Mu gyara halayenmu
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Mu gyara halayenmu

Assalamu Alaikum ya Mamal uban malamai, Bayan dubun gaisuwa mai tarin yawa irin ta masu duban alqibla guda da kaxaita Allah da ibada. Yaya aka ji da xalibai da kuma  GizBaba na bayan Katanga da yaransa?

Muna ta’aziyya ga waxanda suka yi rashi na ‘yan uwa da abokan arziki. Ina miqa ta’aziyyata ga shugaban xaliban wannan wannan makaranta na rashin da ya yi. Haka nan shi ma Shugaban yaran Gizbaba ya yi irin wannan rashi. Allah Ya ba mu jimirin jurewa, su kuma Allah Ya sa aljanna ce makomarsu, Ya kuma kyautata tamu in tazo, amin summa amin.
Bayan haka a gaskiya dokin qarfe mu mutanen Jihar Qadangaren ruwa da ke Qaramar Hukumar sabuwar birnin Zazzau mai masaukin baki na ganin wani abu mai kama da wasa da hankali. Da farko dai tun lokacin mulkin jam’iyya mai xanboto da sanda jirge aka fara aikin wasu hanyoyi, amma sai aka riqa jan qafa, har zavi  sonka da wuce ya zo aka yi aiki kamar za a gama, sai akac e zavi sonka ba zai bari a cigaba ba aka tsaya. Bayan an kafa gwamnatin canji ta Baba Buhari sai kwananan aka dawo da aikin kamar abin arziki an fara sai kuma aka tsaya.
Mu babban kukanmu a nan, shi ne, wata hanya da ke unguwar masu yafa gwado da ta kuma haxe unguwannin Kanawa da Fulani  shi ne ana yin ta ba hanyar ruwa, ga shi kuma hanyoyin ruwan na da an cike su lokacin wannan aiki. Lallai ba makawa idan Mai-duka, Ya saukar da ni’ima al’ummar wannnan yanki za su ba da labarI mara kyau. Domin hanyar za ta koma inda aka fito, kuma gidaje za su wahala.
An dai gaya mana cewa, waxannan hanyoyi gwamnatin tarayya ke yinsu, har a wannan karon an je, an ga minista a kan haka, amma ana ta wannan wala-walar.  Yanzu  kam mun baza na mujiya da na zomo muna kallon ikon Maiduka ana yi mana abin da aka saba da can, abu ya shiga har wajen kasafin kuxi uku anya.
Wani abu kuma shi ne, yadda ake so dole talaka sai ya wahala kan man tunkunza duk da cewa, ba ya da wata daraja yanzu a kasuwannin duniya, amma ana gaya wa talakan Haurobiya savanin haka. Jagoran canji ya ce a cire tallafi, kowa tasa ta fisshe shi; sun vullo da wata hanyar suna voye man. Mun gaza gane me suke nufi, to amma ta Allah ba ta su ba.  Mun  gane sune, ba wai Gwamnatin Baba ce ke da laifi ba. Sai dai kawai suna so talakawa su harzuqa ne a ce Baba ya kasa, to mun gane kuma da sannu za a kai  za kuma su sha mamaki in Allah Ya so. Su dai hankalta da karatun wasiqun jakin gida da na dawa kada a rutsa da su, inda ba su tsammata ba, don ranar qin dillaci na zuwa.
Duk mukarraban gwamnati sun yi ta murna a karon farko wutar lantarkin qasarnan takai wajen magawata dubu babban lauje a watan mai farin kunne da ya arce, Allah cikin ikonSa mara son cigaban qasar nan ba a haxa makonni qofar hanci ba sai da suka tura mu cikin duhun dunxumdurunxum. Da sunan ba a samun man juya injuna ne. ka ji fa don Allah. Abin kamar almara sai da qasar baki xaya ta faxa cikin duhu domin biyan buqatarsu adai ce Baba mai burin canji ya gaza.
Wani abin ma shi ne, idan aka samu wutar daga kamfanonin da ke samarwa, sai masu xauka don rabawa su ce ba sa so, domin ko dai wai suna bin bashi ba a biya su ba, ko kuma suna da wasu matsaloli. Yanzu wata sabuwa suka fara faxa cewa, muddin aka fara samar da wuta mai yawa kuma akan lokaci to wai wayoyin da ke qasar nan ba za su iya xaukar wutar ba. Ka ga ke nan ana gaya mana  ko da kamfanonin samar wuta sun samar masu rabawa ba za su xauka ba. Ka ga duk ta maganar a samar da magawata mai yawa babu ita ke nan. Kai! Allah Ya sauwaqa mana shi ma wannan laifin Baba Buhari ne?
Ikon Allah yanzu kuma kowa a Haurobiya yasan kuxinsu jikan mama domin komai ka tava za ka saya sai a ce maka kuxin mai jan kunne ya tashi birni da qauye, da yawanmu ba mu tava ganin wannan kuxin ba, amma yanzu kowa ya santa in zai maka kari. Allah Kai mana agaji.
Wani abin mamaki kuma shi ne inda kasuwanninmu ke ta kamawa da wuta, suna qonewa qurmus, wuta ta ban mamaki wacce da yawa sun ce ba su tava ganin irinta ba todai ya kamata mu hankalta. Koda yake babban mutum mai rawani na birni Dabo ya gaya wa ‘yan kasuwar abubuwan da ya kamata waxanda ba sai mun maimaita su a nan ba, amma dai waxannan abubuwa ayoyi ne a garemu baki xaya.
A nan zan dakata da wannan wasiqa sai wani lokaci in Maiduka Ya ba mu iko mun sake haxuwa. Allah ya ja zamanin Baba Buhari mai burin canji da duk mai qaunar Haurobiya da Haurobiyawa. Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya da qaruwar arziki duniya da lahira
Naka a kullum kuma xalibin wannan makaranta.

Lawal B Yusuf 08020636825 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited