Dawurwurin durwa
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Dawurwurin durwa

Tun farkon makon da ya arce aka samu wani Mista Ci-wake da ya kamu da ‘DAWURWURIN DURWA, har ya karke da kakaba wa durwan kolonsa lakabin BABAN-BURIN-HURIYYA, al’amarin da ya janyo jami’an tsaro masu takun dan kulki dakon giwa hula bugu da kari suka danko shi.

Batun mai dawurwurin durwan kolo ya kai kololuwar daukar hankalin al’ummar kasar nan. Domin na ji wai har Fuffuken-fankan-fayau, tsohon bututun-batutuwan Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, ya yi katsalandan cewa, an sha dura wa shugaban Masu gudun-loko ashariya, amma sama da kasa ba su taho mu gama ba.
Fuffuken-fankan-fayau a Haurobiya dai an san ya taba rike mukamnin ministan sufurin tsuntsayen sama, inda ya yi sama-da-fadi da damin matsabbai. Kuma wannan lamari na fuffuken fankan-fayau, shi jiga-jigan mai dan boto suka yi amfani wajen yi masa yankan baya, har ya tsorata, inda ya fice daga jam’iyyar mai alamar tsintsiyar tsiyata miyagu da share kazantar cututtuka, don magance radadi da ciwon kurungu. Don haka ban yi mamakin jin cewa, fuffuken-fankan-fayau yana goyon bayan Ciwake, wanda yayi ikrarin kakaba wa durwansa lakabin sunan shugaban kasar Haurobiya. Wani sakarcin da ya tafka shi ne, wai ya furta cewa, an taba kiran shugaban gudun-loko da sunan AKUYA, amma bai ce ko uffan ba.
Batu na ingarman kwangirin titin dogo, ya kamata Fuffuken-fakan-fayau da sauran masu sha’awar tabargazarsa su fasko cewa, ‘ai wargi wuri yake yi.’ Baban-burin-huriyya dai ba tsaran ku ba ne, don haka sai a fasko cewa ‘na kwadi ba tsaran Kwando ba ne,’ kamar yadda Malam mai yaren Hau-hau wajen hawansa ba tare da sa-in-sa ba ya tabbatar mana. Kuma don an kira ubangidanka da sunan dabba ya kyale, ai ku kuka jiwo, tunda mun san cewa har AKUYAR-MAMAN-DAUDU kuke da ita a jerin jiga-jigan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge. Sannan har yanzu bai daina tsiyataku a majalisar tsofaffin Haurobiya, inda har taimaka wa wakilan rafkiya ya yi wajen tsuwurwurta cushe magudin murgude matsabbai a kundin baje-kolin Hauron bana. Kodayake dai darasinmu na yau ya karkata akala ne a kan dawurwurin durwan kolon kalallame Ci-wake.
Mista Ci-wake bai isa makarantarmu ta Dodorido ta bata lokaci a kansa ba, tunda mun san cewa, ‘sai an kula tutu yake doyi.’ Kuma ko ba komai ai an ruwaito cewa, mutane sun zagaya sun aika da durwan kolon ci-wake gidan dindindin. Don haka a matsayina na Babban direban allin farfajiyar Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, ina ganin an kasha BOS a wannan majigin. Ni b abu abin day a shafe ni da Ci-wake koda ya kakaba wa durwansa lakabin DODO, ni ma sai in dauko na maigidansu in yaba, wai sunan wani shafawa DANGWALI-YAbA.
Haurobiyawa ku tuntubi Bokayen Turai da ke kula da masu tabin kwanya, kai har ma masu inganta uwar jikin biladama za su tabbatar muku da cewa, ‘idan kolo mai tabin kwanya ya gantsara wa mutum cizo, to ya shiga halin ha’ula’i, domin ba a san inda cutar za ta tsaya ba. Ko durwan kolo ya ciji Ci-wake da Fuffuken-fankan-fayau ko ko a’a, wadannan miyagu dai suna cikin tsaka mai wuya, tunda Gwamnatin Baban-burin-huriyya ta sanya Gogarma Iro Mugun madambaci ya cafko samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya. Uwa-uba an toshe ramukan burgu, kuma duk wanda ya leko da kurunsa za a kwafde shi, idan kuwa ya kuskura ya koma ciki za su yi arangama da samandagarin samarin kusu. Shi kenan sai mu ce Gogarma ka ci gaba da arabngama da gwagwarmaya da masu fashi da mukami ko da dabarbaru.
’Yan makarantarmu abin da kawai nike so ku fasko game da DAWURWURIN DURWA, shi ne miyagun da suka tafka ta’asa a kwanon tasa, sun cilla durwan farauta ya yi wa Gwamnatin Baban-burin-huriyya fancal, ta yadda ba za ta samu kwarin gwiwar cafko su ba, ko ma ta kakaba wa kurunta tagiyar Malam Mantau. To kuna ji dai Baba ya ce, babu gudu ba ja-da baya. Ku kuwa miyagu lamarin duniya ya zame muku, ‘gaba kura baya sayaki.’
A wata mahangar kuwa, za a iya danganta ta’asar masu dawurwurin durwa da wakar shahararren mai kwanyara wakar nan dan asalin Maradun da ke  Jihar Zaman-fara, inda a wata waka da ya wake Babban mutum mai rawani na kasar Muri ya furta cewa:
“Idan ka ji KARNAI suna haushi,
In ba kura ta biyya nan ba,
Watakila bakin barayi ne.’
Lallai yau sai a yi mini uzuri, domin zan jefa azargagiyar zargi a kan Baban-burin-huriyya, inda nike jin cewa, watakila ya cinna wa su Ci-wake kura, alhali su sababbin samarin kusu ne, shi ya sa suka shiga DAWURWURIN DURWA, ga shi dai sun dabarbarce, har Fuffuke-fankan-fayau na neman ya fisge su.
Ni dai ina kira ga masu yaren Hau-hau wajen hawansa ba tare da sa-in-sa ba, kada su biye wa Ci-wake ko Fuffuken-fankan-fayau ballantana a tada yamutsi. Domin ita rayuwar nan da kuke ji da gani, idan mutum ya tafka ta’asa a kwanon tasa, yana iya haifar da yakin basasa, amma idan aka kama shi, aka dan lallasa shi, har ya yi laushi, ai shi ke nan babu bashi. Nan da ’yan kwanaki za ku ji an daina DAWURWURIN DURWA, sai kuma a sake wasu dabarbarun dabarbarcewa, har a susuce, a sukurkurce, a balbalce. Muna dai neman kariyar Mai-duka daga DAWURWURIN DURWAN KOLO.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited