Ya kamata Musulmi su rika magana da murya daya a Najeriya - Sheikh Bala Lau
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Ya kamata Musulmi su rika magana da murya daya a Najeriya - Sheikh Bala Lau

Sheikh Abdullahi Bala Lau shi ne Shugaban kungiyar Izala ta kasa a zantawarsa da manema labarai a Kaduna ciki har da Aminiya ya bayyana ra’ayinsa kan kokari da ake yi na hada kan Musulmi a kasar nan, kuma ya yi bayani kan dokar aure da ake shirin kafawa a Jihar Kano da sauransu:

 

Me Malam yake ganin zai taimaka wajen hadin kan Musulmi a Najeriya?
Babu shakka a addinin Musulunci hadin kai abu ne mai muhimmanci shi ne ma jagora, domin Allah Ya aiko Annabi Muhammad (SAW) ne don hada kan al’umma. Duk da haka Alkur’ani ya nuna mana cewa al’umma ba za su gushe ba suna cikin sabani sai wadanda Allah Ya yi wa rahama. Manzon Allah (SAW) ya ce addinin nan namu zai karkasu 73 kuma kowane daya daga ciki akwai shaidani da yake kiran al’umma su bi shi a kan shaidancin da yake kai, daya ce kawai za ta kama hanyar kai al’umma zuwa gidan Aljanna. Sai ya karanta ayar Alkur’ani da ke nuna cewa hanya daya tak fitacciya wanda duk ya bi ta, ya kama hanyar zuwa gidan Aljanna. Annabi (SAW) ya yi wannan magana ne sai sahabbai suka ce a kan wace hanya ka bar mu sai ya ce na bar ku a kan wannan. Ku rike Littafin Allah ku rike Sunnata.
To, idan Manzon Allah (SAW) ya bar mu a kan Alkur’ani da Sunnarsa, ashe babu abin da zai hana hadin kan al’umma. Duk yadda mutane ke sabani Allah Ya ba da yadda za a warware sabanin. Alkur’ani ya gwada mana cewa babu makawa sai an samu sabanin, kuma ya gwada cewa idan an samu sabanin a koma ga Littafin Allah a koma ga Sunnar Annabi (SAW) su za su warware wannan sabani namu. In na ce ga yadda ya kamata a yi kai ma ka ce ga yadda ya kamata a yi da ni da kai abin da zai warware mana takaddamar shi ne Littafin Allah, in ba mu samu ba sai mu dubi Sunnar Manzon Allah (SAW), saboda hadin kan Musulmi wajibi ne.  
Akwai haduwa irin ta Yahudu da Nasara, Allah ya ce kada mu yi irinsu domin za ka gan su kamar kansu a hade amma zukatansu daban-daban, mu ya kamata zukatanmu su hadu, kawunanmu su hadu. Kuma babu inda Allah Ya ce mu yi koyi da su sai wuri daya tak. Shi ne wurin hadin kai. “Kafiran nan masoya juna ne, suna kaunar junansu suna kuma rufa wa junansu asiri in ba ku yi irin wannan ba, za a samu barna mai yawa a bayan kasa.” Shi ya sa aka samu Rabidah, kungiyar Musulmi a duniya mai hada kan Musulmi baki daya.
Wadanda ba a tafiya tare da su su ne masu akidar suka da zagi ga sahabban Annabi (SAW) da iyalansa. Babu yadda za a yi masoyin Annabi (SAW) ya zagi matansa ko ya zagi sahabbansa domin ta hanyarsu aka samo addini.
Amma sauran mutane za ka ga daga wanda son Annabi (SAW) ne ya sa ya wuce gona da iri, ya yi ba yadda aka ce ba, ko ya dauki wani jikan Annabi (SAW) ya koma yana son jikan fiye da yadda Annabi (SAW) ya ce, ko suna bidi’o’i iri-iri, irin wadannan dole a yi hakuri da su a zauna inuwa guda domin a gyara.
Mu ma dole mu samu irin Rabida a Najeriya, muna da wata kungiya a Adamawa da Taraba da ake kira Majalisar Musulmi a ciki akwai kungiyoyin addini har 25. Shugabanta daya ne a ciki za ka samu dan darika da dan Izala da sauransu. Hikimar ita ce duk abin da ya taso wa Musulmi a jihar su hadu su magance shi. A Najeriya akwai abin da zai iya tasowa da dan Izala kadai ba zai iya warware shi kadai ba, akwai abin da zai iya tasowa dan darika ba zai iya warwarewa shi kadai ba.
To, ya kamata a ce mun samu wani wuri da za mu zauna domin warware matsalolinmu. Abin da ya shafe mu mu hadu mu yi maganinsa, matsalolinmu na cikin gida mu yi hakuri da su ta yadda za mu warware su cikin hanyoyi na ilimi da karantarwa. Kada in soke ka, kada ka soke ni, amma ka yi wa’azi ka nuna abin da nake yi ya saba wa Alkur’ani da Sunna ka kira ni da hikima har in gane, ni ma idan na ga kana kan kuskure in yi maka wa’azi da hikima yadda za ka gano kana kan kuskure.
Idan ya kama mu zauna a kan teburi in kawo hujja kai ma ka kawo naka har mu fahimci juna. Bai kamata a rika zage-zage da bata juna har a kai ga kashe-kashe da zubar da jini ba.
Babban jagoran da zai taimaka wurin yin haka shi ne Sarkin Musulmi. Sarkin Musulmi wanda duk Musulmi Najeriya ka martabawa da mutunta shi.  Muna ba shi shawara lallai a samar da irin wannan majalisa. Mun sha tattaunawa da shi, mutum ne na kwarai mai kokarin daukar shawara mai tuntubar dukan kungiyoyin Musulmi.
Shi ya sa ma tare da shi muka yi Gidauniyar Sarkin Musulmi, cikin wannan gidauniya akwai kungiyoyin Musulmi daban-daban, ina ciki Sheikh dahiru Bauchi na ciki, Sheikh karibullahi na ciki, Sheikh Ibrahim Saleh na ciki. Ka ga wadannan manya ne a kasa baki daya na darikoki daban-daban duk suna cikin wannan gidauniya kuma ana ci gaba da aiki.
Kuma lokacin da yake Amirul Hajji shi ne ya tsara yadda za ka ga a tantinmu ga wurin kwanciyata ga na Sheikh dahiru Bauchi ga wurin kwanciyar Sheikh karibullahi ga Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun duk an hadu wuri guda. Idan aka ci gaba da wannan al’ummar Musulmi za su samu murya guda su yi magana a madadin al’umma. Musulunci na bukatar shugabanci yana bukatar hadin kai.
Mai martaba Sarkin Kano yana yunkurin kawo dokar aure a jihar yaya Malam ke kallon wannan doka a addinance?
Ba doka ce ta Sarkin Kano ba, ya kamata a yi masa kyakkyawar fahimta, idan kuwa shi ne ya fito ya yi bayani cewa ya yi doka to, bai isa ya yi doka a karan kansa ba. Doka ce ta shari’ar Musulunci kamar lokacin kafa shari’a ce a ce wai za a kafa shari’a a jiha kaza, kuskure ne domin dama shari’ar tana nan. Mutane ne ke kaucewa. Me Allah Ya ce, me Manzon Allah (SAW) ya ce dangane da abin da ya shafi aure?
Allah Ya ce ku auri daga abin da ya yi muku dadi na mata biyu ko uku ko hudu amma in ba za ku iya yin adalci ba ko ba za ku iya rike su ba, ku auri daya. Ke nan ba Sarkin Kano ne ya fadi wannan ba. Allah ne Ya ce idan kana da halin rike mace fiye da daya to ka aura, amma ba wai ciyarwa da shayarwa ba ne, ya zama kana da karfin saduwa da su da biya musu bukata. Idan har zak a ajiye biyu ya zama abin da za ka yi wa wannan, shi za ka yi wa waccan. In ba ka iyawa ko kana da kudi da hali amma ba za ka iya yin adalci ba, za ka mayar da daya ta zamo kamar mai takaba ba ta da miji a gida a wulakanta ta har a gano cewa ga abin da kake yi to kada ka yi.
Duk mutumin yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ga daya, abin da Annabi (SAW) ya ce, zai tashi gaban Allah gefen jikinsa daya a shanye. To, irin wannan ya kamata Mai martaba Sarki ya fito a yi ta yi wa mutane nasiha cewa ga dokar Allah ga abin da Allah Ya ce domin ana wulakanta aure ba a rikewa yadda ya kamata. Ka ga idan mutum ba ya da hali ba zai iya rike su ko da kyar zai iya rike kansa ko mace daya, in har ya je ya karo wannan akwai cutarwa. Ire-iren wadannan ne ya kamata a duba kuma shi kansa Mai martaban jiya ko shekaranjiya mun hadu da shi ya ce muna gayyatarku zuwa Jihar Kano mun yi kundin abin da muka iya tsarawa kuma za mu mika shi ga malamai a yi nazarinsa wane wuri ne ya saba, wane wuri ne daidai, ina za a kara ina za a cire, bayan an samu fahimta da haduwar malamai daga nan sai a mika wa Majalisar Dokoki ta tabbatar da haka.
Saboda haka ’yan jarida da sauran jama’a a yi masa kyakkyawar fahimta ba cewa ya yi a hana talaka aure ko sai mai hali zai yi ba. A’a shari’a ta ya ce ba ka iya yi sai kana da hali Allah ma Ya ce wadanda ba su da halin yin aure su kame har sai Allah Ya ba su wadata. Annabi (SAW) ya ce wanda ba ya da hali ya rika yin azumi, lokacin da yake azumin nan zai karya masa sha’awa.
Idan na fahimce ka kana goyon bayan wannan doka ta Sarkin Kano ke nan?
Kada ka je ka ce Sarkin Kano muna bayan dokarsa, muna bayan dokar Allah ce, ma’ana dokokin da Allah Ya tsara a Alkur’ani da Sunnar Annabi (SAW) su ne shari’a. Ba wani abu sabo, Sarki bai isa ya kawo sabuwar doka ba idan ya kawo ma fatali za mu yi da ita ba za mu saurare shi ba. Duk abin da ya kawo idan muka auna a mizanin shari’a ya zama ya saba ba za mu karbe shi ba. Shi ma ina fata idan ya ga abin da ya saba ba zai yarda ba.
Yaya kuke kallon batun rashin lafiyar Shugaban kasa da damuwa da al’umma ke nunawa?
Shugaban kasa dan Adam ne kamar kowa, dan Adam zai iya rashin lafiya zai iya rasuwa lokacin da Allah Ya dibar masa. Kuma zai kasance cikin farin ciki zai iya haduwa da bakin ciki. Wa yake mallakar wannan iko? Allah ne! Saboda haka ba abin mamaki ba ne idan Allah Ya jarrabe shi da rashin lafiya. Bai kamata wadansu su yi murna da rashin lafiyar ba, ya kamata su gane cewa shi Shugaba ne na al’umma baki daya. In rashin lafiya ta same shi kasar na iya shiga wani hali, don haka ya kamata a yi masa addu’a ce Allah Ya ba shi lafiya. Domin haka mu yadda muke kallon wannan rashin lafiya abu ne da Allah Ya kawo shi Ya jarrabe shi a lokacin da Allah Ya ga dama, sannan ba abin da zai warware wannan sai addu’a.
Don haka muna kira ga al’ummar Musulmin kasar nan mu ci gaba da yi wa Shugaban kasa addu’a, Allah Ya ba shi lafiya kuma Ya dawo da shi gida lafiya. A cikin magabata manyan shugabannin Musulunci akwai Imam Ahmad Bn Hambal kowannensu na cewa da Allah zai karbi addu’ata ina da tabbacin a addu’ata karbabbiya ce, idan da dukan addu’o’in da nake yi daya Allah zai karba da ba zan yi wa kaina addu’ar ba sai na yi wa shugabana. Addu’ar nan Allah da Ka karba nawa Allah na sanya shi ga shugabana na kwarai ka sa ya zama mutumin kirki ka ba shi lafiya ka yi masa jagora. Saboda in shi ya zama na kwarai na kirki ni ma ka sa in sai ya samu lafiya. Lafiyarsa da zaman lafiyarsa zai shafe ni ya kuma shafi iyalina da kasa baki daya. Saboda haka idan shugaba ya zama na kwarai da bayin Allah da kasar za ta zauna lafiya. Ina fata al’umma za mu dage da addu’o’i ga Shugaban kasa Allah Ya ba shi lafiya.
Akwai wadanda ke ganin taruwar da ake yi don yin addu’ar ta saba wa karantarwar Annabi (SAW).Yaya sigar yadda ya kamata addu’ar ta kasance?
Duk inda kake kana iya yin addu’a ba sai an tara jama’a ba. Sai dai duk lokacin da jama’a suka taru domin wata bukata ta karantarwa kamar haduwa a masallaci kamar haduwa a makaranta wannan wuri ne da Manzon Allah (SAW) ya ce idan bayin Allah suka hadu a irin wadannan wurare don ambaton Allah, Mala’iku suna kewaye wurin kuma rahama na saukowa kuma idan sun yi addu’a Allah Yana karba. Lokacin da mutum ya karanta Alkurani Mai girma yana shi kadai ko yana cikin irin wannan harka to, lokacin nan da ake saukar nan Allah Yana karbar addu’a. Saboda haka akwai ire-iren wadannan lokuta wato zababbun lokuta da Sunnar Annabi (SAW) ta karantar cewa in an yi addu’a ana dacewa. Sau da yawa za ka ji mutum na cewa ya yi addu’a amma ba ta amsu ba, wannan kuskure ne. Ku roki Allah alhalin kuna sakankancewa cewa Allah zai amsa muku.
Malamai sun ce akwai lokuta zababu da in ka yi addu’a Allah zai amsa misali yayin da mutum yake tafiya idan ya yi addu’a Allah Yana amsa Hadisi ya inganta. Wanda yake azumi yayin bude baki idan ya yi addu’a Allah Yana karba. Ya kamata ke nan a ce duk mutanen da ke azumi yayin bude baki a umarce su da su yi wa Shugaban kasa addu’a Allah Ya ba shi lafiya Allah kuma Ya zaunar da mu lafiya. Haka matafiya, haka idan an yi kiran Sallah Annabi (SAW) ya ce ku yi koyi da mai kiran Sallah a lokacin da ya idar ku yi wa Annabi (SAW) salati ku kuma roki Allah domin duk abin da kuka roka a tsakanin kiran Sallah zuwa Ikama Allah Yana karba.
Idan ka sa goshinka a kasa lokacin sujuda za a karbi addu’arka domin babu lokacin da bawa ya fi kusanci da Allah kamar lokacin da yake cikin sujuda da sauransu.
Tsakaninmu da shugabanmu ba sai wani ya ce ku zo ku yi ba. Umurni ne Allah Ya ce mu yi masa addu’a yi masa addu’ar nan ibada ce saboda haka ba mu bukatar sisin kwabo, muna yi wa kanmu ne domin duk dan Najeriya kuma Musulmi ya kamata ya gode wa Allah kuma ya gane cewa Allah Yana karbar addu’a. Shekara biyu kafin zuwar wannan gwamnati masallatanmu idan mun shiga a tsorace muke ko bam zai tashi.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited