Sakonnin ’yan makaranta 2
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Sakonnin ’yan makaranta 2

A wannan makon muna dauke da sakonnin daliban makaranta, musamman daga Jihar Da-Fullo-ke-damawa, inda wasu suka yi sharhi kan Saraf-na-sadaf, wasu kuwa sun bukaci a bude shafin fuskantar-bokoko a mashakatar lilo da tsallake-tsallaken na’ura mai dunduma kwanya. Batu na ingarman karafan kwangirin titin dogo, akwai bukatar kowane Bahaurobiye ya himmatu ka’in da na’in wajen agaza wa kasar nan, ta yadda za ta kai ga gaji. daukacin tsilli-tsillin matsalolinmu na zaman-takewa, mu mayar da zamantakewa kyakkyawa; a tsimi da tanadi kuwa, sai mu kauce wa tsarin tsimi da ta’adi, ga lukudi, ga lakume kudi; a tsarin wasan Samson-siya-siya da ake dama-dama da-kurda-kurdar siyasa, sai mu yi yunkuri karkacewa daga titin DAMO-DA-KURA-DA-dIYA.
‘Yan makaranta hakkinku ne ku bayar da amsar wasu tambayoyin da aka bijiro da su, don gudun kada mu kargama wa kurkuridonmu giyar dabaya-dabaya. Mu hadu a darasi na gaba. Abu mafi a’ala. Shi masu bijiro wa makaranta da tambayoyi su sanya adireshin akwatin na’ura mai kwanya ko kurtun Magana na halo-alalo.

Martani: Saraf-na-sadaf
Assalamu alikum warahmatullah. Ina mika gaisuwa ta musamman da jinjina mara iyaka ga babban direban allin wannan makaranta mai albarka ta Dodorido, tare da daukacin dalibanta. Bayan haka, ina son in yi dan tsokaci ne a kan darasin da Malam ya yi a makon da ya arce mai taken “Sunkurun Saraf-na-sadaf,” lallai kuwa Malam ya yi darasin da ya dade yana min kaikayi a cikin ruhina dangane da yamadidi da gutsuri tsoma hada da surutu rututu kamar aku, kai wasu ma har da tofin Allah tsine suke yi a kan wannan gwamnati ta Baban-burin-huriyya da mai agaza masa, wato Usainin-Babajo, cewa, sun kasa yin komai don shawo kan al’amura a kasar nan, saboda talakawa su samu saukin rayuwa, musamman ma halin da ake ciki na tashin kayan abinci.
A batu na ingarma karafan kwangiri titin dogo, idan aka ce za a bayyana yawan ta’asar da wasu suka tafka a kasar na sace dukiyar kasar nan, to lallai za a cike daukacin shafukan Amintacciyar jiridar ku ta Haurobiya da ake bugawa a Haurubja babban birnin Haurobiya, tun daga farkonta har izuwa karshenta da watsattsakewa ba tare da an kammala bayyana yawan dukiyar Haurobiya da masu fashi da mukami suka sace ba, tun daga lokacin da jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ta yi tana mulki, har na  tsawon shekara sili da manuniyar sama.
Saboda haka lallai a nan zan iya cewa Haurobiyawa sun kasa yin na damo domin kurbar romon damo-da-kura-da-diya, domin ba zai taba yiwuwa ba a ce a cikin shekara sili kacal wannnan kasa ta dawo cikin hayyacinta a cikin kankanen lokaci ba. Kai bari in fada muku ku ji, mu fa da muke Arewatawan gabashin kasar Haurobiya, mun fi kowa ganin canji a cikin wannan gwamnati ta Baban-burin-huriya, saboda a yanzu mun daina kwana cikin fargaba da faduwar gaba na tsoron kai mana hari daga fandararrun mutane masu kokarin hana bobo da kwambon bokoko. Kuma lallai a yanzu jama’ar garin su Alan-guburo da dama sun yi koma sana’ar na-duke a garuruwansu, wadanda a baya can musamman ma lokacin da muke gudu-a-loko wasu na ta kokarin Jona-tantin-mulki suna ta saraf-na-sadaf da dukiyar kasar ko a jikinsu. A gefe guda kuwa ana ta kashe bayin Allah, ana zubda jini babu gaira babu dalili.
Ya ku Haurobiyawa ku yi wa kanku karatun ta-nutsu kada ku mance ku ari faden Malam Mantau, ku biye wa wasu miyagun mutane da ba sa fatan ganin kasar Haurobiya ta samu kwanciyar hankali da wanzuwar tattalin tsimi-da-tanadi na kasa.
Ina kara kira gareku ’yan uwana daliban wannan makaranta da dukkan saura Haurobiyawa da mu koma wajen Mai-duka mu roke shi da ya yi mana maganin wadannan matsalolin da muke ciki, ba wai mu buge da surutu da zage-zage har mu hada da hauragiya ba. Wassalam! Ku huta lafiya.
Daga Uncle Bash, a Jihar da Fullo-Ke-Damawa, This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it. 07037133338.

Jajen Saraf-na-sadaf
Assalamu alaikum. Bayan gaisuwa irin ta masu kadaita jalla gwani wajen bauta.
Ina mai durkuso cikin tawabu’u wajen gaida da babban direban alli kana jagoran watsatstsake a farfajiyar Amintacciyar jaridar Haurobiya da Haurabiyawa ke marmarinta wajen daukar ilmu.
Ina yi maka fatan Jalla gwani ya kara maka basira da hikima, wajen daidaita mana kwanyar mu. Amma ba’adu, bayan haka, a madadin ni da daliban Jihar da Fullo-ke-damawa muna masu jajanta wa abokin kwadagon ku, wato Malam Muhyidin game da aika-aikar da ‘YAN SUNkURUN SARAF NA SAdAF  suka yi masa. Muna fatan Rabbi ta’ala ya kiyaye na gaba ya mayar da masa mafificin abin da aka rasa.
Ya ku ‘yan makaranta da fatan kuna cikin wadatar lafiya da wadataccen Hauro a hannun ku tare da daukar darasi daga Malam Dodo, ina kira da babban sauti ga ‘yan makaranta ya dace muke motsawa don inganta tafiyar makaranta, amma shiru kake ji kamar mai ilmu ya hadiyi shirwa. Hobbasar dodanni cikin dakin darasi shi zai kara wa Malam kwazo wajen bayar da darasin da zai kaimu gano har ma mu iso birnin ka-waye da tsaftatacciyar kwanya
Malam Dodo.
Ahabdi bee fukarabe Allah balluma
Daga SABIU UBA YOLA
07032385544, Jagaban jihar da Fullo-ke-damawa This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Gaisuwa ga Malam Dodo
Assalamu alaikum, Malam Abubakar barka da safiya. Gaisuwa ta musamman da fatan an yi sallah lafiya
 Daga Hussaini Musa Yamusa This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.
 
Shafin fuskantar-bokoko
Assalamu alaikum
Bayan gaisuwa da fatan alheri ga jagoran wannan makaranta mai albarka ta Dodorido.
Batu na ingarman karafa ni sabon dalibi ne a wannan makarantar mai tarin albarka, kuma dan aji sili, amma duk da haka ina da wata shawara ga malam  shin me zai hana dalibai irinmu in da hali a bude mana aji a na musamman a fuskar takarda (facebook), domin cillo tambayoyin mu ga malam da kuma tattaunawa tsakanin ’yan makaranta don kara dankon zumunci tsakanin dalibin da ke wata jiha zuwa wata daban.
Allah gafarta Malam idan muka lura za mu fasko babu alaka tsakanin dalibin da ke Jihar Da Fullo-ke damawa da kuma takwaransa wanda ke Jihar Tumbin giwa ko Haurubja.
Daga karshe fatan alheri ga daukacin dalibai da ke jihohi kofar hanci da manuniyar sama, hada da Haurubja.
YAHYA SA’ID
08163499676
Daga jihar da fullo-ke-damawa.

Lissafin makaranta
Assalamu alaikum. Hakika ina jin dadin makarantar nan mai koyar da Hausa mai zurfi. In da hali ina so ku koya min lissafi daga daya zuwa goma. Bugu da kari a gaya min yadda ake kiran Jihohin Haurobiya guda talatin da shida.
Allah ya kara daukaka.
Daga  U.S. Muhammad Yola.
08186097646

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited