Logar lakume lagwada
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Logar lakume lagwada

Hukumomin hada-hadar sarrafa matsabbbai na duniya sun kware wajen tsibe tsabar basussukan wuni-wuni, irin na ’yan uwan da ba su-da-wani ga al’umma, idan an yi bikin dare guda, shi ke nan sai a fara taraddadin biya.

To ‘ranar wanka dai ba a boyon cibi.’ Turawan Turai dai sun saba yi wa mutane badda bami, musamman wajen yi wa nahiyoyin Asiya da Ifrikiyya ‘Turin-wawa,’ a tsarin tattali. Turin-wawa dai shi ne aringizon lamunin langar ligidin Lagad, inda daga bisani a turo ’yan baranda su yi laga-laga da kasa, watakila ma fahimtar irin wannan logar ce ta sanya sa’adda Shugabar Hukumar Lakume Lumanar Lamuni ta duniya ta taba sauke langarta a Haurubja babban birnin Haurobiya da sauran sassan kasa, inda masana suka nuna adawar su har suka soki lamirin lakumar lumanar tattalin dukiyar Haurobiya.
Da uwargida mai langar lakume lumanar tattalin kasashe masu yunkurowa ta gano cewa an fasko jirginta, sai ta fake da cewa, kasar Haurobiya ba ta bukatar lamuni, illa dai akwai wasu ’yan gyare-gyare irin na gyare da kurege da ake so ta aiwatar. A jerin wadannan sharudda akwai yin rugu-rugu da Hauron Haurobiya, ta yadda Haurobiyawa za su shiga cikin haure-haure da hauragiya. Ta bijiro da shawarwarinta ne cikin watan Janye-wuri na shekara ta dubu karamin lauje da sili a manuniyar sama. Shi kuwa  Shugaban kasar Haurobiya, Baban-burin-huriyya ya nuna rashin gamsuwarsa da tsare-tsaren da wannan hukuma ta lakume lumanar tattalin tumun kasashe masu yunkurowa. Jin haka ke da wuya uwargida ta kwashi langar ligidinta ta yi gaba.
Uwargida mai langar lamuni da ta koma gida ta natsu, sai ta fara shirya wa Haurobiya gadar zare, inda dimbin masana a fannin tsimi da tanadi, suka yi ta nusar da Baban-burin-huriyya alfanun da ke tattare da karya lagon Hauro. Da na-zomon Baba ya dode sai ya daina sauraren su. Don haka sai suka yi amfani da Barau-dan-canji, suka caje mu, inda aka karke da DAFDALAR DAULAR DALA. A lokacin da aka dabaibaye mu da ciniki bisa doron Dalar kasar Uban-Mama, jikan Kenyawa, jagoran Amurkawa, hatta mai tuwar kosai da mai tallar goriya marsa in ya tsula tsada sai ya fake da hauhawar farashin musayar Hauro da Dala. Ba a kammala dafdalar daular Dala ba, sai kuma a ka shiga TASKUN TURKA-TURKAR TUNKUZA. Taragon tunkuza ya tunkuda mu cikin rukuki. Domin har yanzu akwai turka-turkar takun sakar ’yan Hauren-Danja masu bula bututu, don bumburutu.
Can kuwa a wani barayayin Baban-burin-huriyya ya tura ro Mugun Madambaci yana fafatawa da miyagu masu magu-magu, musamman ’yan watandar Hauro, da suka arce da damin Dalar cinikin makaman artabu  amasu haramta Bobo da kwambon bokoko. Mugun Madambaci ka kara shirin nada dambe, domin ni na ga in an toshe can, sai kuma su huda wani ramin, tunda ga shi ar yanzu su Mace-da-zane ba a san makomar su ba.
Hauobiyawa duk wannan walankeluwar da nike ta yi muku wai so nike yi ku fasko cewa akwai azargagiyar zargi a kan Uwargida mai langar ligidin lamuni. Domin ta yi amai ta lashe, tunda ta yi has ashen cewa tattalin tulin dukiya zai tuttulo wa Haurobiya da kashi karamin lauje da digo kwanciyar magirbi ciki sili da zagaye-zagaye ba wani zagaye-zagaye; sai kuma kwatsa ta bullo da LOGAR LAkUME LAGWADA, tunda ai Langar ligidin Lagad ba ta samu shiga ba.
’Yan makaranta batuna tsaunin Kwatarkwashi ne, tunda na baje na-mujiya a kan shafi na sili da kofar hanci da ke cikin jaridar Dalilin-taron-su ta ranar karamin lauje da zagaye na watan yawon-wulli, inda aka ruwaito yadda Hukumar Lakume Lumanar Lamunin Lumanar tattalin kasashe masu yunkurowa ta dankwafe bunkasar tattalin Haurobiya, a jerin manuniyar attalin arzikinta.
Uwargida mai langar ligidin lugwigwita tattalin duniya, lallai ki sani, in maye ya kakaba wa kan sa tagiyar Malam Mantau, ai mai da ta Malam Tunau yake sanye da ita. Ki sani cewa, Asusun Je-fi Mugun shi ya fara wancakalar da Haurobiya daga jerin manuniyar bunkasar tattalin arziki ta duniya da ya saba baje wa masu nazari, musamman masu zimmar zuba jari a ciki da wajen Haurobiya. Je-fi Mugun dai karshe sai da kaikayi ya koma kan mashekiya.
Batu na ingarman kwangiri Je-fi Mugun da ya jefi kasar Haurobiya ya karke da badakala iri-iri, don haka ke ma uwargida mai langar ligidin lagad, tsarin wala-walar ‘Logar lakume lagwada,’ da kika bullo da shi ba zai yi tasiri, tunda Baban-burin-huriyya ya himmatu ka’in da na’in wajen ganin an hukunta ’yan watanda da suaran migyagun da suka kassara kasar nan.
’Yan makaranta kowa ya yi kishi, amma ban da kisisinar kishiya da sanabe da felekenta. Kuma ka da ku bari a shirya mana kissa, don samun saukin yi wa tattalin mu kisan mummuke; ko snaben daurin saniyar bebe. Domin yin haka ne kawai zai ba mu damar karya lagon logar lakume lagwadar dukiyar kasar mu a ciki da wajen kasar nan. Masdu koyon watsatttsake  buda wagagen littattafai a farfajiyar Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya lallai a shirye muke wajen dakile duk wani yunkurin Logar Lakume lagwadar tulin tattalin Baban-burin-huriyya da Usainin-Babajo, a karkashin tutar Jam’iyya mai maganin zogi da radadin ciwon kurungu. Mutanen Mista Darlung, masu fuka-fukin tashi ku ne karfin al’umma, lallai a daina zaman kashe wando, don ka da a kifa wa kasar ku Kwando.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited