Dokar taqaita qara aure Masarautar Kano ta jawo taqaddama
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Dokar taqaita qara aure Masarautar Kano ta jawo taqaddama

Sheikh Aminu DaurawaDokar da Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ke shirin kafawa don taqaita aure ga talakawa da kuma magance yawan saki tana ci gaba da jawo taqaddama, inda Malaman addinin Musulunci, suka ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan matakin kafa dokar.

A tsakiyar watan jiya ne Sarki Muhammadu Sanusi ya bayyana shirin vullo da wannan doka da kuma qarin wasu matakai da ya ce za su magance ximbin matsalolin da suka dabaibaye harkar aure a jihar.
Malami na farko da ya fara sukar dokar shi ne Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, wanda ya ce ilimantarwa da wayar da kai ne kawai za su magance matsalolin aure, ba wata doka ba.
Sheikh Aminu Daurawa ya shaida wa BBC cewa, “Dama maganar auren fiye da mace xaya Allah Ya riga ya sa sharaxi a Alqur’ani sai in mutum zai iya adaci, kuma malamai suna qarawa da wasu sharuxxa 13 da dole mutumin da ke son qara aure zai cika su. Ke nan kamata ya yi a ce waxannan sharuxxan ne za a wayar wa da mutane kai a kansu. A sanar da mai son qara auren da wacce za a aura da dalilin qara auren don su san sharuxxan.”
Sheikh Daurawa ya ce matsalolin aure sun ta’allaqa ne a kan rashin ilimin su ma’auratan a kan ma’anar auren kansa. Ya ce, “Akwai wanda aure ya wajaba a kansu da waxanda ya haramta a gare su, akwai waxanda an so su yi auren, akwai kuma wanda ba a so su yi auren, don haka ya zama wajibi a wayar wa kowa kai don sanin matakin da ya faxa kafin a kai ga yin doka.”
Malamin ya yi kira ga masarautar Kano da gwamnatin jihar cewa, kamata ya yi a saka batun aure a cikin tsarin karatun makarantu tun daga sakandare. “Hakan zai sa kafin mutum ya kai minzalin auren ya san dalilan da suka sa ake yi da kuma sharuxxansa, amma idan aka yi doka ba tare da an ilimantar da mutum sharaxin dokar ba, to dokar ma ba za ta yi aiki ba,” inji Sheikh Daurawa.
Shehin Malamin shi ma ya koka kan yadda ake yawan sakin aure da yadda zawarawa ke qaruwa, ya ce wayar da kai ne zai rage faruwar haka. “Abin takaicin shi ne yadda za ka ga waxansu maza suna da halin riqe mata huxu, amma sai matarsu ta cikin gida ta ja daga ta hana su yin hakan, to su ma ya kamata a yi doka da za ta ba su qarfin gwiwa su riqa qara aure,” inji Daurawa.
Sheikh Daurawa ya ce babban qalubalen da ke tattare da dokar shi ne, ta yadda za a gane wanda ke son qara auren yana da hali ko ba ya da hali. Ya ce ya ga talakan da ya sayar da rigarsa don ciyar da matarsa. Na biyu kuma zai yi wahala a yi binciken har a gano gaskiyar lamarin, “Mai kuxi ya sha yin aure fiye da xaya ya samu karayar arziki daga baya, haka talaka yana iya aure da yawa daga baya ya yi arziki, to ta yaya za a aiwatar da dokar a irin wannan yanayi,” inji shi.
A ganinsa ilimantar da mutane sosai a kan dokokin shari’a da sharuxxan Allah a kan batun aure ne kawai hanyar da za a bi don magance matsalolin da suka dabaibaye jama’a.
Ya ce a wasu lokutan ma halin riqe aure ba a arziki ko wadata yake ba, ya danganta da irin zuciyar mutum ne ta yin abubuwa.
Wannan yunquri ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a tsakanin al’ummar Najeriya ba Jihar Kano kawai ba, inda mutane da dama suke ta tofa albarkancin bakinsu a shafukan sada zumunta da muhawara duk da cewa dokar ta sarki Sunusi ba ta riga ta fara aiki ba, kuma sai an miqa ta ga kwamitin malamai sun duba dacewarta ko akasin hakan kafin a miqa ta ga majalisar dokokin jihar don tabbatar da ita.

Ya kamata Sarkin Kano ya sake nazari kan dokar - Sheikh Jingir

Daga Hussaini Isah, Jos

Shugaban Majalisar Malamai ta qungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis ta Qasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II ya sake nazari kan dokar taqaita qara aure da yake qoqarin kafawa a masarautar Kano.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Jos, inda ya ce wannan magana abin baqin ciki ne musamman idan aka yi la’akari da girma da darajar masarautar Kano, wadda daga masarautar Sarkin Musulmi sai ita.
Sheikh Jingir ya ce Mai martaba ya koma ya sake nazari kan wannan al’amari kuma ya tambayi malaman masarautar Kano. Kada ya xauko malaman da suka samu tasirin Turawa ya ce su ne malamansa.
Ya ce duk Musulmi sun yi imanin cewa Allah ba Ya kure. Kuma Alqur’ani a cikin Suratu Nasa’i Allah Ya bai wa Musulmi dama su auri mata biyu ko su auri mata uku ko su auri mata huxu, idan kuma suka ji tsoron ba za su yi adalci ba, su auri mace xaya. Ya ce ka ga a nan babu inda aka yi maganar kuxi ko ciyarwa sai tsoron rashin adalci.
“Ya kamata fadar Sarkin Kano ta riqa lura da duk abin da za ta faxa domin wannan fada babban wuri ne na jagoranci. Don haka bai kamata ta riqa yawan maganganu ba. Yawaici a baya fadar Sarkin Musulmi da fadar Sarkin Kano ba su cika yawan magana ba, domin maganarsu tana da qarfi,” inji shi.
Sheikh Jingir ya ce idan aka dubi kashe-kashen maza da ’yan Boko Haram suka yi hatta a Kano da irin dubban matan da mazansu suka mutu, waxansu ma suna da mata huxu waxansu uku, suna nan babu maza, kawo wannan doka bai dace ba.
Ya yi kira ga al’ummar Musulmi su mayar da hankali kan yin aure, domin Allah Ya nuna cewa duk mai son kansa da alheri ya yi aure.

Idan aka kafa dokar taqaita aure a kafa dokar tilasta masu kuxi su qara aure -Imam Usama
Daga Hussaini Isah, Jos

Limamin Masallacin Unguwar ’Yan Majalisar Tarayya da ke Shiyyar B. a Apo, Babban
Birnin Tarayya, Abuja, Imam Ibrahim Awwal [Usama] ya yi kira ga masarautar Kano kan ta kafa dokar tilasta wa masu kuxi su qara aure a masarautar a qoqarin da take yi, na yin dokar taqaita aure ga talakawa.
Imam Ibrahim Awwal ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya, inda ya ce wannan qoqari da ake yi na kafa wannan doka waxansu suna ganin ya dace, waxansu kuma suna ganin bai dace ba. Ya ce “Amma ni a ganina ya kamata idan aka kafa dokar ta taqaita aure ga talakawa. To a kafa wadda za ta tilasta wa masu dukiya da ke masarautar Kano su qara aure. Idan aka yi haka za a rage matan da ba su da aure.”
Ya ce idan masu kuxi suka ce ba za su iya qara aure ba, to sai a sanya doka duk mai kuxin da ba zai iya qara aure ba. Idan ya gina wani gidan saukar baqi a wajen gari, wanda ake kawo ’yan mata daga manyan makarantu, gwamnati ta qwace wannan gida. “Saboda mafi yawa za ka ga yanzu manyan mutane idan mace ta zowurinsu neman wata buqata, sai su yaudare ta, su yi lalata da ita. Shi ya sa ba son qara aure saboda suna da waxansu matan a waje. Don haka gara talakan da zai yi qoqari koda daxi ko babu daxi ya qara aure. Ya fi wanda zai riqa yin irin waxannan munanan abubuwa.”
Imam Usama ya ce mai yiwuwa ne a maqwabtan Mai martaba Sarkin Kano a samu mutum xaya wanda zai iya ciyar da mutum 100 a kowace rana. Amma ba za a iya samun qila ya xauki nauyin mutum biyu a cikin gidansa ba. “Ya kamata shugabannin Najeriya su gane cewa kan talakan Najeriya ya fara wayewa akwai haqqoqin talakawa da dama waxanda ya kamata sarakuna su tsaya wajen ganin an qwato musu.”

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited