Gwamna el – Rusau
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Gwamna el – Rusau

Malam Nasara el-Rusau, Gwamna gwarangwam a Jihar Bayan-kada ya shiga bakin duniya, musamman saboda dokar hana tashin-tashinar addini da korar ’yan bumburutu da ya aiwatar a kwannan nan. Lallai ya kamata mu yi tsokaci a kan mutanen Malam Darlung da ke fadin kasar nan, musamman masu bumburutu buruntun satar tunkuza da ke gararamba a tituna. Ko Malam ya yi daidai ko akasin haka, ba ita ce manufar mu ba; manufa dai a gyara rayuwar masu fuka-fukin tashi kolin-koliyo, don kada a kwada su da kasa, su nakasa.
A farfajiyar wannan makaranta mun sha karawa da Malam el-Rusau tun yana Magajin garin Haurubja babban birnin Haurobiya. A wancan zamanin an ce ya yi aiki da wani katafaren kundi mai taken: Matsala falan-falan: Cikakken ikon rusau.  Wannan kundi ya sanya har waka na yi wa Malam ina rerawa:
Magaji ya rusa birane
Magaji ya rusa mutane
Dalilin wakena kuwa shi ne, a zamanin mulki Magajin gari el-Rusau, wadanda suka dandasa gine-ginen zamani, amma ba bisa ka’ida ba, an yi rugu-rugu da akurkin su. Sannan a zamaninsa ’yan tasku masu faso sun ci Karen su babu babbaka; a takaice dai su suka rusa masu laluben na-koko, musamman a garin tako-tako cikin dakin katako, a Haurubja bangaren Utako.
Lokaci dai ya yi da ya kamata a nusar da Malam cewa, Jihar Bayan-kada ba za a kwatanta da Haurubja. Don haka zai yi ta samun tarnaki da ’yan bana-bakwai, musammman masu cuwa-cuwa da camamar man tunkuza. Hasalima na ji labarin yadda masu jinni-ajika suka yi biris da wannan doka ta bumburutu a unguwar nagge da karsana da ke birnin Bayan-kada.
Batu na ingarman karafan kwangiri, a Arewacin Haurobiya mun saba da tallar kayan dundume kururu, shi ya sa ma idan mutum ya farka da gari yawaye zai ji ana cewa:
Ya damu da gaya koko
Ko ya damu da gaya kunun tsamiya
danwake da mai da yaji,
Ya tsufa a kai shi bola
Abin da nike son nusar da mu shi ne ko Gwamnan Jihar Bayan-kada ya hana dillanci da tallace-tallace, yana da alfanu al’umma su bullo wa kan su wata ’yar dabara da ba za su sba wa hukuma. Dalilin bijiro da wannan batu shi ne, na fasko cewa a zamanin mulkin baraden Haurobiya, karkashin Baban-burin-huriyya, wato a shekara ta alif sili da manuniyar kasa da madambaci da tsayuwa bisa kafa daya, da aka hana garamba a titi da tallata hajja, mutanen birnin Dikko da kewaye sai suka rika yin wannan ciniki a ’yar yara. Ko dai a yi kasuwancin kayan dundume kururu a ’yar yara, ko kuma uwargida ta kafa wata ’yar shigifa ko ta zauna a azure tana ta zare-zaren Hauron Haurobiyawa.
A yau ma zan mamaita irin tallafin da na sha bijiro wa hukuma kan lallai ta difaro wa mutanen Mista Dalong, wato dai ina son Malam el-Rusau ya dauka tamkar shi ne Gwamna Lalong, sai ya bayar da tallafin kafa Shagong Dong fong irin na mutanen Mao Zedong, kuma a dauki mutanen Mista Gizagong su yi Dakong, ta yadda za su daina garamba da kashe wandong a cikin Kangong.
Idan har Mai girma Gwamna gwarangwam, Malam Nasara el-Rusau ya fitar wad a mutanen Mista Dalong da muhimman tsare-tsaren tysere wa tsara, tabbas ni za fito in ce: Gwamna ka zama Makasau, tunda an ce kai jikan Babban mutum mai rawani Kwasau ne.
Shi kuwa batun kakaba wa masu babatu da sunan ibada ga Mahalicci, sai mu duba kundin labaran da, da na yanzu, inda za mu fasko illolin da tsinin tsinuwar Marwa ta yi wa al’ummar birnin Dabo; da karon battar da aka sanya Masu Kadaita Mahalicci da Ibada da bayin Allah da ke cikin Majami’a. Don haka matukar ana son tabbatar da lumana, a wannan karon ina tare da Malam el-Rusau. Hasalima akwai bukatar rushe duk wani mai mummunar ta’ada da ke amfani da dandamalin yin batutuwa ga mabiya don tada kan adda, wai shi ya zama ci-ci. Matukar ana so mu zauna da ’yan uwan mu cikin lumana, to kada a bari miyagu su rika fakewa da guzuma don su harbi karsana. Karsana da nagge da bujimi an duk ba a sakin su sakaka, sai da mai kiwo.
A dan tsahirta da rushe-rushen matsugnnan al’umma, har sai an samar musu wurin taushe na-zomo, don su ji dadin yin na kasa, don kasa, mu kuwa mu kasa mu kwashi kashi.
Lallai Malam ka san yadda za ka tallafi rayuwar  mutanen Mista Dalong. Idan ka hana su camama da cuwa-cuwa, to ka tura su cikin garka da gayauna su farde mana mana dazuka; a tada kwarin kunya, har tsirron tsabar hatsi ya tsattsafo mana daga kasa. Kuma a sanya su, su yi limbu-limbu a cikin lambu ko mun samu ganyayyakin girka dambu. Wanda kuwa yake da shaidar koyon watsattsake da buda wagagen littattafai mai inganci, to a kara ingantata. Idan kuma an samu gurbin laluben kadago a wajen kwadago, sai a dan tsarma su yadda za su samu abin curin mandako a dan koko. Sannan akwai bukatar a nusar da masu fuka-fukin tashi, mutanen Mista Dalong, cewa, ba lallai sai mutum iya bobo da kwambon bokoko ba zai rike kansa ba. A’a, domin Malam mai yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba, ya ce “ba maraya sai rago.” Shi ke nan sai ku ji cewa:
Malam ya gyara birane
Yana ta inganta rayuwar mutane
Ku kwashi girkin da ke tukwane
Zogi da radadin kurungu ya zagwanye
Kasalar gabobi ta kwaranye
Yau gari ya waye
Ga maganin miyagu da wawaye
Ba ruwan sa da shafaffu ko masu zane!

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited