Sakon ’yan makaranta 2
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Sakon ’yan makaranta 2

Bayan sallama ta addinin gaskiya, zan yi amfani da wannan dama na yi godiya ga Direban Alli bisa ga irin fadakarwa da ilmantarwar da yake yi mana ba tare da gajiyawa ba. Ya ‘yan uwana dalibai ina ba ku hakuri, na san kuna nan kun kasa na zomo kun sa na mujiya ku ji ko ku ga motsin monitocin wannanmakaranta, amma shiru duk da kuna ta jin darussan da malam yake yi kuma wasunku su kan sanar da mu irin jin dadin karatun da Direban Alli yake gabatarwa.
Mai Kowa Mai Komai ya ja kwanansa ya inganta uwar-jiki, ya albarkaci ‘yan dugwi-dugwi da Ma-ba-da-mama). Da yardar Mai -duka za mu nemeku domin dorawa daga inda muka tsaya, don hada kan ‘yan makaranta da yadda za ta kara habaka.
A madadin sauran dalibai, nike mika godiyarmu ta musamman ga iyaye da jagororin wannan wageggen littafin ‘AMINIYA’ na Haurobiyawa da ake gudanarwa cikin yaren Hawan-sa, shi ne lamba sili (1) a kasar Haurobiya, musamman ganin yadda ake bai wa jama’a gishirin-zaman duniya da wayar musu da kai. Da fatan Mai-duka ya kara daukakaku.
Ban manta da daya daga cikin daliban wannan makaranta ba ‘Halliru Jodi’ da aka yi wa nadin sarautar Wazirin Hausawa a Jami’ar Usmanu danfodiyo da ke Birnin Shehu, a ranar daga ke sai tushen aiki, kofar hanci da zagaye a watan babban lauje, a shekarar karamin lauje zagaye sili manuniyar sama (30/5/2016). Muna taya shi murna da yi masa fatan Mahaliccin kowa da komai ya yi masa jangora a cikin wannan sarauta. Ya Mai-kowa Mai-Komai ka ba  u dukkan alherin da ke cikin watan azumin nan tare da inganta mana uwar-jikinmu, ka ba mu ikon ayyuka na kwarai, wadanda za su kusantar da mu da Kai, Ka tsaremu dukkan abin ki. Jama’a mu yi kokari wajen taimakon ‘yan uwanmu da abin da Mahalicci ya hore mana, ka da mu ga kankantarsa.
Na gode.
Umar Muhammad Abdullahi
Daga Tumbin-Giwa
Ofishin Shugaban Tsangayar Kimiyya
Jam’in Jama’ar Jami’ar San Kano,
+234(0)8067676454,
+234(0)8099767645, This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

A sammana sudi
Bayan sallama da salama ga daukacin daliban wannan makaranta mai albarka ta Dodorido, ina kira ga shagabanni a duk inda suke da ma sauran al’umma da muka ga Mai-duka ba don komai ba, domin shi ne Mai-kowa, Mai-komai, a kasar nan tamu ta gado Haurobiya a zamanin Shagaba Gawo aka fara karin Hauron man kuli-kuli, har ya zuwa yanzu da muke ciki, bana mantawa Mai-duka ya kai ga rahama ga makwancin Shagaba ‘Yar’bishiya don ya yi namijin kokari wajen rage farashin man tunkuza daga kwanciyar magirbi da babban lauje ya zuwa manuniyar sama da babban lauje na tallafi da ake talla da shi ga wasu kasashen ketare ba wai cikin gida ba. To al’umma ina kungiyar masu kwadago ku suma sun koma dandago ne suna ta dago-dago, su yi kira ga Shagaban Buhariyya ko a sammana sudi, don samun saukin rauywa.
DagaShagabar Mata Hajiya S. Baci-rarwa Jihar Tumbin Giwa

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited