Raboti Mun-ga-gobe
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Raboti Mun-ga-gobe

Kurkum
Kurkum, kurkum kum!
Kwaramniyar kurum!
dandasa kwalliyar kurum
Da takun kunkurunkurum

Wasan ’yar burunburum
’Yan bumburutu buruntun burum
Sun burma burum
A cikin tafki tsundum
Dodoridon diskon dundumdurundum

kurkurido
Da baburido
Kekerido
Laulawar dodorido
Laulayin shorido

Tsaron kan iya sai Dodo
A kifa wa miyagu Kwando
kyale su da harbin kudan tsando
A shiga ruwa a tsinko bado
Wani aiki sai Lado

Shirmen shoridon Na’ibin bawa
Ezagareb! Ezagareb!
Jin jim jim!
Na tsinci kaina a garin Kujam
Haka na yi ta fafatawa

Rodi da sassaben titi
Rawar dandi da sassarfa a titi
Rikirkitaccen zare afatati
Kai a rike mini baiti
Ko na samu saiti

A kandamo kindirimo kundum
Madara kitif-kitif
Tsalan nono ya ciko taf
Shakurukundum
Baba ne shakundum

A dundume kururu dum
Da baki sai ku yi gum
Lullumin lumana lulum
kwalkwalin kurungu kwalam
Ku sha kuruminku kurum

Narandar Moda
Talakawa sun dandana kuda
Gandun Gandi ba a gada
Ba a dafdalar turke ma’aurata da guda
Ko tamnar marau-marau gyada

Raboti Mun-ga-gobe
Gayaunar Turawa tushen tuntube
Harkar na-duke ta cabe
Al’amura sun rincabe
Gaya wa Malam Bakabe

A Zaman-gidan-buwai
Talakwa na wai-wai
Raboti ya kawar da kai
Tsageru ’yan garai-garai
Shalelen Turawan Turai

Yaya za a shuka tsirrai
An tafka ta’asar son rai
Raboti ya yi kuskure
Kowa na laluben kirare
Bumburutu buruntun satar mai

Baban-burin-huriyya
Ga darussan duniya
A gandun Gandi yadda ta kaya
Narandar Moda ya yi tsiya
Ya janye abin saye da biya

Can a Somaliya
Talakawa na shan wuya
Dalilin tada kayar baya
Wasu sun hau dokin wuya
Na-kwadi sai an yi uwar tafiya

Masana
Masu yawan magana
An jiwo ku a Ghana
Burinku a wawushe karfanfana
Nufinku cin amana

A daina shaci fadi
Ra-mirododo
An girma an yi gododo
Shudi-shudi
Da rodi-rodi

Masu hannu da shuni
A daina wuni-wuni
Masu tabargazar karni
Sun haure da Hauron birni
Wai su gwanayen gini

Tabargazar Anyi-mimi
Masu fashi da makami
A’a, ’yan fashi da mukami
Sha-wuya ke rike barandami
Dabarbaru ne a cikin dundumi

A wangale shafukan littattafai
A baje mana ilimi a faifai
Za a kyallo mai yawo da kamfai
Ta haka za a fahimci malamai
Masu manufa takamaimai

Daga Harubja zuwa Honolulu
A falle mana shafukan mujallu
Har da makalu
Mu fahimci al’amura fululu
Mu kwankwade na kwadin tulu

A yi ayyuka a aikace
Babu ka ce-na ce
Babu bambance-bambance
Da mun kulla kawance
Sai mu ce - Baba sabi-zarce

Iya ta iya rumace
Rama da garin gero a kawance
’Yan dugwi-dugwi sai da kwatance
A kwada mana mu tantance
Dattijo yi maganin mai kwace

Dodorido mai yawan zaurance
Malam ka cukurkuda zance
Haurobiyawa na ta habaice-habaice
Kada a bari al’amura su sukurkuce
Ba ma biyayya a makance

Masu yamadidi
Fullo kuke yi wa kaudi
Makekiyar makiyayar fullo
Zamani ya zo da sabon salo
A magance wa al’umma radadi

Tiren-taliyar Maman-tine
’Yan sisi ta yi kane-kane
Kurtun maganar nawa ne
Ai sai wane da wane
Haurobiyawa na sane

Da fatan an gane
Baba ya fara gine-gine
Babu mai yi mana gatsine
Kada a ce a yi nune-nune
Komai na nan a bayyane

Haurobiyawa na ta kwakwadzon ganin Baba ya jinka musu damin matsabbban da ya karbo daga samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya, amma ya yi musu biris. Hasalima wasu masanan sai hajijiya suke yi wajen rikita al’umma, musamman idan sun hango cewa gwamnatin Baban-burin-huriyya ta tabo inda ba sa kaunar a taba. Don haka ma suke ta kwakwazo game da matsalolin tattalin dukiyar kasa.
A iya fahimtata idan gwamnati tace za ta kyautata wa talakawa ko halin kaka, to akwai yiwuwar a karke da kwata abin da RABOTI MUN-GA-GOBE ya yi a Zaman-gidan-buwai, inda ya kwacbe gayaunar Turawa ya tura wa talakawan da ba su iya sana’ar na-duke ba, har ta kai ga an kassara harkar a kasarsa. Shi ya sa nike ganin yadda talaka ke da kaso a dukiyar kasa, shi ma mai hannu da shuni wajibi ne a kiyaye masa muradunsa, wadanda ba za su cutar da al’umma ba. Domin adala ba ta ce a ware wnai rukuni na al’umma ba, a ce shi za a fifita, illa dai ana iya fifika bukatun al’umma gwargwadon muhimmancinsu. Sanin kowa ne a yau, tunda Gwamnatin Tanzaniya ta takura wa dangatan kasuwa, wajen samar da makamashi, tuni ya garkame masana’antarsa. Kun ga ken an a irin wannan yanayi, gwamnatin kasar da al’ummarta su za su fi jigata, tunda za a samu karin masu zaman dirshan da kasha fatari.
NARANDAR MOdA, wanda shi ne Farin-ministan Gandun-Gandi, a kokarinsa na farmakar masu kauce wa biyan haraji da masu kwashi-kwaraf, ya karke da jefa talakawan kasa cikin jangwam.
Bisa la’akari da al’amuran da ake tsuwurwurtawa a fadin duniya, nike ganin ya kamata kowa ya yi kama-kama a kasar nan, wato duk sa’adda mahukunta suka bullo da wani tsari ko shirin inganta rayuwar al’umma, lallai a samu masu karfi su kwatanta, tunda Gwamnati ba za ta iya bai wa kowa abin laluben na-koko ba. kila bisa wannan fahimta ce ta sanya ake ta fafutikar komawa fardar garka da gayauna.
Kowa yana sane da yadda DAFDALAR DAULAR DALA ta kassara dukiyar kananan kasashe, musamman wadanda ke nahiyoyin Ifrikiya da Asiya. Kuma TASKUN TURKA-TURKAR TUNKUZA ta yi mana illa a Haurobiya. Wannan ne dalilin da ya sanya nike ta yayata muhimmancin hada karfi da karfe a mafi yawancin darussan wannan makaranta. Kada mu yi adawar neman dawa; adawa in ba dawa, ai sai a shiga dawa.
’Yan makaranta mu himmatu ka’in da na’in wajen nakaltar managartan sare-tsare, ta yadda za mu nusar da hukuma yadda za a inganta su, amma ba mu karke da soki-burutsu ba, alhali ba mu da wata dabarar tsuwurwurtawa da za ta fitar da mu daga duma. Aikata sabanin haka kuwa, ku aiwatar da dabarar Mista Raboti Mun-ga-gobe, zai haifar da rabon-bati, ta yadda idan gobe ta zo, sai a yi ta garamba a titi.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited