Abin da ya sa na gina masallaci – Obasanjo
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Abin da ya sa na gina masallaci – Obasanjo

A ranar Asabar da ta gabata ce tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya kaddamar da Masallacin Juma’a da Tsangayar Koyar da Ilimin Addinin Musulunci da Harshen Larabci a harabar dakin karatu na duniya da ya gina a birnin Abeokuta na Jihar Ogun, Masallacin da Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya bude a madadin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar.
Lokacin da yake jawab, Cif Olusegun Obasanjo ya ce ya assassa ginin masallacin ne domin hidima ga al’ummar Musulmi su samu tagomashin addinin Musulunci. “Bayan da na kammala ginin katafaren zauren karatu na duniya tare da gidan adana kayan tarihi da sauran mahimman wurare na kuma gina coci, sai na yi la’akari da wannan yanki namu na da mabiya manyan addinai biyu wato addinin Kirista da na Musulunci, sai na ga wajibi ne a kaina in gina masallaci da cibiyar koyon addinin Musulunci domin na bai wa Musulmi gudunmawata su samu damar amfanuwa da wannan aikin. Na kuma gina tsangayar koyar da addinin Musulunci da harshen Larabci ne domin ’ya’yan Musulmin wannan yanki su samu ingantaccen ilimin addinin Musulunci. Hakazalika na lura cewa mafiya yawan littattafan Musulunci an rubuta su ne da harshen Larabci don haka muka debo masana harshen daga kasar Saudiyya kuma akwai kasashen Larabawa irin su Moroko da Masar da suka yi alkawarin ba mu karin malamai. Yin haka ba ya nufin a Najeriya ba mu da malaman da za su iya koyar da Larabci, sai dai ba za a hada wanda Larabcin yarensa na asali da wanda ya koya,” inji shi.
Cif Obasanjo ya kara da cewa “Bugu da kari mun gayyato manyan shaihunan malaman Larabci da addinin Musulunci daga jami’o’inmu na kasa domin su tallafa mana, fatanmu mu samar wa ’ya’yanmu ingantaccen ilimin addini, domin duk wanda ya fahimci addini ba za ka same shi yana aikata miyagun ayyuka ba.”
Tsohon Shugaban kasar ya yi kira ga al’ummar Musulmi su yi amfani da wannan dama wajen inganta imaninsu tare da neman ilimi, ya kuma gode wa mutanen da suka ba da gudunmawarsu har aka kai ga cimma nasarar kammaluwar ginin masallacin. Kuma ya ce nan gaba za a gina wa limamin da zai jagoranci Sallah gida a daura da masalacin, kuma ya ce za a ci gaba da neman taimako don a samu damar ci gaba da daukar dawainiyar masallacin.
A jawabin Alafin na Oyo, kuma Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jihar Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III ya bayyana gina masallaci da cibiyar addinin Musulunci da Cif Olusegun Obasanjo ya yi a matsayin dattaku da girmama kowane addini da aka san kabilar Yarbawa da shi.  Ya ce hakan ne ya sa ya ba za ka taba jin rikicin addini ya barke a yankunan Kudu maso Yamma ba, “Mu Musulminmu da Kiristocinmu kanmu a hade yake ba tare da nuna bambance-bambance ba, lokutan bukukuwanmu na Musulunci tare muke yi da Kiristoci, hakazalika in nasu bukukuwan sun zo sai su yi tare da mu. Wannan al’ada tamu da muka gada tun kaka da kakkaninmu ne ta sa Cif Obasanjo ya kaddamar da wannan gagarumin aiki, kuma ya zama wajibi mu yaba masa,” inji Alafin na Oyo.
A jawabin Sarkin Musulmi wanda Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya wakilta kuma ya gabatar cikin harshen Larabci tare da yin fassara da Ingilishi a wurin bude masallacin, ya tunatar da al’ummar Musulmi muhinmmancin gina masallaci tare da tsabtace shi da raya shi ta hanyar yin ibada da neman ilimi a cikinsa. Sarkin ya ce masallaci abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar Musulmi domin daki ne na ibada da koyon addini da rayuwa gaba daya. Ya ce farkon abin da Annabi (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi) ya fara yi da ya yi kaura daga Makka zuwa Madina shi ne gina masallaci inda ya shiga aka yi aikin ginin da kansa. Sarkin ya kuma karanto Hadisin da Abu Huraira ya rawaito inda Manzon Allah (SAW) ya ce “Duk wanda ya gina masallaci don Allah, to Allah zai gina masa gida a Aljanna.”
A karshe Sarkin Musulmin ya mika godiyarsa ga Cif Obasanjo a Madadin ilahirin Musulumin Najeriya kan wannan karimci da ya yi musu.
A zantawar da Aminiya ta yi da tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanatan Kano ta Tsakiya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce kimanin shekara 10 ke nan da aza harsashin ayyukan da Cif Obasanjo ya kaddamar. “Wannan abin farin ciki ne a gare mu domin  lokacin da nake Gwamna nan muka zo muka aza harsahshin gininsa muna daga bulo muna sanyawa muna ba da tamu gudunmawar. Kuma ga shi yau Allah cikin ikonSa Ya yi mana tsawon rai mun zo an bude masallacin da mu. Abin a yaba wa tsohon Shugaban kasa ne gannin yadda ya assassa wannan aikin a matsayinsa na Kirista amma ya hada kai da al’ummar Musulmi masu hali aka yi wannan gagarumin aiki, aka kammala masalacin aka yi masa ado aka sanya kayan alatu, ta yyada al’ummar Musulmi za su rika yin ibada a ciki. Wannan abin alfahari ne wannan abin ci gaba ne. ka ga wannan wani abu ne na daukar darasi domin da mutane za su rika yin irin haka da an samu sauki rigingimun addini da kabilanci da ake samu a wasu wurare,” inji Kwankwaso.
Ya kara da cewa: “Yadda mutumin da ba Musulmi ba ya ja ragamar wannan aiki abin alfahari ne, don haka muna taya shi murna, kuma abin da ya kamata mutane su sani shi ne wannan katafaren aikin da aka kadamar a yau na dakin karatu na duniya da ya kunshi abubuwa da dama na tarihi da ilimi da addini da siyasa wannan katafaren wuri ba abu ba ne da in babu Baba ’ya’yansa za su zo su dauka a matsayin gado. A’a an gina shi ne a matsayin gidauniya domin amfani jama’ar kasar nan da wadanda za su zo daga kasashen ketare.”
A zantawar da wakilinmu ya yi da Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa, Alhaji Ali Modu Sheriff ya bayyana tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin gwarzon Afirka in aka debe toshon Shugaban Afirka ta Kudu, marigayi Nelson Mandela. “Idan ka dauke Nelson Mandela a duk Afirka babu kamar Baba Obasanjo,” inji Modu Sheriff.
Sai dai a daidai lokacin da Cif Obasanjo ya jiyo zantawar da Ali Modu Sheriff yake yi da wakilin Aminiya, cikin barkwanci ya ce wa Shugaban jam’iyyar ta PDP, “To kai a wani matsayi kake a nan, ba mu gane maka ba ka yi mana bayani.” Cikin raha shi ma Ali Modu Sheriff yana kokarin ba shi amsa, amma sai ya ce tunda dama a tafe yake tare da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan.
A tattaunawarsa da Aminiya a wajen taron Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Abdulahi Bala Lau ya ce suna yi wa Cif Obasanjo fatan alheri da addu’ar samun shiriya lura da kyawawan ayyukan da ya gabatar. “Wannan kalubale ne ga sauran shugabanni da su yi koyi da irin wannan, ga shi yau Obasanjo Musulunci ya amfana da dukiyarsa, in fata sauran shugabanni za su yi koyi da shi su kuma duba irin abubuwan da bai yi ba su dora a kai,” inji shi.
Sakataren kungiyar ta kasa, Sheikh Kabiru Gombe kuwa ya danganta kyakyawan aikin na tsohom Shugaban kasar da dadaddiyar kyakkyawar alaka a tsakanin Musulmi da Kirista tun a zamanin Manzon Tsira. Ya ce abin sha’awa ne da zai kara dakon zumunci a tsakanin Musulmi da wanda ba Musulmi ba. “Idan ka kalli Yarbawa mutane ne masu kokari zakakurai, wajan hidima wa Musulunci, sai dai kawai suna bukatar a rika yi musu da’awa ta Sunnar Annabi (SAW),” inji shi.
Bayan jagorantar bude masallacin Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, ya jagoranci Sallar Azahar da La’asar raka’a bibbiyu wato kasaru, inda manyan malaman addinin Musulunci da manyan sarakuna ciki har da Mai martaba Sarkin Ilorin Alhaji Ibrahim Sulu Gambari da Alafin na Oyo Oba Lamidi Adeyemi III da gwamnonin Arewa da dama wadanda suka halarci bude masallacin da sauran jama’a suka yi Sallah tare da shi.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited