Rukukin rafkiyar rafkanannu
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Rukukin rafkiyar rafkanannu

Kwakyariyar cusa aikace-aikacen bogi da Majalisar Wakilan Rafkiyar Haurobiya ta tafka na ci gaba da daukar hankalin Haurobiyawa, musamman a wannan lokaci da dagirgirin Dogari da Kofaton Majalisar suka sanya zaren dambacewa da asakala. Watakila ko SHAGO da dANDUNAWA sai sun yaba musu, ballantana GURGU MAI ALJANA da MAMMAN BUROS, da sauran ’yan ku ci ku ba mu a harkar dambe da asakala. Wakilan rafkiya dai sun rafkana, domin a lokacin da suke fantamawarsu babu wanda ke jin kansu, har sai da na-kwadi ya yi tsami suka afka cikin rukukin rukwatubo, wai ‘TSANTSAMI TSANTSAMIN TSAFGA TSAMIYA,’ tuni dai an tunkuda TUNKU, kamar yadda Malam Sa’idu Faru ya fanfare, ya karkare mana a cikin wakensa.
Wannan lamari na cusa abin da babu a cikin KUNDIN BAJE-KOLI, kamar yadda masana suka yi nuni ba bakon abu ba ne, amma abin da ya sanya wannan karon ya ja hankalin kowa a kasar nan, shi ne, Gwamnatin Baban-burin-huriyya ta himmatu ka’in da na’in wajen cafko masu kwashi-kwaraf da dukiyar kasa, har ma da wadanda ke rike wa miyagu kaho su yi ta tatsar nonon nagge da karsana. Kun ga ke nan idan Dogarin majalisar rafke al’ummar kasar Haurobiya rike wa Kofato kaho ya yi, shi kuma ya yi ta tatsar kindirimo, to ‘NONON ya yi TSAMI,’ sannan furar da suka dama ta damalmale ta dame. Ni dai ban a shan tsantsama, a kandamo kindirimo a cikin damamma. Kai wata gaisuwar sai mun je birnin TAGADAS, in mu ci CA’AMMAS, du kind aka kewaya, sai kawai a ce maka DA DAMA! e, DA DAMA!
Haurobiyawa, musamman masu bibiyar makarantarmu ta Dodorido, ya kamata ku fasko cewa, Dogari dai shi ne Ja-gaban Majalisar Rafkiya a kasar Haurobiya, shi kuwa Kofaton da ya tattake damin matsabbai ya cusa su cikin kundin baje-kolin bana, shi ne ja-gaban kwamin-titin tantance ayyukan da aka tsara gudanarwa da damin Hauron da aka yi hankoron samu a shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama. Wadannan shagabannin al’umma lallai sun sha gabanmu, maimakon su aiwatar da ayyukansu yadda ya dace sai suka tsuwurwurta tsiyataku, har aka bankado TAbARGAZA da bARANbARAMAR da suka dade suna tafkawa.
Dogari dai tuni ya fatattaki Kofato daga jagorancin Kwamin-titin tantance aika-aika. Shi kuwa gogan naku da ya tabbatar an yi masa bita-da-kulli, sai ya yi ta babatu a mujallu da mukallu, har ma da akwatuna magana da masu wutsil-wutsil din dodannin hoto. Wai nufinsa ya wanke kansa da SABULUN SALO, amma ina! Shi ma Dogarin sai ya fara kiran masu watsattsake a jaridu da mujallu don su tagaza masa ko ya tadiye Kofato ya daina yi masa takun dodanni, wato SARMA-SARMA DIF-DIF. Kai Haurobiyawa akwai DUDUFNIYA a majalisar rafkiya, domin sun yi rafkanuwa har sun rafke kawunansu, inda yanzu haka suna cikin rukuki. ‘Tuntsun dai da ya jawo marka-marka shi za a make.’
’Yan makaranta ba don kada ku jefa azargagiyar zargi a kaina ba, ku ce na iya hadin fada, ai da sai in yi musu wakar mu ta tasuniya, wato: KURTU BANBAM, KURTU! KURTU MACI FADAWAN SARKI, KURTU MACI SARKIN MA KANSA! Kai shi ke nan idan mai wutsil-wutsil na cikin kurtu ya lakume fadawan babban mutum mai rawani, ai shi ma uban tafiyar ba ya sha ba. Ni dai na roki Mai-duka ya kare mana Maimartaba Muminin Babban mutum mai rawani na birnin Dikko da Maimartaba Masanin Sisi-da-sisi na birenin Dabo da Mai alfarma Ja-gaban Masu fuskantar alkibla don kadaita Mahalicci da ibada da ke birnin Shehu Mujadaddi bini Fodiyo da Shehun Bararon-nono da ke jan ragamar al’umma a birnin su Alan-guburo. Su kuwa Dogari da Kofaton majalisa idan har ba su tuba ba, sai mu yi fatan aniyarsu ta bi su. Kuma wajibi ne a kan Haurobiyawa su daina bai wa masu tafka ta’asa damar damalmala al’amura a kasar nan.
Kundin baje kolin bana har samartakar kusu da rangwadar ’yan mata jaba da gafiya aka yi masa, inda ya yi batan dabo. Ni dai ban taba ganin kundin baje kolin Hauro da aka taba yi masa walagigi ba irin wannan. Kodayake an ce, har su ma ’yan majalisar tsofaffin kasar Haurobiya suna da hannu a wannan tabargazar da aka tafka, har ta kai ga wasu sun jefa azargagiyar zargi a kan Akuyar-maman-daudu, mai taimaka wa Ja-gaba Saurayin-kirinki. Kuma a da shi ne mataimakin Dauda-mai-maki, tsohon Shugaban Majalisar Tsofaffin Haurobiya.
Haurobiyawa duk iskancin da aka ce Akuyar maman-daudu ta tsuwurwurta ba zan yi mamaki ba, domin a wannan farfajiyar makaranta mun san cewa, ita ’yar iska ce, kodayake daga bisani mun fasko cewa, ita JAKADIYAR SHEkE AYA ce. Mun kuwa fasko matsayin wannan akuya ne, domin an ce karshen ISKANCI bindin AKUYA. Akuyar-maman-daudu dai ta taba bijiro da bukatar ganin an mayar da UWARGIDA ta zama UWARGAdA, wato iyayen giji ko adon-gari su zauna kara zube, ba a karkashin jagoranci ja-gaban iyali ba, sai abokin holewa, su yi ta gada, kai har ma cewa ya yi duk mai bukatar sheke aya da cin gashin kanta lallai a bata lasisi. Haurobiyawa kun ji fa irin shagabannin namu. Shi ke nan LADO da OKONKO da LASISI kun yi CANJARASI.
Batu na ingarman karfen karafan titin dogo idan har muna son gyara, ba ’yan gyare-gyare irin gyare da kurege ba, wajibi ne gama-garin al’umma su daina bai wa miyagu damar wakilci ballantana su yi rafkiyar kan mai uwa da wabi. Sannan wanda duk ke son gyara idan har ya tabbatar ya tafka ta’asa a kwanon tasa, to lallai ya nemi afuwar al’umma, domin ta Mai-duka mai sauki ce matukar an cika sharuddan tuba.
Masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a wannan farfajiya ta Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, ina da tabbaci idan har aka tuntubi Malam Na-kwaciri game da sharuddan tuba, zai ce muku: WA AMMA SHURUddUD TAUBATI, AN NADAMU ALA MAFATA, ALLA YA UDA ILLA ZAMBIN, ma’ana dai yin nadama kan aika-aikar da mutum ya aikata, sannan ya tabbatar wa kansa cewa ba zai sake komawa zuwa ga zunubin ba. Wannan karatu dai yana nan cikin Littafi Lahallari. Kuma ina da tabbacin cewa wannan ka’ida ba ta saba wa kowane addini da ke son mutane su zama NAGARGARU, amma  ba FANdARARRUN KANGARARRU ba. Kai hatta tsarin al’adu na matukar son mutane su rika aiwatar da kyawawan ta’addu. Saboda haka Dogarin wakilan rafkiya ka tuntubi Kofato kan lallai ku yi tuba na gasken gaske, amma ba waskiyar wa-ka-ci-ka-tashi  ba.
Lallai lokaci ya yi da jagororin al’umma za su daina cusa karya da karairayi a kundin baje kolin Hauro, don kawai suna hankoron haurewa da matsabbai, su jefa gama-garin al’umma cikin haure-haure da hauragiya a kasar Haurobiya. Idan kuma suna ganin kafafen yada kwakwazo za su cece su, to a ci gaba da cakusawa; a ci gaba gashi, suya kuwa sai ranar sallah.’ Muna neman tsari daga afkawa RUkUkIN RAFKIYAR RAFKANANNU.

 

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited