Akwai alfanu a cikin dokar - Limamin Soja
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Akwai alfanu a cikin dokar - Limamin Soja

Limamin SojaBabban Limamin Soja na Birged na 13 da ke Kalaba, Manjo Kabiru Yakubu Sa’ad, kuma shugaban Qungiyar Limamai da Malamai ta Jihar Kuros Riba, ya ce akwai alfanu a dokar da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ke shirin kafawa don hana talaka marar qarfi qara aure da hana yawan saki:

 

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II ya kawo shawarar a kafa dokar taqaita qara aure ga talaka da kuma hana yawan sakin aure, me za ka ce kan haka?


Musulunci bai bar mu haka ba, ba tare da ya yi mana bayani kan kusan komai ba. Mai martaba Sarkin Kano da ya kawo wannan shawara yake qoqarin xabbaka wannan doka yana son ya dawo da mutane cikin hankalinsu cewa akwai wanda mabuqaci ne akwai wanda ba ya da buqatar aure akwai wanda yake auren farilla ne gare shi wani mustahabi ne. Gaskiya ce yanzu yadda ake, yanayin aure abubuwa ne sun wuce gona da iri waxansu ma auren suna yi domin wasa. Wato wane yana da mata 2 ko 3 ni ma bari in qara. Za ka ga waxansu ba su da wata qwaqqwarar sana’a, a wata ba zai iya kawo Naira dubu biyar gidansa ba, amma ya tara iyali, ya tara mata babu adalci kullum faxa shi ya sa za ka ga an haifi yara an kasa tarbiyantar da su ga barace-barace, abubuwa na varna daban-daban. Mutum ya tara iyali ya kasa ciyar da su ya kasa tarbiyantar da su me kake tsammani? Sai varna da sace-safe da sauransu.


Kana ganin kafa dokar zai iya magance waxancan matsaloli?

Insha Allahu zai magance tunda an saki abin ne ba wata doka da idan aka tabbatar qarfinka bai kai ba ka yi, za a kai ka kotu a hukunta ka. Ai ka ga a cikin maganarsa ya ce waxanda ba su da iko ko halin da za su auri fiye da mace xaya. Amma idan kana da hali bai ce ya hana maka aure ba. Yin dokar gaskiya za ta rage abubuwa da dama qwarai da gaske .

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited