Yamadidi!
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Yamadidi!

Gwamnatin Baban-burin-huriyya da Usainin-Babajo, a karkashion jam’iyyar maganin zogi da radadin ciwon kurungu na fafatawa da matsalolin da ke ci wa Haurobiyawa tuwo a kwarya, musamman kwashi kwaraf da dukiyar al’umma; da yamutsin Haramta Bobo da kwambon Bokoko; ga ’yan watandar Samun-bom-da-sauki da Mace-da-zane da sauran gungun miyagun da suka addabi kasar nan, amma an buge da yin yamadidi da fullo, wato dai ana ta bugun taiki, an kyale jaki.
Yayime-yayimen ’yankwana kasa suka sanya aka fake da guzuma ana harbin karsana, don a cutar da Fullo mai fululun nagge da karsana da bujimi, da ke samar da abin dundume kururu samfurin balamngu da tsire da ragadada da malkun mululluke kururu da kawuna da kafafun bisashe. Fullo ya saba karakaina a dokar daji yana kiwata bisashe don samar wa al’umma kiragan burgame da fade da sawu-ciki. Duk da haka tsawon zamunna babu wata hukuma, ko wani ba’ari na masana da ya bullo da dabarar yadda za a tarairayi sana’ar fullo, don ya ci gaba da tara mana bisashe fululu.
Wani abin takaici shi ne, a makon da ya arce duk wanda ya falle shafukan jaridun kasar nan babu abin da zai gani sai labarin kanzon kurege kan yadda Fullo ya kai farmaki a Garin-tutu da birnin Ina-gungun masu biyan-fura, har ma aka ce ya kassara rayuwar dimbin al’umma, amma maharani babu abin da ya same su, ko ya jikkata nagge da karsana da bujimi. Wannan ta’annati da aka danganta fullo da shi, har ya kai ga wasu na some-somen tarwatsa Haurobiya, ko kuma a ace kowa ya ci bakon gidan sa. Hasalima wasu sun furta cewa, lallai a fatattaki Fullo daga Kudancin Haurobiya.
Sanin kowa ne, tsohon Gwamna gwarangwam na Jihar Bini-ina-wai, dake birnin Makurda ya taba bijiro wa Gwamnatin Shugaban Gudun-loko da bukatar gani an fatattaki fullo daga birnin Haurubja, ko ma kasar nan dungurungum! Yau wa gari ya waya? Sususun-wawan Makurda ya yi karo da Iro Mugun madambaci. Fullo ya tsallake taskun sa, amma ya afka taskun masu kwakwazo a kafafen surutu rutu rututu. Domin ai wannan badakala ta Fullo mai dimbin nagge ta zama bidiri birede biredi a wajen su Fanco da Gadin-yana da Banga-da-gadi. Kodayake an yi sa’a jaridun Dalilin-taron su da Balon-faranti da Faffale-dalili sun dan tallafa wajen yada batutuwa na ingarma karafan kwangiri, musamman a wannan lokaci da miyagu suka waske daga kan turba.
Batu na ingarman karfen karafa bari in raira wakar mu ta ’yan dugwi-dugwi, kafin in bijiro wa Fullo da mafita, tunda shi da iyalansa ai Haurobiyawan Haurobiya ne, masu ’yanci kamar kowa.
Za ni zaniye,
Za ni Zariya zuga,
Zugar doki,
Dokin kara,.
Kara na albasa,
Albashi kwadi,
Kwadin zuci,
Zuciyar damo,
Ta sare Kudu,
Ta kuma ta sare Kudu,
Kudu garin baka,
Baka na manomi,
 Nomau noma ciyawa,
Ciyawar rago,
Wane rago?
Ragon Sarki Allah mai ruwa da kankara,
dan makolin bisa kolin kwash!
Wannan wake namu na ’yan dugwi-dugwi na nufin cewa, tunda a Kudancin Haurobiya a kwai Hauren-Danja, yanki mai dimbin albarkatun man tunkuza, mu ma a Arewacin kasar nan muna da Hauren Hatsi da bisashe, wadanda in aka tarairasye su yadda ya dace, to tattalin dukiyar kasa zai tsayu kyam!
Ardo da Jauro bayan na kwashi gaisuwa, wato ina mai gaya muku Jamirawo, to ku kara kaimin kiwon bisashe bisa doron tafiyar zamani. Kuma lallai ku sani cewa, duk wani fullo da ke kasar nan, tun daga birnin Shehu Mujadaddi zuwa birnin su Alan-guburo mu muna daukarsa, tamkar Tanirawo ne a wurin  danfodiyo, shi yasa muke takaicin ganin sun ki daukar wasiyarsa. Tabbas da Ardo da Jauro sun dauki batun kakan su, Mai-duka, Mai kowa, Mai komai zai ba su kariya daga masu fashin nagge da karsana da bujimi, har ma su rika watayawa daidai da salon kowane zamani da suka samu kan su a ciki.
Tunda mun fasko jirgin masu yamadidi da fullo, musamman a yama-yamar su ta neman madi, ina ganin akwai bukatar a bijiro wa Gweamnatin Babnan-burin-huriyya dabarun kafa MAKEKEKIYAR MAKIYAYAR FULLO. Yin hakan kuwa ya zama dole, musamman a wannan zamani da kasar Danniyar-maki ta zama babban garke garaken nagge da karsana da buji, har ma da sauran bisashe a Arewacin Turai. Kuma duk inda BURTALI yake a kwato shi.
’Yan makaranta, masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a farfajiyar Dodorido da ke cikin Amnintacciyar jaridar kasar Haurobiya, inda ganin akwai bukatar a yi wa Fullo jihohin sa, ko a kwato masa garuruwansa, irin su wuro-baggo da Rugar Jawo da makamantan su.
Ardo da Jauro lallai ina jan na-zomon ku kan lallai ku dauki batun Mujadaddi, domin Sa’adun mu na Zungur, wanda ya ce lallai mu yi zungur (zumbur), amma ka da mu yi zugum:
Shehu Laminu da shehu Mujadaddi
Sun bar mana gadon gaskiya.
Idan har ana son tabbatar da ADALA a kawar da JUHALA, weajibi ne mu yarda cewa, cikin kowace al’umma akwai NAGARGARU, kamar yadda ake da KANGARARRU. Lallai a yi wa Fullo adalci, ko don bai iya murguda baki da kanga gilashi ya yi ta yaren Ingilishi ba? A’a, What can’t TSUGILAGI Turanci and sometimes kOBOBO?!
Sai mu karkare da batun Shehu, wato: Njange da Ndure da Ndeme, ma’ana ku koyi watsattsake da buda wagagen littafai, har ma da tafiyar tsutsa; ku yi kiwon bisashe; sai kuma ku bazama cikin sana’ar na-duke, wajen fardar garka da gayauna.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited