Taskun turka – turkar tunkuza
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Taskun turka – turkar tunkuza

Jiga-jigan jan ragamar kwadago a kasar Haurobiya sun yi barazanar takun saka tsakaninsu da Gwammnatin Baban-burin-huriyya, saboda karin farashin man tunkuza da ya yi wa al’umma, wato daga Hauro tukunyar dambu da manuniyar sama da kwabbai babban lauje da zagaye, zuwa dari sili da tsayuwa bisa kafa guda da babban lauje.

Wannan lamari bai yi wa Haurobiyawa dadi ba, musamman wadanda ke da masaniyar cewa, tunda daga zamanin mulkin Shugaba Gawo ba a taba samun karin farashin da ya kai na Baban-burin-huriyya ba.
Lamarin makamashin sarrafa na’urori da ababen hawa, samfurin kurkurido da baburido da shorido-shorido, ya jefa al’ummar kasar nan cikin taskun turka-turkar tunkuza. Dundumi ya kama mu, mun kasa lalubo bakin zaren. Kusan kowa ya dora laifi a kan Baban-burin-huriyya, har ma wasu na nuni da cewa, ya yi amfani da IGIYAR CUKWU-CUKWU, ya cukwikuye Haurobiyawa. Masu hankali a kwanyarsu, sun san inda bakin zaren yake, amma masu hankali a hannun riga, sun yi hannun riga da batun ingarma.
A da dai tsarin cinikiyya ya gaji ‘ga wuri ga waina,’ amma yanzu kuwa kowa ya san ga WURI GA WAWURA, shi ne tsarin da ake tafiya a kai. Ga dai Baban-burin-huriyya ya himmatu wajen hana HANDAMA da WAWURA da BABAKERE.
Sai dai abin takaici ba mu cika wassafawa a cikin kwanyarmu ba, kan yadda za mu dambace da tsilli-tsillin matsalolinmu, illa dai kawai mu yi wa gwamnati tsallen badake. Domin al’amura sun rincabe, ta yadda mutane na ganin gwamnati ya kamata ta yashe musu kwatami, ko tarin jujin da suka jibge a matsugunansu. Watakila wannan ne dalilin kara-kainar sauro da kyankyaso da kusu da jaba da gafiya. Kai lallai da sake. Mu bullo da dabarun hadin gwiwa da shugabannin al’umma, wajen kawar da JUHALA da tabbatar ADALA!
Ni dai ban kware a lauye-lauyen dokoki ba, amma ina da masaniya cewa Gwamnatin Haurobiya mai ci ta bi ka’idojin da suka dace wajen cilla farashi tamkar a faranshi. Kuma hujjar da ta bijiro wa al’umma, kamar yadda aka kattaba a jaridun kasar nan, ita ce rincabewar musayar Hauron Haurobiya da sauran kudaden kasashen ketare, musamman Dalar Amurkawa, wadda aka fi tu’ammali da ita a kasuwannin duniya, al’amarin da ke cin dunduniyar tattalin kasashe masu tasowa, har ta kai ga Gwamnatin Haurobiya na dawuwurin juya akalar cinikinta bisa doron Yuwanin Sinawa. Kuma aiwatar da wannan dabarar sarrafa dukiyar kasa har masana na ganin an yi abin da ya dace.
Ba na bukatar zama masanin tsimi da tanadi, ballatana in fasko cewa, kudaden musaya sun tsawwala. Wanda duk bai gamsu da wannan bayanin ba, to sai ya tambayi Barau-dan-canji. Kai har ma kwararrun masu lissafin shige-da-ficen Hauro da damin matsabbai a kasashen duniya. Duk wanda ya fasko juyin karni na karamin lauje da sili, musamman tsarin tsimi da tattali da damo-da-kura-da-diyya, ba zai yi ta’ajibin tashin gwauron zabon da man tunkuza ya yi ba.
Don haka ina ganin tsallen badaken da masu laluben kadago da ladar kwadago ke shirin tsuwurwurtawa a Haurobiya ba zai haifar da da mai na-mujiya ba, musamman in an yi la’akari da cewa, an sha daukar irin wannan mataki, har ma an yi tattaki, amma ‘hakar kwakware ba ta cimma na-kwadi ba.’ Shi ya sa na fasko cewa, kungiyoyin neman lada da la’adar kadago suna bukatar a nusar da su dabarun ririta abin hannu, kuma kowa ya hakakke wa kansa cewa, matukar ba ki yi gashin wance ba, kada ki ce za ki yi kitsonta. kasashen da al’ummarsu suka fa’idantu da dimbin azikin man tunkuza da ake matsowa a kasa, suna da tsare-tsare managarta, wadanda suke bi don sarrafa dukiyarsu, ta yadda talakan kasa ba zai samu kansa a dabaibaye da sasarin talalar talauci ba, tunda gwamnati ta samar da matsugunan al’umma; da kula da uwar jiki a farfajiyar bokon-Turai da koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a farfajiyar direbobin alli kyauta-kyauta.
Haurobiyawa, idan har Gwamnatin Baban-burin-huriyya ta kwatanta inganta walwala da watayawar al’umma, ko ta cilla mana farashi zuwa faranshi, ai sai mu yi murmushi. Domin idan ’ya’yanmu suka koyi watsattsake da buda wagagen littattafai kyauta-kyauta, wata rana za a samu masana kimiyya da za su himmatu wajen sarrafa fitsari ya zama makamashi, tunda na ji an ce a Birtaniya da Amurka an samu wadanda suka kera na’urar ja-ni-ina-reto mai aiki da fitsarin amalala. Kun ga ke nan idan amalala yana tsula fitsari babu wanda zai sake nema masa magani, tunda an gano cewa, fitsarin kwance ai ba cuta ba ce. Kai ta yiwu ma a ce mu daura wa amalala bututunn roba ya rika kwararawa a ciki.. Yin haka zai ba mu damar samun kariya daga ’yan Hauren-Danja masu fasa bututu.
’Yan makaranta kada wani ya yaudare ku cewa, Direban allinku yana yin wasannin Dodanni ne don kawai ya kare Gwamnatin Baban-burin-huriyya. Batu na ingarman kwangiri ina ganin hakki ne na masana kimiyya a kasar Haurobbiya su samar mana da makwafin man tunkuza, ko na’urori da ababen sufuri za su kwakwadi man tunkuza kadan, ko fitsarin amalala su ci gaba da aiki ka’in-da-na’in ba tare da sun rankwafa ba. A kasashen nahiyar Turai da Asiya, akwai baburido da kururido da ke amfani da makamashin rana, kai hasali ma har kurkurido mai tuka kanta da kanta aka kero, kuma an yi gwajinta, mun ji, mun gani.
Kai wannan babban kalubale ne ga masana kimiyya da kere-kere a Haurobiya, kan lallai su lalubo mana wata sabuwar hanyar sabunta nakamashi, musamman a daidai wannan lokacin da albarkatun man tukuza suka yi rugu-rugu a kasuwannin duniya, kuma suka tsula tsada a kasar Haurobiya. Idan masananmu suka nuna gazawa, to sai mu dauka kawai sun karke da kimiyyar kimtsa miya da kurmusun karago.
Shi kuwa mai kaso-kason wawanci ko jiga-jigan jigata al’umma a cinikin man tunkuza, in sun kasance masu kishin Haurobiya, wajibi ne a kansu, su samar da hanyar samar da man tunkuza a farashi mai rahusa, ta yadda ba za a bari ya lula zuwa faranshi ba. Shi kuwa talaka mai fama da sasarin talalar talauci yana bukatar dabarun ririta makamashi don kada ya lakume masa ’yan matsabbai.
Gwamnatin Haurobiya kuwa hakki ne da ya rataya a wuyanta ta nusar da Haurrobiyawa kishin kasa, musaman sanin cewa Larabawan Sawun-diyya da yankin Khalijil-Arab suna horar da ’yan dugwi-dugwi son kasarsu, ko garinsu, abin da suke yi wa lakabi da “HUBBUL-WAdANI. Domin yin hakan zai bai wa kasar nan kariya daga haifar da miyagu irin su Samun-bom-da-sauki da Mace-da-zane da sauran gungun ’yan watandar jam’iyya mai dan boto da sanda jirge da suka jirkita kasar nan. Wata hujjar a kan haka Malam Bature ya nusar da mu muhimmancin “PATRIOTISM,” wato son kasa da kishinta.
Masu laluben kadagon lada da la’adar kadago a ofisoshin gwamnati da kamfanoni masu cin gashin kansu, akwai bukatar kowa ya bayar da gudunmuwarsa, wajen inganta kasar nan, ta yadda za mu samu sa’ida da saukin farashiin albarkatun man tunkuza. Masanin kimiyya a jam’in-jama’ar jami’o’in Haurrobiya ga kalubale nan; dangatan kasuwa da Audu-tela ga ku yi gwaggwaban kasuwanci, amma ba kaso-kason wawanci ba. Ku kuwa ’yan Hauren-Danja in kun ki ji, ba kwa ki gani ba. Domin an samu man tunkuza a sassa daban-daban na kasar nan; can a Ikko akwai yiwuwar gwamnati ta fara samun na-koko; a birnin Dikko akwai Bamle kauyen masu nagge da karsana da bijimi. Idan mutum ya nausa zuwa yannkin gabashin Arewa an dade da bankado kwantancen man tunkuza da iskar gas, har zuwa cikin tafkin Chadi. Da dai yamutsin haramta bobo da kwambon bokoko ya kawo wa kasar nan cikas, yanzu kuwa ga dama babu damuwa. Shamuwa masha ruwa wuya mike!

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited