Babu savani a tsakanin Buhari da Osinbajo – Gwamnati
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Babu savani a tsakanin Buhari da Osinbajo – Gwamnati

Shugaban Qasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi OsinbajoFadar Shugaban Qasa ta ce babu wani savani a tsakanin Shugaban Qasa Muhammadu Buhari da Muqaddashinsa, Farfesa Yemi Osinbajo.

’Yan gaza-gani sun riqa yin maganganu suna nuna matakan da Farfesa Osinbajo yake xauka na gaggawa wurin tunkarar matsalolin da qasar nan ke fuskanta bayan tafiyar Shugaba Buhari hutu, suna nuna cewa wai ya fi Shugaba Buhari kazar-kazar. Kuma hakan ya sa suke ganin ya yi wa mai gidan nasa zarra a wata xayan da ya shafe yana lura da al’amuran qasar nan.
Sai dai fadar Shugaban Qasar ta mayar da martani cewa duk wani yunquri na a nuna cewa Osinbajo ya fi Buhari “qoqari ne na kawo ruxani kawai.”
Mai Bai wa Shugaban Qasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Sanata Babafemi Ojudu, ya ce ’yan adawa ne kawai suke son kawo ruxu ta hanyar cusa wa mutanen tunanin akwai rabuwar kai a tsakanin Shugaban Qasa da Mataimakinsa.

Sanata Ojudu ya ce, “Kusan a kullum sai (Osinbajo) ya tuntuvi Shugaba Buhari saboda akwai abubuwan da suke buqatar hakan. Ina nufin yana neman shawararsa wajen zartar da manyan hukunce-hukunce.”

Ya ce ayyukan da Farfesa Osinbajo yake yi yana yi ne domin ya burge Shugaba Buhari ya kuma nuna masa cewa zai iya gudanar da al’amuran mulki ko da Shugaban ba ya nan.
Tun ranar 19 ga Janairu Farfesa Osinbajo yake jagorancin Najeriya a matsayin muqaddashi sakamakon hutun dda Shugaba Buhari ya tafi yi a Ingila kuma domin likitoci su duba lafiyarsa.
Muqaddashin Shugaban Qasar wanda shi ne Shugaban Kwamitin Tattalin Arziki na Gwamnatin ya zartar da wasu ayyuka da ake ganin sun kawo sauyi musamman a fannin tattalin arziki, inda a makon jiya ya umarci Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zuba miliyoyin dalolin Amurka a kasuwar musayar kuxaxe, lamarin da ya sanya darajar Naira ta xan farfaxo.
A baya gwamnati ta hana yin haka da manufar qarfafa darajar Naira tare da daqile shigo da kayayyaki daga qasashen waje waxanda ake ganin za a iya yinsu a cikin gida.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited