wariya a wurin aiki, shi ma babban kalubale ne, musamman wajen raina aikin da take sai ka ji an ce ai aiki da mace sai a hankali, ‘Yan makaranta ku gane mini hanya, wai mahaukaci ya hau kura, ni a tunanina ai Mai-duka ne ya hallice mu, kuma hatta farin-mushi idan aka ga mace mai kamun kai ce sai ka ji ana cewa, ba za a yi mata don bata ba da hadin na kurungu, ko kuma a rika kyararta idan tazo a makare ba za a rika duba cewar ita aikin har kofar hanci ba ne kula da ‘yan dugwi-dugwi, kula da mai gida ga kuma ita kanta ko ba haka ba ‘yan makaranta?

Daga:dalibin Makaranta na Jihar dakin-kara Sani Y. Muhammad 07037881271

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited