Gayaunar bisashe
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Gayaunar bisashe

Jojin In-wala, mashahurin mai watsattsake ne da ya wallafa wagegen littafin nan mai taken “Gayaunar bisashe,” inda aka tsakuro hargowar bisashe  a gayaunar su, suna ta shimfida mulki, bayan da suka karbe gayaunar daga hannun makiyayi.

Salon watsattsaken Jojin In-wala sai gwanayen murguda baki kamar suna cin kilishi, masu sarrafa harshen Ingilishi za su fasko irin shaguben da ya yi wa masu gumurzun gurguzu, musamman a tsohuwar tarayyar Sobiyat, wadda ta tarwatse ta zama Rasha, inda ba a cin rashawa.
Abin da ya sa na bijiro da batun watsattsaken wallafar Jojin In-wala na ‘Gayaunar bisashe,’ ba domin gurguzu ku akidun makisanci sun samu gindin zama a Haurobiya ba, a’a, illa dai kawai na ga a tsarin mu na Ja-in-ja-da-jarin haja, wasu na tafiya sakaka tamkar ba su da makiyayi. Kuma ba don na ji Baban-burin-huriyya ya nusar da jagororin Ifrikiyya cewa, tabbatar da zamantakewar adalci za ta inganta rayuwar al’umma, da na nusar da shi cewa, mafi yawan Haurobiyawa na karakaina ne a gayaunar kashin sha kushe. Domin duk da dimbin abin biyan bashi da ake bai wa ’yan kwadago a Haurobiya kafin a shekara sai ka ji kungiyoyin masu fafutikar neman kadago na nema karin ladar kwadago, har ma da la’adar kadago.
Sanin cewa akwai dimbin ’yan kwadagon da ba su da tarbiyyar ririta kadago, inda za su rika aiki da agogo, amma ba wasan cikin kango ba, sai na bijiro wa hukumomi da bukatar a rika difara wa ’yan kwadago ‘Albukata,’ ta yadda idan daukacin bukatun biyan bokan Turai da koyon watsattsake da buda wagagen littattafai suka biya, babu wanda zai yi wa hukuma tsallen badake ko tada jijiyar wuya don neman karin la’adar kadago.
Haurobiyawa, lallai akwai bukatar masu watsattsake da buda wagagen littattafai su fasko cewa, mu warware sasarin gayaunar kashin sha kushe da ke dabaibaye takun talakawa da shugabannin su a Haurobiya, ta yadda za a kawar da juhala a tabbatar da adala. Wannan kuwa zai yiwu ne idan muka tallafa wa Baban-burin-huriyya da Usainin-Babajo a fafutikar su ta hana kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma; mu daina yi wa doka karantsaye. Uwa-uba mu gina manhajar makaranta mara hajijiya don samar da kwararrun Bokayen Turai da Direbobin alli da jami’an tsaro, tunda kasa ta zama babu tsaro sai tsoro.
Mu daina gumurzun gurguzu, tunda babu yadda za a ce wajen rabon dukiyar kasa an bai wa kowa daidai wadaida, kuma ai Jojin In-wala ya ce, “daukacin bisashe sun daidaita, amma wasu sun fi samun daidaito.” Wannan dai na nufin idan har aka yi yunkurin daidaita kowa da kowa, to wasu sai sun samu fifiko a kan gama-garin al’umma. Idan kuwa aka tafi a kan tsarin ja-in-ja-da-jarin-haja, to hajijiya ake karkewa da ita, idan ma ba a yi sa’a ba, a ci kasa.
’Yan makaranta mun dandana mulkin mulaka’u a hannun Turawan Ingilishi ba mu sha da dadi ba, amma da bakaken Turawan Ifrikiyya suka kama ragama, har sai muka gwammace kida da karatu. Domin a yau da za a bai wa al’umma zabi kan ko Turawa su dawo ko a ci gaba da ‘Gudun-loko da su a karkashin tutar jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, tabbas masu hankali a kwanyar su za su zabi mulukiyar Birtaniya, tunda ba a cin burtuntuna. Kuma ko Sa’addunmu na Zungur wanda ya ce, ‘mu yi zumbur ka da mu yi zugum,’ ko Aminin siyasar mutanen birnin Dabo da ya furta cewa, ‘motsi ya fi labewa,’ sun bijiro da tsare-tsaren tsere wa tsararraki da muka ki bi, shi ya sa aka bar mu a baya. Malam Sa’addun mu dai ya ba mu zabi, “Arewa mulukiyya ko ko jamhuriyya; muna nan dai a cikin jamhurun jamhuriyya.
Yau idan mutum ya tafi kasar Birtaniya zai tabbatar da cewa, ba su yi watsi da al’adun su na gargajiya ba, watakila ma shi ya sa bayan shekara dari tsayuwa bisa kafa daya, suka yi bikin tunawa da mashahurin mai watsattsaken wasan kwaikwayo da wake-wake, William Girgiza-masu; fitattu daga cikin wagagen littattafan sa sun hada da Matsolon Attajiri da Daren sili da karamin lauje da sauran su. Mu kuwa mun kakaba wa kurungun mu tagiyar Malam Mantau, inda aka daina ta’ammali da mawallafan Jatau Na kyallu da Uwar gulma, ballantana gwarzon masu watsattsake Alhaji Imam da ya kara da Zurke dan Muhammad a Ruwan Bagaja.
Don kada in cika ku da surutu rututu, bari in karkare batutuwana da batun Mai fasaha Akiliyya, inda a waken sa yake cewa:
Saba da samo gaskiya ta fi nisa
Sarari da boyi ka don ka so bunkasa
Ga gargadi ya zuwa garemu zumaina
Da duk da wanda yake Hausa
Ku nan na kurkusa har na Cana da nisa
Ba wai gwani ne ni ba,
Ku karkade kunnuwanku ku ji ni zumaina
Gargadin da zan mana shi ne:
Sikikin-bakaka tiki-kaka kyaftinkif!
A daidai wannan lokaci da Haurobiya take hankoron zama sansanin Sinawa, to mu sani cewa Sinawa ba su kai inda suka kai ba, har sai da gwarzon su Mao Zedong ya dora a kan turba. Yanzu kuna ga di Jinping, ya gyara birni yana ta fafutikar warware wa mazauna karkara sasarin talauci, don haka ma a makon da ya arce kafafen yada kwakwazo suka ruwaito cewa ya yi jele a yankunan karkara da ke fadin Sin. Saboda haka mu yi aiki tukuru wajen koyi da kyawawan ta’adu irin na mutanen Mao Zedon, amma wajen dabbakawa a aikace, mu tabbatar mun daidaita su da al’adunmu da addinin mu.
’Yan makaranta, mu kauce wa zama a ‘Gayaunar bisashe,’ ta yadda za mu shawo kan ‘kason sha kushe. Shi yasa nike ganin lalllai mu yi azama wajen tunkude Saurayin-kirinki, amma kada mu bayar da damar jigata al’umma ga Akuyar-maman-Daudu, musamman ma tunda kafafen yada kwakwazo sun bankado cewa shi kanwa uwar gami wajen takaddama da cukurkuda al’amuran kundin baje-kolin bana. Tunda kullin makircin su ya bayyana, me kuma za su kulla wa kasar Haurobiya, musamman ganin cewa ba su ke jan ragama ba?

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited