Fama – faman fannin nama
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Fama – faman fannin nama

Fama-faman fannin nama kullin dukiya ce da aka tsibeta a tsibirin tsatsubar tsubbacen harajin kasashen, inda talakawa masu fama da talalar talauci suka samu lalitar kasar su ta zama fanko. A duk sa’adda aka tambayi masu mulki, sai su ce fam-fam! Wato dai ba a hannun su ’yan matsaban al’umma suka salwanta ba.

Haurobiyawa dai ba a bar su a baya ba, musamman jin cewa, Saurayin-kirinki da Dauda-mai-maki da dangatan kasuwa duk suna cikin wadanda aka jefa azargagiyar zargi kan su, a badakalar Fama-faman fannin nama.
A yayin da jiga-jigan jigata al’umma suka dauka cewa, giwa ta fadi a fannin nama, don haka suka zare balati, suka yanko, har suka cefanar, inda suka tara tarin fama-famai. To, masu wasan Samson-siya-siya da suka yi mana damo-da-kura-da-diyya, a dama-dama-da-kurda-kurdar siyasa sai ku natsu, domin fama-faman fannin nama sun ci karagar mulkin Firayiministan Tsibirin kankara, kuma giyara zargo wadanda ake tuhuma wajen tafka ta’asa, da warwasawa wajen cin wasa-wasa a kwanon tasa. Anan gumurzun gutsuttsura gurasa na tunkarar Dauda dan Kamaru, wato Firayiminhistan Birtaniya, inda ba a cin burtuntuna. Ga kuma Ladanin-mur na kasar Rasha, shi ma ya sha mur, saboda ganin ana yunkurin zargo shi.
Can kuwa a kasar Barazana-da-zilliya, uwargida Dilma ta kusa dilmeyewa cikin jerin wadanda ake zargi da tafka ta’asa. Kai al’amarin dai ya zamto kamar gasar dama gasara, don neman zama gargasa ko gagara-gasa.
Badakalar Fama-faman fannin nama ta fi tonon sililin wirkilili da Jallon Sange ya bankado a shekara ta dubu karamin lauje da sili da kofar hanci, musamman ganin cewa, al’amuran da aka bankado sun ta’allaka ne a kan tsarin difulomasiyar Amurkawa, wajen juya akalar kasashen duniya. Ita kuwa badakalar Fama-faman fannin nama, jiga-jigata al’umma ne faman fatattakar arziki, su tsuwurwurta tsiyataku a kasar su.
’Yan makaranta, lallai akwai bukatar mu fasko cewa,  abin da ya sanya ake samun dimbin jiga-jigan jigata al’umma a kasar Haurobiya, wadanda suka kware wajen yin kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma, duk bai wuce cutar sha’awar halin kusu ba. Kuma gama-garin al’ummar da rukunin masu tsuwurwurta tsiyaku ke dan difara musu na-koko, sai su shantake, su kasa ganin aibun miyagu.
Tsibi-tsibin matsabban da aka tsibe a tsibirai an tsame su tsaf, don kada kwalekwalen da ke dakon su ya wuntsula cikin teku. Kuma idan aka samu akasi fama-famai suka antaya cikin rafi, shi ken an an fasa kowa ya rasa. Wannan ta’asa da aka dade ana tafkawa shekaru aru-aru, ba sabon al’amari ba ne, illa dai kawai gama-garin al’umma ba su fasko jirgin masu tsuwurwurta lamarin ba har sai da kafofin kwakwazo da mujallu da makalu da jaridun irin su Gadin-yana ta Birtaniya da jaridar Jamusawa suka bankado badakalar.
Mu a nan Haurobiya, wadanda ake zargi da arce da fama-faman fannin nama, sun hada da Saurayin-kirinki da Dauda-mai-maki da dangatan kasuwa da Janar Najume. Wadannan rukuni na al’umma matukar ba su zille daga azargagiyar zargin da ke neman zargo su, ko wata tantama babu sun yi amfani da  mukaman sun a jagorancin al’umma wajen yin camama, sun bar kasa a cikin rashin makama.
Ko da Gwamnatin Tarairayar Haurobiyawa, karkashin jagorancin Baban-burin-huriyya da Usainin Babajo sun cafko wadannan jiga-jigan jigata jama’a, ai ba za ta sake zane ba. Domin abin Haurobiyawa ke bukata, shi ne, tarairaya da biyayya, su kuwa shugabanni su zama masu tabbatar da adala da kawar da juhala, ta yadda ba za mu hango su a wajen tafka badala ba.
Akwai bukatar duk wanda lakabinsa uya fito a jerin wadanda suka  daure damin Fama-faman fannin nama, to a nusar da su yadda za su dawo wa kasar Haurobiya da hakkokinta, su kuma dauri aniyar yin nadama tare da alkawarin ba za su sake tsuwurwurta irin wannan ta’asa a kwanon tasa ba.
Duk mai sha’awar gutsuttsura gurasa gami da masa a Masussukar Fansa, sai a nusar da ji illar da zai iya yi wa ’ya’ya da jikoki. Domin ba lallai ba ne su samu dama irin tasa ba. Sannan wajibi ne a hukunta duk wani kamfanin Lauye-lauyen dukan dokoki da ke taimaka wa miyagu wajen boye dukiyar da aka wawura daga lalitar kasa, don gudun kada su mayar da ita fanko kowa ya rasa na-koko. Masu bobo da kwambon boko, lallai a daina labewa a loko ana dukan al’umma da katako.
Wani abin ban ta’ajibi da ya akmata mu lura shi ne, babu Amurtkawa masu yawa a jerin sunayen wadanda suka tafka ta’asar Fama-faman fannin nama, lamarin da wata jarida ta ta’allaka shi da kudurin Uban-mama Jikan Kenyawa, Jagoran Amurkawa, wajen cin tarar duk wani asusun kasuwanci da aka samu da hannu dumu-dumu wajen sarrafa dukiyar samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya.
Hasalinma, mai shafin tonon sililin wirkilili, Mista Jallon Sange ya yi nuni da cewa, kasar Uban-mama na da hannu wajen bankado wannan badakala, musamman don ta bata sunan Ladanin-mur na kasar Rasha. Koma dai mece ce manufa al’ummar duniya ta yi amana da bankado wannan badakala, tunda ko ba a yi wa miyagu komai ba, ai sunan kura ya baci tun tana \’yar karamarta. Mu kuwa tabbas sai mun hadata da babban gardi, don ya makureta, ta amayar da abin da ta dundume kururunta da shi.
Koma dai wane ne ya bankado badakalar Fama-faman fannin nama, ya taimaki Haurobiyawa, domin za mu yunkura wajen mayar da namu, su zama Fama-faman fannin noma, wato dai mu himmatu ka’in da na’in wajen yin sana’ar na-duke, musamman limbu-limbu a cikin lambu.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited