Sunkurun saraf-na-sadaf
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Sunkurun saraf-na-sadaf

Na dade ban ji an shigo unguwar mutane a Haurubja an sungumi kurkurido ko baburido an arce da shi, har said a muka halarci bikin karrama ’yan kwadagon Kamfanin buga amintattun jaridun kasar Haurobiya

, wadanda suka shafe shekaru sili da zagaye zuwa, suna na laluben na-koko, wato dai a ranar sili da manuniyar sama ga watan ruwan bana, muna fitowa daga cikin Otal din ci-da-kanka sai muka tashi da alhini shigar sunkurun da saraf-na-sadaf ya yi wa kurkuridon abokin kwadagon mu, Malam Muhyidin.
Halin da abokin kwadagonmu ya kasance shi ne na rudani da rashin sanin makama, a lokacin da saraf-nasadaf ya samfe da kurkuridonsa, alhali a lokacin mun fito daga wurin biki cike da farin ciki. Shi ken an wannan lamari ya zama WASU NA kWALLARA KUKA, WASU NA RUGUNTSUMIN BIKI. Duniya ke nan, wata rana a sha zuma, wata ranar kuwa sai a kwankwadi madaci.
Wannan dan kwadago na san ya shiga halin ha’ula’i, musamman ma saboda a cikin ’yar kurkurarsa yake karakaina wajen neman abin dundume kururu. Hasalima a wannan shekarar ana kukan matsi da rashin ’yan matsabban sayen abin tuwo, har ta kai ga wasu sun kakaba wa kurungunsu tagiyar Malam Mantau, ta yadda  ba za su taba jin cewa Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ita ce ta yi wa al’umma shigar sunkurun, wajen binne damin matsabban da suka yi sabi-zarce da su, shi ya sa aka kulle kullin dukiya, ta yadda matsabbai ba za su shiga hannun gama-garin al’umma ba. Kuma tsarin mulkin mulaka’u da aka tsuwurta na tsawon shekaru sili da manuniyar sama. Ni dai na cewa tsofaffin shugabannin kasar nan sun taka rawarsu, wasu sun wuce dan-kuntuku da rawa. Baba-ojo dai ya yi rawar banjo, da shugaba ’Yar’bishiya ya kama ragama, sai igiyar mulkin ta zama raga, don bai ma samun damar taka rawar ba, ballantan mu hakakke kykawun takunsa.
Zamanin mulkin ’Yar’bishiya ya dare bisa laulawar laulayi ne, inda lalurar rashin ingancin uwar jiki ta jikkata shi, har ya riga mu gidan dindindin. Masana dai da masu nazarin harkokin dama-dama-da kurda-kurdar siyasa, sun yi masa kyakkyawan zaton cewa, lalurar Marigayi ta yi wa mai dan boto fancal, tunda an san ya kudurci aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa sili da sili. Da mai aukuwa ta dauke rayuwar wannan gwarzon al’umma, shi ke nan sai mataimakinsa ya dare bisa karaga, inda ya rike wa wasu kaho suka yi ta tatsar nonon nagge da karsana, har suka tatse, suka kanjamar da saniyar, amma duk babu wanda ya fasko jirginsu, saboda man tunkuza na tagazawa a wancan zamanin, ta yadda ko karsana ta tsilance, sai su sanya ta dan ciko.
Haurobiyawa da dama ba su san cewa, lokacin da aka yi Gudu-a-loko da su wasu sun fantama, sun yi wadaka, inda suka yi wa lalitar kasa shigar sunkuru, tamkar yadda aka yi wa Malam Muhyidin.
Ko mece ce alakar shigar sunkurubn da aka yi wa abokin kwadagonmu da tatuke lalilitar kasar Haurobiya da marasa kishi suka tafka? Hakika miyagu sun tafka ta’asa a klwanon tasa, har t akai ga sun kasa farfajiyar koyon watsatttsake da buda wagagen littattafai da ke fadin kasar nan, sin kuma jikkata farfajiyar Bokan Turai, ta yadda masu fama da talalar talauci ke zaune cikin kaskanci, su kuwa da zarar sun ji zogi da radadi a kurungunsu, sai su arce kasashen ketare, har sai sun gyagije, sannan su komo Haurobiya, su ci gaba da tsuwurwurta tsiyataku.
Kowa yasan mnuna fama da DAFDALAR DAULAR DALA ga RUkUkIN RAFKIYAR RAFKANANNU ga Haure-haure da hauragiyar Hauren-Danja, sai yamutsin masu BIYAN-FURA da ya yunkuro kwanannan. Gama-garin al’umma sai suka-da-burtsatsen maganganu suke yi wa Baban-burin-huriyya, kan lallai ya yi hanzarin saisaita TAbARGAZAR da aka tafka ta shekara sili d amanuniyar sama cikin shekara sili.
Koma dai wace irin shigar sunkuru suka yi wa dukiyar kasar nan, babu wanda zai musanta cewa, sun yi sandar saraf-na-sadaf, inda suka mamayi kowa, har ta kai ga tun kafin mulki ya subuce musu an baza sunaye su: Santala kwaiduwa da Mace-da-zane da Baudadden Joji. Kai shi kansa Loma-a-murde jagoran Hukumar Gogarma sha gwagwarmaya da arangama da masu fashi da mukami ko da dabara. Jerin miyagun da suka tatuke kasar nan, sun yi matukar kokarin ganin sun mayar da Loma-a-murde ya zama garjejen MUZURUN LAMI, shi ya sama ya kasa katabus.
Batu na ingarman karafan kwangiri titin dogo, ta’asar da ’yan watanda suka tafka a baya illarta ce muke fafatawa da ita. Haurobiyawa tabahuwa ta taba al’umma a mulkin Baban-burin-huriyya, musamman yadda nike jin wadanda ba su cancanta ba, suna ta rusa kuka. Haurobiyawa, wani abin farin ciki, shi ne, kafafen yada labarai a kasar Haurobiya sun sha ruwaitowa daga bakin Madam In-gwangwaje-in-wala cewa, Gudun-lokon da aka yi da Haurobiya shi ne sanadin jin-jikin da ake yi. Kowa dai ya san wannan mata ita ta rike turakar sarrafa dukiyar kasar Haurobiya har sau karamin lauje. Domin ta taya Baba-ojo rawar banjo, sannan Shugaban Jona-tantin mulki da Gudun-loko ya sake jajubota, don ta agaza masa wajen SAMFEWA da matsabban al’umma. Tun da bai ce uffan ba, har sai da al’umura suka rincabe.
Lokaci ya yi da za mu daina ihu da karajin banza da wofi. Kamata ya yi masu dan abin hannunsu su tausaya wa marasa shi. Hukumomin gwamnati kuwa wajibi ne a kansu su fitar da al’umma daga duhun kai, ta yadda idan ana kwakwazon ganin kowa ya fantsama cikin gayauna ko limbi-limbu a cikin lambu, sai a agaza da maganin kwari da takin zamani. Kodayake wanda duk ya samu damar dibar gararumar takin juji da kashin nagge da karsana da bujimi, kai har ma da na tsuntsayen miya, sai ya yi hamdala, domin garka da gayaunarsa za su bayar da yabanya da dimbin amfani a bana.
Baban-burin-huriyya da Usainin-babajon Haurobiyawa, ku kara fafutikar ganin kun kare dukiyar al’umma a cikin gida, ba lallai sai a kungurmin dajin SAMAN-BISA ba, musamman jin cewa kun karya lagon masu fafutikar hana Bobo da kwambon Bokoko. Sannan wasu na kara yin kiraye-kirayen ganin an aiwatar da hukumar daidaita farashin kayan masarufi, ta yadda gama-garin al’umma za su iya yin cefane kayan masarufin da za su sarrafa don dundume kururu. Koda an aiwatar da wannan shawarar akwai bukatar al’umma su koyi ririta dan abin hannunsu, su daina fariya da tunkahon almubazzaranci. Uwa-uba wanda duk ya mallaki randa da tulu, to ya tuttulo wa dan uwansa ya na kwadi ya kwankwada don gudun kishi ya yi masa kisan mummuke; mai tarin tufafi ya kamata ya taimaka wa mai yagaggar taguwa; mai kewaya gari a cikin kurkurido da shorido-shorido ya agaza wa wadanda ba su da halin karaikaina a ababen hawa. Ni dai zan karkare shawarwarina da bijiro muku da labarin wata BAJAMUSHIYA da ta shekara ba ta kashe ko kwandala ba, wai don kawai ta ji yaya matalauta ke fafatawa da al’amuran rayuwa. Sai a bibiyi tsafaffin dab’in Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, musamman shafukan labaran ban tajibi da suka taba bijiro da batun yadda Bajamushiya ta kasance tsawon shekarar ba ta yi mu’amala da matsabbai ba, wai don gwajin rayuwar marasa hali, har ma ta shuka shakushe, don dundume kururunta, ta yadda ba sai ta shiga kasuwa cefane ba. Mu dai taya Baba da addu’a, mu tausaya wa junanmu; mu ririta dan abin hannunmu. Sannan mu nemi tsari daga sharrin SUNkURUN SARAF-NA-SAdAF!

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited