Bayan shekara 10 babu haihuwa: Matar likita ta haifi ’ya’ya biyar
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Bayan shekara 10 babu haihuwa: Matar likita ta haifi ’ya’ya biyar

Kowa ya yi hakuri bai dace ba to hakurin kadan ya yi inji masu iya magana. Wani kwararren likita a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Kalaba mai suna Dokta  Ekpo Edet, wanda ya shafe shekara 10 da aure ba tare da haihuwa ba, matarsa ta haifa masa ’ya’ya biyar rigis, uku mata, biyu maza. Wannan shi ne karo na farko a tarihi da wata mace ta taba haifar ’ya’ya biyar a lokaci guda a Kalaba. Wakilinmu ya tattauna da Dokta Edet dangane da yadda ya ji da wannan baiwa ta haihuwar ’ya’ya biyar da Allah Ya yi masa. Mai jegon na kwance a asibitin ana ba ta kulawa ta musamman kuma tana cikin koshin laiya kamar yadda mijin ya sanar wa wakilinmu.

Aminiya: Dokta Ekpo barka dai, ashe an samu karuwa. Ko za ka gabatar mana da kanka?
Dokta Ekpo Edet: Sunana Dokta Ekpo Edet,  Likita ne ni da ke aiki a wannan asibiti na Koyarwa na Jami’ar Kalaba.
Aminiya: Ga shi matarka ta haifa maka ’ya’ya biyar rigis. Yaya ka ji da wannan baiwa da Allah Ya yi muku lura da cewa wadansu na kokawa da halin matsin rayuwa, a ce an haifa wa mutum ’ya’ya biyar?
Dokta Ekpo Edet: Ka san ba yadda Allah bai iya ba, na yi matukar farin ciki da wannan baiwa da Allah Ya yi min.
Aminiya: Da ma kun taba haihuwa ne ko kuwa wannan ne na farko gare ku?
Dokta Ekpo Edet: Wato wannan ne na farko a gare ni domin shekararmu goma ke  nan  da muka yi aure da matata. Kullum rokon Allah muke yi Ya ba mu haihuwa, kullum addu’armu ke nan, to ga shi Ya amsa mana Ya ba mu haihuwa. Ya amshi addu’armu Ya yi mana kyautar ’ya’ya har biyar, uku mata biyu kuma maza, kuma dukkansu suna cikin koshin lafiya.Yanzu haka ma suna karkashin kulawar sashen kula da jarirai na wannan asibiti.
Aminiya: An ce matar Gwamnan Jihar Kuros Riba, Dokta Linda Ayade ma ta zo ta ga jariran har ma ta ba da kudin aski gaskiya ne?.
Dokta Ekpo Edet: Eh! Gaskiya ne ta ce ta ba mu gudunmawar Naira milyan daya. Bayan ta nuna mana matukar farin cikinta. Ban da haka ma ta dada bayar da kyautar wasu kudin ma har Naira dubu 500 ga unguzomar da ta karbi haihuwar.
Aminiya: Wadansu idan an haifa musu ’ya’ya biyu ko fiye da haka sukan gudu su bar matan da jariran nasu amma ga shi kai kana ta nuna farin cikinka me ya sa?
Dokta Ekpo Edet: Babu abin da zan ce sai dai yi wa Allah godiya da wannan baiwa, kuma da yadda matata ta haihu lafiya, jariranta ma lafiya. Fatata yadda Allah Ya ba mu su Ya hore  mana yadda za mu dauki dawainiyarsu. Wadanda ba su samu ba kuma Ya ba su.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited