Kauyen Kannen-Audu
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Kauyen Kannen-Audu

‘GizBaba,’ inji Nigawa

Namijin majigin Haurobiyawa
Man-kaza abokin Indiyawa
Da Michael Jackson mawakin Amurkawa
Na bayan kango mai rausawa
Kai mai jarumai da basawa

Gyaran mota sai Kanikawa
Julius Berger Jamusawa
’Yan kwantiragi Larabawa
Ku gyara Haurubja ta zam ta kawa
Baban-burin-huriyya da Usainin-Babajon Haurobiyawa

Mai kulob ka yi yawa
Ka shiga daji shan yazawa
Amintacciyar jaridar aminiyawa
Shekaru sili da zagaye tana dada zagayawa
GizBaba da Ddrd na dada jinjinawa

Ni Dodo abokin Larabawa
Har da Frank Rogers dan Jamusawa
Farfesa Sultan Poly Hassan dan Misirawa
Ko zu mu yi ta cakusawa
Kun fi karfin kadamusawa

kannen -Audu
Nalelen-audu a kudu
Balon-Audu
Inna rududu
A kwaikwayon Holewar-Dudu

Kafin kannen-Audu su fara wasannin zille-zille da zankade-zankaden Zillaziyya da Zankadaziyya  a dandalin majigin Haurobiyawa, an saba baje na-mujiya a makarkata mai babban allo, ’yan kallo ko sun yi dubu allon su guda. Kuma babu abin da suka fi nuna wa gayu irin rausayawa Indiyawa da tsalle-tsallen kung-fu irin na mutanen Sin. Kodayake a wani loton akan nuna wa gayu magijin harbe-harben Kaboyi da Turancin tarairayar Holewar-aududu, inda gayu Turawa da Amurkawa ke cin asin-da-asin rike da sigari tushen bidi’a, ‘in ba ka sha ka kunna ka rike.’
Baya ga majigin Balon-Audu da Holewar-Dudu har da sana’ar Shago da dandunawan Turawa da asakalar su duk ana baje mana su a akwatunan magana da ke baje witsil-wutsil din dodon hotuna. Hasalima yanzu har shugaban Haurobiya Baban-burin-huriyya ya bayyana wa Mista Infantino, shugaban Hukumar Harbatta-mati ta duniya cewa, Haurobiyawa sun kulla auratayya da ta-mola, amma duk da haka yana yunkurin yi wa Hukumar Ta-molan Haurobiya garambawul.
Al’amarin majigi da dodannin hotuna masu wutsil-wutsil yana da matukar ban ta’ajibi, musamman in yi la’akari kan yadda ya yi tasiri a rayuwar Haurobiyawa. Kai ni nasan wadanda suka kakaba wa kawunan su sunayen jarumai da basawan majigi. Idan ma ba a samu wadanda suka kakaba wa kan su sunaye jaruman magijin Inidiyawa da Sinawa, to sukan yi rausaya da tsalle-tsallen Amitbacha da Shashikapur da Bursuli da Jackiechan. Can kuwa a bangaren dukan ta-mola ba abin mamaki ba ne ka ji mutum ya kira kan sa Balan-toliyar ta-mola; Masar ko Mesar ta-mola ga Rawanin ta-mola, ballantana su Pele iyayen falle ta-mola a zamanin da.
Tsananin darsuwa da kaunar dukan ta-mola kan hairfar wa masu jini a jika cacar baki, har da mangari ko ma a karke da kisan gilla. To ba wannan ne abin ji ba, tunda ana gudanar da wadannan shirye-shiryen majigi a harshen Mutanen Mahtma Gandhi da Mao Zedong kuma Haurobiyawa ba su cika jin abin da ake furtawa ba. Don haka akwai bukatar a yi wa tufkar hanci, tun kafin a yi mana shigar hanci da kudundune.
Batu na ingarman karafan layin dogo, akwai lokacin da na fasko cewa wake-waken Indiyawa na burge Gizo-gizon-dakin-gwaggo, sai na yi yunkurin yi masa faskaren ma’anoni a wata wakar da na ji ana rerawa:
Taimaki gatari, ka riki gatari
Bi tara molaki ya! Ho!
Harikici, hariya!
Ma’anar da na ba shi kuwa ita ce:
Ka taimaki kanka da rikon gatari, ban da taraliyyar molaki-molakin yayin huhun ma’ahu, wato dai kada ka zama huhun ma’ahu- ta gina ba ta shiga ba. Kuma ban da harin rikici a rariya. Duk da irin wannan shatale-talen da nike ta yi wajen shawo kan ’yan bayan kango su zama natsattsun mutane ba masu badala ba, har yanzu ba su daina bin kannen-Audu yawon dandalin daben shirin wasan majigi. Kun ga ken an akwai sauran rina a kaba.
’Yan makaranta ya kamata ku fasko cewa, ina ta kai gwauro da mari ne,’ don samar da kyakkyawan yanayi a kauiyen kannen-Audu na shirya majigi da ake yunkurin kafawa a birnin Dabo inda ba a dabo. Kuma ina dan yin takatsantsan don kada Ulama’u su jefa mini kaulasan, musamman jin cewa suna adawa da fannin ilimin fina-finan majigin kannen-Audu.
Ina son lallai Ulama’u su yi mini uzuri in shirya majigin da zai magance laluben dan kanzo da kai wa dandagodago bara da dankoko.  Kai akwai bukatar a shirya majigin da zai nusar da kishiya illar kisisina da kissa, har ma da kassara rayuwar ’yan dugwi-dugwi. Lallai malaman da ke jan ragamar harkokin ibada da mu’amala don kadaita Mahalicci da ibada su bari a shirya mana majigin da zai hana masu fukafukin tashi laulayi da garamba a layi, suna yin ’yan zuke-zuke da kara wa sama hazo, wai su ga babaye ko bebaye ne ma oho! Ni dai na san in Baba ya zama baba, shi ke nan sai a ga tamkar yana kwaikwayon Babe na mijin fara.
Ita kuwa Gwamnatin Baban-huriyya akwai bukatar ta fayyace wa al’umma yadda za ta horar da ’yan was an majigi, sun kware wajen nusar da al’umma kon watsattsake da buda wagagen littattafai. Uwa-uba a amfanar da al’umma dabarun sarrafa BOBO-DA-kWAMBON BOKOKO, ta yadda masu rike da madafun iko za su daina samarkatar kusu ko rausayar ’yan matan jaba da gafiya. Haurobiyawa dai kusan kowa shaida ne kan irin dambarwar da ake tsuwurwurtawa a majalisun tsofaffi da wakilan rafkiyar kasar nan. Ga Saurayin-kirinki can har yanjzu bai warware asakalar da yake yi da Hukuma da Kotun Kwaran-kwandam ba. Shi kuwa Dogarin wakilan rafkiya ya shiga takun saka sa Kofaton rafkiyar al’umma da su hadin gwiwa wajen gwagwiyar goribar Hauron kundin baje kolin Hauron bana.
Hukumar daukar kwandon barau da Gogarma sha gwagwarmaya da arangama da msu fashi da mukami ko da dabara, suna shan bakar wahala ne saboda rashin fayyace wa al’umma manufar su ta kange miyagu daga kassara kasar nan. A nan ma akwai bukatar a shirya mana majigi da zai fayyace mana dabi’un su Madam Araruma da ’Yardidida Farfesun Gareji da Santala kwaiduwa da Mace-da-zane, sai kuma Samun-bom-da-sauki tare da sauran ’yan watanda da suka kassara kasar nan.
Idan kuwa Ulama’u da sauran masu adawa don ba a difara musu dawa ba, suka yi biris da batuna, to akwai yiwuwar a haifi mutum a karamar Hukumar Rogo ya kakaba wa kan sa ROGOKAPUR; ko kuma a haife shi a Gujungu ta Jihar Jijjiga-ciyawa, sai kawai ya ce ai shi sunan sa GUJUNGUN-KHAN ko GUJUNGU-KAPUR. Domin an taba samun irin haka, wani matashi dan asalin birnin Dabo da aka tura shi Indiya koyon watsattswake da buda wagagen littattafai sai ya karke da zama gwanji rawa kamar dan mazari, ga kuma wake-waken Indiya, sannan ya kakaba wa kan sa suna AMIN KHAN. Kai akwai ma su HUTSANYU masu tsalle bisa tsinin mashi, wai suna kwaikwayon Judo da kareti da Kung fu irin na mutanen Mao Zedong.
Sannan akwai yiwuwar wasu su rika yi wa Arewtawan Haurobiya kallon hadarin kaji, musamman jin cewa masana a fannin ilimin addini suka hana kafuwar kauyen kannen-audu. Domin na taba jin labarin cewa, a garin Dodon-doya, wani maigadi day a hango Malam mai yaren Hau-hau wajen hawan sa, ba tare da sa-in-sa ba, na kokarin kutsa kai cikin farfafjiyar koyon watsattsake da buda wagagen littattafai da yake tsaron kofa, sai ya kasa ya tsare, wai mutumin ba zai shiga, domin a zaton sa aikin gadi zai nema. Bayan sun gama takun sakar ya kyale Malam ya shiga, inda suka gana da shugaban Makaranta, ashe mai yi wa kasa hidima ne, saboda haka aka ba shi a ji ya koyar da Ingilishi. Ganin mutumin ya fara aiki ka’in da na’in, sai maigadi ya lallaba, ya leka ta taga, don ganin ko me Malam ke yi a aji, sai kurum ya hango shi ya dauko alli ya rubuta ENGLISH. Da ganin haka sai maigadi ya ce, “THIS WORLD DON SPOIL A HAUSA MAN TEACHING ENGLISH!
Mu dai mun san Marigayi babban mutum dukan gangar taushi na birnin Dikko ya taba furta cewa:
Nufin su mu (yi) wasan gargajiya, ya sa mu kara fahimtar juna
Wasu sun bar al’adu na iyayen su, sun bi na ’yan ci-rani.
Haurobiyawa masu hankali a kwanyarsu, ya kamata ku fasko cewa, muna bukatar shirya majigin kawar da BAdALA  da JUHALA don tabbatar ADALA. Kowa ya bayar da gudunmuwarsa don inganta yanayin kAUYEN kANNEN-AUDU, idan kuwa munm kiya to a tauraron dan Adam ma za mu ci karo da shirye-shiryen HOLEWAR-DUDU. Dama Holewar-dodo ce ai sai mu ce ku baje na-mujiyar ku, don Direban allin wannan farfajiya ya ja ragamarku a cikin shorido ko ya dora ku a baburido ko kekerido, laulawar Dodorido.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited