Aliyu Kabir: Mai digirin da ke rayuwa da sana’ar sayar da shayi
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Aliyu Kabir: Mai digirin da ke rayuwa da sana’ar sayar da shayi

Aliyu Ahmed Kabir matashi ne da ya mallaki digiri a fagen karatu, amma hakan bai sa zuciyarsa ta mutu wajen jiran tsammanin samun aikin gwamnati ba, inda yanzu haka yake sana’ar sayar da shayi a Layin Bebeji da ke cikin garin Kafanchan, kuma ya shaida wa Aminiya cewa ya gamsu da wannan sana’a kuma ko ya samu aikin gwamnati a duk inda yake ba zai yi watsi da sana’a ba:

Mene ne takaitaccen bayaninka?
Sunana Aliyu Ahmed Kabir. An haife ni a cikin garin Kafanchan shekara 28 da suka wuce kuma a nan na yi karatu a Firamaren Anglican zuwa Firamarin Waziri Ali, sannan na yi karatun sakandare a GSS Kafanchan. Bayan na kammala da sakamako mai kyau sai na yi jarrabawar shiga jami’a inda na yi sa’a aka dauke ni a Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi kuma na kammala ta a shekarar 2013, kuma na yi aikin hidimar kasa. Na yi digirin ne a kan Ilimin SaninYanayin kasa da Ma’adinai (Geology and Mining). Kafin nan na je Kwalejin Koyon Aikin Kiwon Lafiya ta Jihar Bauchi (Health Tech) da ke garin Ningi inda na yi kwas din satifiket kan muhalli.
Yaya aka yi daga karatun jami’a ka koma sayar da shayi?
Da farko dai sana’ar sayar da shayin nan gadarta na yi wajen mahaifina. To da na duba na ga mu fa ba masu kudi ba ne, kuma ga irin halin da ake ciki sai na tsaya na yi nazari da kyau na ga cewa ita fa wannan sana’ar sayar da shayin da ita aka dauki nauyin karatuna tun farko har zuwa inda ta kawo ni yanzu, to me zai hana in ci gaba da yin ta? Sannan ga shi mahaifina ya tsufa ya kamata na bar shi ya huta haka shi ma. Baya ga haka nan kuma ni ina mamakin wadanda idan sun dan yi karatunsu da bai wuce cikin ludayi ba wadansu NCE suka yi wadansu kuma Diploma, ko ma digirin sai ka ga sun fara fadi suna jiji da kansu suna ganin sun fi kowa, don haka kaskanci ne a wajensu a ga suna wata sana’a da a tunaninsu za ta zubar musu da mutunci. Suna ganin idan ba aikin gwamnati ba, ba abin da ya dace da su. Ni kuma abin da ban yarda da shi ba ke nan, shi ya sa ka ga na kama sana’ar sayar da shayi.
Za ka watsar da sana’ar shayin idan ka samu aikin gwamnati?
Ba zan iya barin sana’a ba. Duk inda na samu aiki ko a ina ne zan san irin sana’ar da zan yi da ta dace da wurin. Ai ita sana’a ba lallai sai na sayar da shayi ba ce, kuma ba lallai sai wanda za ka zauna kai da kanka ba ce. Idan ka kalli manyan shugabannin da muke da su babu wanda ba ya da wasu hanyoyi da ya kafa da ke samar masa da kudi. Aikin gwamnati ba abin dogaro ba ne domin ko nawa kake karba idan ba ka assasa wata sana’a da shi ba da zarar ka bar aikin za ka dawo abin tausayi ne, karshe ma abin da ka tara za ka dawo kana cinyewa. Don haka idan na samu aikin gwamnati zan yi, amma zan samar wa kaina wasu harkoki na kasuwanci da za a rika gudanar mini da su, ka ga kamar yanzu ma da nake sayar da shayi ina da wasu harkokin bayansa. Ina sayen buhunan citta ina aikewa da su jihohin Taraba da Adamawa.
Wane irin alherin da ka samu a wannan sana’a?
Abubuwan da na samu a sanadiyyar wannan sana’a suna da yawa. Na fada maka cewa da ita ce mahaifina ya dauki nauyin karatuna kuma da ita na sayi filaye a Jihar Bauchi da Adamawa. Da wannan sana’a na samu jarin da nake sayen citta nake turawa zuwa wasu garuruwa. Bayan nan ina harkar kasuwanci da dillanci. Yanzu idan kana son sayen kaya ko daga Kano ne kuma ko kayan ya kai yawan tirela ce ina da hanyar da zan sa a kawo maka ko in tura ka wajen da za a ba ka.
Wace matsala kake fuskanta a wannan sana’a ta shayi?
Babu wata matsala da nake fuskanta da ta wuce tsadar rayuwa da tsadar kayayyaki wadda ka ga da muna sayar da kofin shayi hadadde a Naira 80 ne, amma yanzu saboda tsadar kayayyaki Naira 120 muke saidawa, amma duk da haka ba a daina zuwa shan shayin ba.
Wacce shawara za ka bai wa matasa ’yan uwanka musamman wadanda suka yi karatu kan rungumar sana’a?
Kiran da zan yi musu kawai shi ne su tashi su kama sana’a. dan karatun da ka yi kada ya sanya ka girman kai domin mu fahimta fa, shi kansa manufar karatun ba wai shi ne yin aiki don karbar albashi ba. Makaranta tana koya wa mutum ilimin yadda zai sarrafa rayuwarsa ce ta yi kyau, ba wai a wanke kaya a goge a fito ana kwambo ba. Ka tsaya ka duba da kyau duk aikin da ka ga iyayenka na yi kai ma ka kama da kyau, idan ma ba za ka yi irinsa ba, ka nemi wata sana’a don tsira da mutuncinka a rayuwa. Ka ga ko matsalolin da ke addabarmu a Kudancin Kaduna na yawan tashe-tashen hankali ai talauci da zaman banza ke haifar da su. Sai ka ga mutum ya gama karatunsa ya komo yana zama a gindin bishiya wai shi ya fi karfin yin sana’a yana jira sai ya samu aikin gwamnati. Ba alfahari ba, mu idan ka kalli matasanmu a cikin gari musamman a irin wannan lokacin da ake aikin citta za ka ga masu karatun na yi, wasu ma ma’aikata ne wadanda a wuni daya sai ka ga mutum ya tashi da Naira dubu uku nasa. Ka fada min wane karamin ma’aikaci ne yake aikin Naira dubu uku a rana? Sauran kabilun kuwa za ka ga matansu na zuwa ana aikin da su amma matasansu suna can karkashin bishiya suna shan inuwa. Ya kamata a fada musu cewa yin hakan ba zai fisshe su ba.
Mece ce shawararka a karshe ga hukuma?
To alhamdulillahi, kowace sana’a dai ba za ta iya gudana yadda ake so ba, in babu zaman lafiya. Babban abin da ke damunmu a nan shi ne yawan tashin hankali. Akwai wani abu guda daya da duk wani dan yankin Kudancin Kaduna ya sani, shi ne ana yawan samun matsala da jami’an tsaron yankin a duk lokacin da wani rikici ya faru da ya shafi addini ko kabilanci, za ka ga ana zarginsu da taimakon ’yan uwansu a fili. Dalili kuma a nan saboda suna ganin yawancinsu idan ma ba duka ba, kabilun yankin ne. Jawo hankalin hukuma da za mu yi a nan shi ne ta duba jami’an tsaro na ’yan sanda a duk inda ake yawan tashe-tashen hankula inda duk ta ga kabilun yankin sun fi yawa, to ta yi musu
garambawul. Ba muna magana kan jami’an tsaron da aka kawo su aiki na musamman kwanan nan ba ne, muna magana ne kan ainihin zaunannun ma’aikatan da muke tare da su, idan aka yi haka zai taimaka. Sannan a karshe muna rokon gwamnati ta rika tallafa wa masu kananan sana’o’i da isasshen jari don bunkasa sana’o’insu.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited