Osinbajo ya rantsar da Onnoghen a matsayin Babban Jojin Najeriya
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Osinbajo ya rantsar da Onnoghen a matsayin Babban Jojin Najeriya

Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya rantsar da Mai shari’a Walter Onnoghen a matsayin Babban Jojin Najeriya bayan da Majalisar Dattawa ta amince da nadinsa.
A safiyar ranar Talatar da ta gabata ce aka rantsar da Mista Onnoghen a dakin taro na fadar Shugaban kasa.
A watan Nuwamba ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mista Onnoghen daga Jihar Kuros Riba a matsayin Mukaddashin Babban Jojin bayan da Mai shari’a Mahmud Muhammad ya yi ritaya.
Mista Osinbajo ya ce Shugaba Buhari ya umarce shi ya shaida wa sabon Mai shari’ar cewa ya samu aikin ne a lokacin da “jama’a ke kara nuna rashin amincewa da bangarorin gwamnati da dama.”
Amma ya ce yana da kwarin gwiwa cewa Mista Onnoghen zai taimaka wurin farfado da yardar da jama’a ke da ita a kan gwamnati.
Nadin ya zo ne a daidai lokacin da bangaren shari’a ke fama da manyan matsaloli, inda manyan alkalai da ma’aikatan kotu da dama ke fuskantar shari’a kan zargin cin hanci da rashawa.
Da yake magana a wurin rantsarwar Mai shari’a Onnoghen ya ce zai yi aiki domin kare tsarin mulkin kasar nan.  Kuma ya ce zai nemi tallafin dukan ’yan kasar domin cimma burinsa na kawo sauyi a fagen shari’a.
A lokacin da ya bayyana a gaban Majalisar Dattawa lokacin tantance shi, Mai shari’a Onnoghen ya ce zai yi kokarin ganin ya kara karfafa sashin shari’a a matsayin bangare mai cin gashin kansa.
Da sanatoci suka tambaye shi kan yadda zai tabbatar da adalci ga talakawan Najeriya da yadda zai tabbatar da yin shari’ar wadanda aka kama da laifin cin hanci ba tare da an bata lokaci ba, Mai shari’a
Onnoghen ya yarda da batun da sanatocin na cewa akwai cin hanci a bangaren shari’a, kuma ya ce hakan zai kasance daya daga cikin matsalolin da zai magance.
Sabon Babban Jojin, ya yi bayani kan yadda zai karfafa bangaren shari’a a matsayinsa na wuri na karshe da ’yan Najeriya za su yi fatan samun adalci.
Ya ce ba lallai ba ne sai kowane dan Najeriya ya ga alkali ba kafin gaskiya ta yi halinta, inda ya shaida wa sanatocin cewa: “Za mu karfafa ’yancin da muke da shi. Ba zan yi sake da wannan ba.”

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited