koton kurciya, koton zakara
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

koton kurciya, koton zakara

Kwankwatsa da tsattsagar ci-maka salon sarrafa kayan dundume kururu ne da tsuntsaye suka kware a kai, tsawon zamani. Don haka a duk sa’adda aka zuba wa tsuntsayen gida da na dawa hatsi a kasa, sai su rika caccakar kasa da tsinin bakin su, suna ta sudda kai da dagowa, wato dai sama da kasa ke nan. Don haka talo-tolo da shirwa da hankaka da sauran tsuntsaye duk suna da salon koton su, al’amarin da bai saba wa koton kurciya, koton zakara ba.
koton tsuntsaye ko dundume kururun mutane, a iya cewa kwade tabahuwa ne da kota. Domin akwai dimbin jagororin al’umma da ke koyi da koton kurciya, koton zakara, a wajen ririta dukiyar al’umma da aka danka musu amana. Kai wasu ma talakawa suke dan difara wa kaso dan mitsitsi, su kuwa su haure da damin hatsin Hauro, domin su ji dadin yin rawar gaban hantsi. E. mana, kun ji batu, tunda ai Malam mai yaren Hau-hau wajen hawan sa, ba tare da .sa-in-sa ba, ya ce, ‘hantsi ba hatsi hatsari.’ Wai hatsaniya ke nan!
A tsakanin shekarin dubu karamin lauje da manuniyar sama zuwa ta dubu karamin lauje da kwanciyar magirbi, idan na shigo Haurubja, babban birnin Haurobiya sai in ziyarci Kwacanga, inda ake kwankwatsa da tsattsagar ci-maka. Wani lokacin nakan kwashi toyeyen shakushe da farfesun kayan ciki, amma da muka dawo bayan Otal din ci-da-kanka da ke garin tako-tako sai na fara goge hakora da cinyar kaza matar zakara. To kaji!
Kodayake wani hanzari ba gudu ba, nasan cewa, musamman a wannan watan da masu fuskantar alkibla don kadaita Mahalicci da ibada ke kame baki, Malamai sun gargadi masu ibada da yin koton kurciya, koton zakara, wato dai a wurin ibada kada a rika yin ’yar dungure babu kakkautawa, musamman ga wadanda ke son zuwa makarakata mai babban allo,, ’yan kallo ko sun yi dubu allon su guda; ko ’yan tashe da makamantan su. Ni dai na san Malam Mai kawa’idi ya ce: Wal I’itidalu, waddumaniyatu, wato daidaituwa da natsuwa ke nan. Sai mu kula domin wannan bai takaita ga ibada ba, har ma da mu’amala a zamantakewar al’umma. Wannan na nufin duk aikin da aka yi babu natsuwa wata gwaggwabar fa’ida na yin tashin tsuntsuwa. Shi ke nan an rasa ta. Wajibi ne mu bi ka’ida don samun fa’ida.
Haurobiyawa, abin da nike son nusar da mu shi ne, a lokacin da na yi dogon hutuna, bayan da na karade yankin ‘Laka da ke karkarshin masarautar birnin Dikko,’ inda na yi karakaina a tsakanin Huntun-dutse da Munumfasa,’ da na dawo birnin Dabo na ga abin mamaki. Wata rana ina walagigi a kan titin kotu daura da titin gidan giwa da gidan zaki, sai na ga jaridar Dalilin-taron su dauke da labarin ‘Laulayin Lolo,’ inda Gwamna Gwaramgwam na Jihar Ni-na-ja, mai mulki a birnin Mina-mina ya rusa ‘Kukan Tenhiya,’ wato dai shi ya nuna gazawarsa wajen biyan lada da la’adar kadago ga ’yan kwadagon jiharsa. A cikin labarin an bijiro da dimbin batutuwa da suka yi nuni da cewa, mafi yawan jihohin kasar Haurobiya ba za su juri biyan bashin kwadagon watsattsaken masu aikin farar kwala ba, tun daga kan direbobin alli zuwa kan masu zaman dirshan a ofisoshi suna kwanklwadar shayi, suna ta ‘Bobo da kwambon bokoko.’ Sai na ce assha! Murguda baki kamar an ci kilishi da kanga gilashi ana ta yaren Ingilishi kuwa zai yiwu? A’a, what can’t TSUGILAGI Turanci and sometimes kobobo?!
Laulayin Lolo ko lambatun lambun lakume lalo? Titibiri da kolo kun ji sabon salo, tamkar a kurtun magana na halo alalo, musamman idan mutum ya shiga layin gwalalo, yana ta yi wa jama’a gwalo; ko dolon Dola-kaina yasan wannan sabon salo ne irin na masu kidan molo.
Matukar aka ci gaba da samun korafe-korafen jagororin al’umma wajen kasa difara wa talakawa kason su, daga dimbin abin da aka ware musu daga lalitar kasa, duk da cewa ana fama da tangal-tangal din tattali, ai sai mu shiga rukunin ’yan adawa, har sai an difara mana dawa, mun yi koton kurciya, koton zakara, don kada mu shiga dawa. Kai ina Gwamna Gwarangwam ke samu damin Hauron da yake yi wa duniya shataletale? Kuma ina belin-auta da Baban-burin-huriyya ya jinka muku; ko ya zama Billen-wauta ne?
Ba don gudun kada a jefa mini azargagiyar zargin shiga jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ba, ai da na shawarci mashawartan Gwamna gwarangwam, musamman na Jihar Ni-na-ja. Kai sai ma na yi domin ina kyautata zaton yana da alaka da mutanen can masu Inda-inda, ni kuwa mutumin Jihar dakin-kara ne. Kuma kamar yadda na sha yin tsokaci a darussan wannan makaranta, cewa, idan za a kwashi gaisuwa a gaban Babban mutum mai rawani, a Jihar Ni-na-ja, sai a ce “BAAGADOJI,” mu kuwa jinjina muke yi wa Maimartaba Muminin Babban mutum mai rawani na birnin Dikko. Yawwa kun ji, kun ga bambancin.
Shin wai wadanda ke kukan sun kasa biyan ladar kwadago, ba su ji cewa, Gwamna Gwarangwam na Jihar Bararon-nono da ke mulki a birnin su Alan-guburo har ikirari ya yi a wannan mako cewa, ‘ bai taba fashin biyan lada da la’adar kadago ga ’yan kwadago ba, har tsawon watanni manuniyar sama da zagaye ba wani zagaye-zagaye? Wata bajintar da ya yi, ita ce, cewa, ‘yamutsin haramta bobo da kwambon bokoko bai kawo masa tarnaki ba.
Wani mashiriricin da ke mulkin mulka’u a Jihar Aikin-titi, Gwamna Gwarangwam Ayayondandalin Fetsararren Faya-fayen-soye cewa ya yi ya shiga yajin kwadago tare da ma’aikatansa. Kuma abin takaici, wai da Iro Mugun Madambaci ya binciki asusun ajiyarsa, a Asusun Zannin Hauro ya same shi dibge da damin Hauro gashin balama sili da malala dari karamin lauje. Kai wannan mugu dan muguwa ya cancanta a kada masa jauje a kudarsa. Ayayon-dandali ba shi da hankali shi ya sa ake sanya masa kidan garmaho na Faya-fayan-soye-soyen zuciya. Yau dai ga shi sun ci karo da Hukumar Gwagwarmaya da arangama da masu fashi da mukami ko da dabara. Lallai Iro kada ka sassuta masa. Ku kuma talakawan Aikin-titi kun shiga taskun mai hankali a hannun taguwa, saboda za ku yi ta fama da tabahuwa, har sai Mai-duka ya kawo muku dauki.
A wannan gabar nike ganin ya dace in bai wa Gwamnatin Baban-burin-huriyya shawara kan yadda za ta yi wa tufkar hanci, tun kafin miyagu su jefa mu cikin rikici. Kai har ma daukacin masu rike da madafun iko a kasar nan, tun daga kan mataimakin Baban-burin-huriyya, Usainin-Babajo zuwa kan daukacin gwamnonin Haurobiya dole ne su yi wa al’umma bayani filla-filla kan yadda kowa zai samu kason sa daga lalitar Gwamnatin Haurobiya, walau a farfajiyar Bokan Turai ko a cibiyoyin koyon watsattsake da buda wagagen littattafai.
Shugaba Baban-burin-huriyya, ai da ka tafi birnin Lantsandan, wajen gyaran na-zomo a farfajiyar Bokan-Turai, sai ’yan adawa suka rika baza jita-jitar cewa, wai ka zama NA-DAKAMA DANKAM, BA KA JIN DAKA SAI DAMU! Kuma ai, ‘adawa in ba dawa, sai a shiga dawa.’
 Da na shiga damuwa, har na yi tunanin yadda za a shirya maka Liyafa a Lantsandan, sai Shugaba Malam Mun-ga-gobe na kasar Zaman-gidan-buwai a Kudancin Ifrikiyya ya furta cewa, duk kasar da ake ta yin SURUTU RUTUTU kamar kasar Haurobiya, babu shugabancin da ya dace da al’umma, tamfar jagorancin Na-dakama. Saboda haka babu abin da nike so a cikin watan rahama, watan alfarma, illa kawai ka kandamo kindirimo a cikin damamma, amma ba na shan tsantsama; shi ya sa ma idan da hali ka dan difara mana ’yar zuma. Domin ta haka ne kawai za ka iya magance zogi da radadin kurungun Haurobiya.’
Lallai a tursasa kowane gwamna gwarangwam ya samar da makekiyar garka da gayauna, inda za a rika tada tudun kunya don hatsi ya tsattsafo, mu samu abin tsattsaga da kwankwatsar ci-maka, amma ba a kyale wani gwamna gwarangwam shi kadai ya yi ta kOTON SHAHO da SHIRWA da  HANKAKA ba. Kuma nan gaba idan har za a jinka musu Belin-auta, sai a mika shi ta hannun Hukumar Inda-sisi, mai bai wa ajiyar asusu-asusun ajiya a Haurobiya kariya; ko kuma ta hannun Kamfanin Aman-kunu da ya kware wajen cefanar da asara ta rikide ta zama riba. Ni dai ina sha’awar ganin a bude GANDUN GWAMNA, inda za a rika fardar garka da gayauna, tare da kiwon tsuntsaye da bisashe. Haurobiyawa sai mu fahimci cewa, kukan kurciya jawabi ne, amma kukan zakara tashin hankalin rashin hatsi ne.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited