Buskin-mati
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Buskin-mati

Haurobiyawa barkan mu da bude baki, domin nasan al’umma da dama sun kwashi kayan dundume kururu. Musamman tuwon samfarera da taushe a gidan Malam Mai yaren hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba. Sai dai a sani a wannan zamani a kwai wata nau’in samfarera da ake samu a Gandun Gandi, wadda masana suka ce tana inganta uwar jiki, har ma ta tayar da kwomadar tsofaffi tukuf-tukuf, wato dai ina yin batu ne a kan Buskin-mati.
Kimanin shekaru tsayuwa bisa kafa guda da suka arce, an taba tuka mini tuwon Buskin-mati, bayan mun dundume kururunmu, har muka aika wa makwafta. Wannan lamari ya auku ne a birnin Dabo inda ba a dabo, amma makwafciyar mu tamkar an yi mata dabo, tun da ta dandana gardin Buskin-mati da miyar taushe. Domin bayan mako guda ya arce, sai kawai matar makwafcina ta samu Dodanniya matar Dodo ta bijiro mata da tambaya cewa, “a makon da ya arce wane nau’in kayan dundume kururu kika girka mana?” Sai Dodanniya ta ce, “ai samfarera ce, samfurin buskin-mati.”
Kai ko a cikin ’yan kwanakin nan sai da Dodanniya ta ce in sawo musu Buskin-mati, amma sai na ki, saboda jin cewa samfarera ta tsula tsada, har na ma fara tunanin ko shanshera zan sawo a turara, sannan a murzata a inji, ta yadda za mu ji dadin alkinta ta a buhu.
Batu na ingarman kwangiri abin da ya san a bijiro da batun Buskin-mati, shi ne nag a an yi batunta a shafi na karamin lauje da tsayuwa bisa guda da ke cikin Aminiyar wannan makon, har ma aka nuna yadda ake sarrafata a dakin girka kayan dundume kururu don karawa da tabahuwa. Uwa-uba na zagaya wasu sasssan Arewacin kasar nan a lokacin da na yi dogon hutuna, inda na ga yadda aka farde garka da gayauna don shuka samfarera.
Wanda duk ya ziyarci Durbin-bande da ke karamar Hukumar Takunkai ko Fifi-dallo da sassan karamar Hukumar Albashi kwadi da ke karkakshin Jihar Tumbin -giwa zai tabbatar da batuna tsauni ne. Durbin-bande da Fifi-dallo da Gisal-belli da Bere garuruwa ne da nike ganin ya kamata a yi musu lakabin Kwarin-samfarerar Birnin Dabo, musamman a wannan lokaci da suka yunkuro wajen samar mana da dumbin kayan dundume kururu.
Kai Manoma Allah Ya taimaka mana wajen hatsi, cikin duniya ba  abin da ya kai ga farau-farau.”
Kodayake muna batu ne kan Buskin-mati, tunda an ce a kasar Mahtma Gandhi ake samo Buskin-mati, lallai ya kamata mu fasko yadda za mu rika sarrafa samfarera ta zama Buskin-mati, maimakon a ce duk sa’adda mutum ke bukatar wannan kayan dundume kururu dole sai ya ziyarci katafaren shagon Sahada, wato ka saka damin Hauro ka harhada kayayyakin masarufi; ko kuma ka shiga shagon JIFA-DA-FATU; ko SHAFA-KA-RIRITA, wai Shafin-ririta kayan masarufi. Lallai Buskin-mati abincin masu hannu da shuni ne. Saboda haka nike kira ga Gwamnatin Baban-Burinhuriyya ya yi kokarin samar mana Buskin-mati a farashi mai rahusa, musamman a wannan lokaci da shugaban al’umma ya mayar da hankali wajen dundume kururun marasa galihu a fadar tsaunin Bila a birnin Haurubja.
’Yan makaranta a yi sallah lafiya. Da fatan an dundume kururu da Buskin-mati, amma ban da tambele a kan titi. Shi yasa ma na himmatu wajen yi wa kwanyarku saiti, kodayake idan kun yi santi wannan laifi ba ne. Da an kammala bikin idi, to a hanzarta wajen komowa makaranta don koyon wattsattsake da buda wagagen littattafai.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited