Rusa Hisba ya haifar da cece-ku-ce a jihar Sakkwato
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Rusa Hisba ya haifar da cece-ku-ce a jihar Sakkwato

Rusa shugabannin Hukumar Hisba ta Jihar Sakkwato bayan kwana daya da karbe kayan kidan bikin ’yar Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya haifar da cece-ku-ce a jihar.
Kwamadan Hisaba ta Jihar Sakkwato Dokta Bello Kasarawa ya ce takaddamar ta faro ne saboda jami’an Hisba sun kwace kayan kida a wajen bikin ’yar Gwamnan saboda sun saba wa shari’a. Ya shaida wa manema labarai cewa sun so su kama makidin da hannu amma ya ranta a na kare, amma kayan kidan da aka yi amfani da su a wurin liyafar abincin dare kafin daurin auren suna hannunsu.
Ya ce abubuwan da suka faru a wurin cin abincin sun saba wa Musulunci kuma su an Kafa su ne don su kawo gyara kan duk wata badala da ake yi a jihar. Don haka ba za su bari wadannan abubuwan suna tafiya haka ba. Ya ce duk kayan da suka kama na kidin za su lalatar da su ne yadda ba za a sake amfani da su ba.
Sai dai kwana daya da fitar labarin sai ga labarin dakatar da hukumar ya watsu a jihar in da Kwamishinan Harkokin Addinin Musulunci Alhaji Mani Maishinko Katami ya ba da sanarwa a zantawa da manema labarai a Lahadin da ta gabata. Ya ce sokewar ta biyo bayan rikicin da ya dabaibaye hukumar ne kuma ba a dauki wannan hukuncin ba sai dai aka yi taro da duk bangarorin tare da Ma’aikatar Shari’a ta Jihar. “An yanke hukuncin ne kan bangarorin Hisba uku sun kasa daidaita kansu tsawon lokacin da aka ba su na su zama daya don aiwatar da aiki mai inganci na hadin kai. Gwamnati ta ba su fiye da shekara daya amma sun kasa aiwatarwa wanda hakan ya saba wa dokar da ta kafa hukumar, ga takura wa jama’a ba da hakki ba da suke yi, wanda an yi ta kawo koke-koke kan lamarinsu gare mu suna ke ta haddin mutane,” cewar Kwamishinan.
Alhaji Mani Katami ya umarci shugaban daya bangaren da kayan aiki suke hannunsa ya mayar da su zuwa ofishinsa kuma za su sanya tsari da zai hade shugabancin hukumar.
Sai dai bangaren Dokta Bello Kasarwa bai aminta da sun aikata ba daidai a dukan kamen da suka yi da suka kai dubu tara ba, sannan hukuncin da gwamnati ta dauka abin mamaki ne, amma zai mika kayan aiki ga gwamnati don shi mai bin doka da oda ne.
Ya nuna aikinsu mai kyau ne sai dai wadansu jami’an gwamnati ba su jin dadin abin da suke yi.
Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan na Sakkwato, kuma Limamin Farfaru, Sheikh Abubakar Jibril, a tattaunawarsa da Aminiya kan dakatarwar ya soki hakan inda ya ce, hukumar ba ta da alaka da siyasa aiki ne na Musulunci, Sheikh Abdullahi Fodiyo ya yi rubutu kan aikin Hisba na hani ga sabon Allah da horo da bautar Allah.
Ya ce in wani ya hana ko ya soke ko ya rage mata karfi hakan na iya kaiwa ga kafirci, don Allah da ManzonSa suka ce a yi wa’azi.
Sheikh Abubakar Jibril ya ce: “Jami’an Hisba mutane ne suna yin kuskure, kuma in sun yi, ya kamata a kira su ne a gaya masu ba wai daukar wani mataki na daban ba. Hisba da dokar da aka kafa ta a gwamnatin da ta gabata abin yabawa ne, tarihi zai ci gaba da gode musu wannan abin da gwamnati ta yi ba daidai ba ne, muna yi musu nasiha su sani hakan na iya kaiwa ga ridda.” Ya nuna mamakin kan yadda bayan ba da sanarwar dakatar da Hisbar wadansu batagari suka je ofishinta sun balle kofa suka kwashe kayan kidan asharalle da aka kama wurin bikin ’yar Gwamnan.
Ya ce Hisba ta yi wa jihar aiki, inda ya ce akwai wani boka da aka kama mai yi wa mata tsafi, aikinsa ke nan yi wa matan manyan gari sihiri kuma duk wadda zai yi wa aiki sai ta yi zindir ya yi mata rubutu a farjinta don samun biyan bukatunta. Ya ce ko saboda wannan ya kamata manyan jihar su gode wa Hisba da ke kokarin hana matansu zuwa wurin tsafe-tsafe, maimakon su bari matan su zuga su su dakatar da Hisbar. “Muna zargin wannan zugar mata ce kuma ba a hana mutum zargi, ku sani fa bokayen suna sanya mata dibar jinin hailarsu su zuba a abincin maigida ya cinye, duk bokayen an kama su a hannu ba zargi ba, ya kamata Gwamna ya sani Hisba shi take yi wa aiki da mu talakawa, kuma  aiki a bai wa mai yin sa da sha’awarsa zai fi kyau. Don haka shugabannin farko a bar su kada a canja su a Hisba in ko aka canja Hisba za ta koma ’yan amshin shata sun mamaye ta,” inji shi.   
Sakamakon cece-ku-cen da ta biyo bayan matakin na farko ne sai wata takarda dauke da sanya hannun Sakataren Gwamnatin Sakkwato Farfesa Bashir Garba ta bayyana tana cewa: “Hankalin gwamnati ya karkato ne a lokacin da wasu labarai suka rika yawo cewa an soke Hukumar Hisba ta Jihar. Ya zama dole gwamnati ta yi bayani mai gamsarwa kan hukumar da doka ta yi don fita daga cikin rudani. Ba a soke hukumar ba kuma shugabanninta suna nan kan aikinsu da doka ta san da ita. Gwamna ke da damar cire shugaba ko wani mamba kuma ba a yi haka ba, abin da kawai muka sani Ma’aikatar Al’amuran Addini ta yi taro da bangarorin Hisba guda uku kan za su dinke wuri daya don ci gaba da aikinsu da zai amfani mutanen jihar kuma kudirin na nan ana tattaunawa da wadanda lamarin ya shafa don samun nasara,” inji shi.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited