Rikicin Yarbawa da Hausawa: Yadda kilu ta jawo bau a Ile-Ife
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Rikicin Yarbawa da Hausawa: Yadda kilu ta jawo bau a Ile-Ife

Takaddama kan wurin zama a tsakanin wata Bayarbiya mai sayar da ruwan leda fiya wata da wani yaro Bahaushe da yake sayar da dafaffen abinci ta koma rikicin kabilanci a tsakanin Yarbawa da Hausawan garin Ile-Ife inda aka kashe mutane da dama kuma aka kone gidaje da motoci da kadarori masu dimbin yawa a shekaranjiya Laraba.
Duk da cewa har zuwa hada wannan rahoto ba a tantance yawan rayukan da aka rasa ba, amma bayanai sun nuna cewa an kone gidaje fiye 30, wadanda galibi ya fi shafar Hausawa mazauna garin.
Wasu majiyoyi sun ce, rikicin ya samo asali ne tun a yammacin ranar Litinin kafin ya kazance a ranar Laraba da safe a Unguwar Sabo Ile-Ife, mazaunin Hausawan.
daya daga cikin shugabannin Hausawan Ile-Ife, Alhaji Abdul’azeez Muhammed Sardaunan Ile-Ife , ya shaida wa Aminiya ta tarho cewa, “A ranar Litinin an samu rashin jituwa a tsakanin wata Bayarabiya (mai suna Kubura) da wani yaro Bahaushe da ya ajiye dafaffen abinci a kusa da shagonta, inda ta ki amincewa da zamansa a wurin. Hakan ne ya haifar da gardama a tsakaninsu inda matar ta mari matshin shi kuma ya rama. Wannan ne ya fusata matar wadda matar wani jigo ne a kungiyar Direbobi ta NURTW, inda ta kira ’yan daba suka fara tayar da zaune-tsaye a ranar. Mun hanzarta sanar da ’yan sanda inda suka kwantar da lamarin.”
Ya ce ’yan daban dauke da kwalabe sun sake dawowa da yamma a ranar Talata amma jami’an tsaro suka kore su. “Abin mamaki da sanyin safiyar shekaranjiya Laraba sai muka wayi gari gungun mutane dauke da adduna da bindigogi sun yi mana kawanya suna harbin kan-mai-uwa-da-wabi. An kashe mana mutane masu yawa an kone motocinmu an shiga gidajenmu an yi mana barna,” inji shi.
Alhaji Abdul’azeez ya ce tunda sanyin safiyar ranar muka sanar da ofishin ’yan sandan yankin amma har zuwa karfe 2:00 na rana da yake magana da Aminiya, babu jami’in tsaron da ya kai musu dauki, sai ci gaba da kashe musu mutane ake yi ana kona gidaje da kadarorinsu.
Bayanai daga yankin sun tabbatar da cewa har zuwa lokacin ana harbe-harbe da bindigogi a Unguwar Sabo, Ile-Ife.
Da yawa daga cikin Hausawan da ke zaune a garin Ile-Ife sun yi wa Aminiya bayani ta tarho suna cewa, an kashe fiye da Hausawa 20. Wadansu daga cikinsu an yi musu yankan rago wadansu kuma an sanya musu tayoyin mota an barbada musu fetur a cinna musu wuta.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce: “Shi kansa Kwamishinan ’Yan sandan Jihar ya gane wa idonsa gawarwaki a kan hanyoyi bayan wadanda suke cikin daji da ba mu ji duriyarsu ba har yanzu. An kone mana gidaje fiye da 15 da motoci masu yawa kurmus tare da shiga cikin gidaje da shagunan kasuwanci ana sace mana gwala-gwalai da dimbin kudaden da muke canji da su. Wata matsala da muke ciki a yanzu ita ce mun zama ’yan gudun hijira muna zaune a waje daya ba shiga ba fita babu abinci tare da mu. Don Allah ku taimaka mana da abinci da ruwan sha,” inji shi.
Tuni Gwamnatin Jihar Osun ta sanya dokar takaita fita daga karfe 6:00 na yamma zuwa 7:00 na safe a garin inda aka tura sojoji don tabbatar da tsaro. Sanarwar kafa dokar ta fito ne daga ofishin Gwamnan Jihar Mista Rauf Aregbesola a daidai lokacin da Mukaddashin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Osun Muhammad Abubakar Koji ya jagoranci tawagar jami’an tsaro zuwa inda aka yi rikicin domin gane wa idonsu tare da kwantar da hankali.
Gwamnan Jihar Rauf Aregbesola ya yi Allah wadai da tarzomar, inda ya ce gwamnati ba za ta lamunci karya doka da oda ba daga kowane bangaren jama’a a jihar.
Dokar takaita fitar ta kwana uku 3 da ta fara aiki a yammacin shekaranjiya Laraba, sanarwar ta ce, kafa dokar ya zama dole.
Kuma sojoji da ’yan sanda suna isa sassan Unguwar Sabo domin shawo kan lamarin.
Da yake yi wa Aminiya bayani ta tarho Mukaddashin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Osun, Muhammad Abubakar Koji, ya ce, “Gaskiya ce an yi kone-kone da kashe-kashen rayuka a Ile-Ife amma yanzu komai ya lafa. A yanzu ba za mu iya gaya maka yawan mutanen da suka mutu ba sai daga baya za mu sanar da ku komai idan muka kammala bincike.”
Mukaddashin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Osun, Malam Muhammed Abubakar Koji ya fadi ta bakin Kakakin Rundunar, Misis Folasade Odoro cewa an dauki matakan da suka wajaba don kwantar da kurar tare da tura karin ’yan sanda zuwa Ile-Ife.
Lokacin da Aminiya ta tuntubi Sarkin Hausawan Ile-Ife Alhaji Mahmuda Lawal Madagali kan halin da ake ciki a yammacin shekaranjiya Laraba, ya ce yanzu hankali ya kwanta kuma an samu zaman lafiya bayan shiga tsakanin da jami’an tsaro suka yi.
Sarkin Hausawan ya ƙara da cewa rikicin kabilancin ya samo asali ne a ranar a Litinin da ta gabata da dare sannan ya yi kamari a shekaranjiya Laraba. “Akwai wani yaro Bahaushe da yake sayar da abinci a bakin tashar ’yan Yuniyan a gaban shagon wata mace sai ta yi korafin yana zubar mata da shara, nan rikici ya kaure a tsakaninsu, ta mare shi ya rama, ’yan Yuniyon din suka yi wa yaron dan karen duka daga baya aka shiga tsakani aka sasanta su,” inji Sarkin Hausawan.
Ya kara da cewa: “Dama akwai wani tsohon shugaban wurin ana ce masa Jagaba don ni ma na ba shi sarauta a masarautata da wani basarake da ke da kujera a fadar Ooni na Ife sai suka sayo bulala duk Bahaushen da suka gani sai su yi ta dukansa su zane shi, haka dai ba a kula su ba a ranar Talata daga nan sai suka debo zauna-gari-banza suka shiga Unguwar Hausawa suka yi ta kwashe mana dukiya suna sarar jama’a suna kone musu rumfuna da gidaje, amma yanzu mun gode Allah tunda kura ta lafa.”
Alhaji Mahmuda Madagali ya ce tun a ranar da rikicin ya yi kamari Mai alfarma Sarkin Musulmi da tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso suka kira shi suka jajanta musu tare da kwantar mausu da hankali.
Ya ce mai gidansa Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin ya ba su gagarumar gudunmawa wajen kwantar da rikicin. Sarkin Hausawan ya ce ya tabbatar da ganin gawarwaki uku na mutanen da aka kashe aka aje a kofar gidansa kafin a yi musu sutura kuma akwai wadansu mutum biyu da aka tsare a kan babur aka kashe su aka kone su da babur dinsu.
 Ya yi kira ga jama’a da su dauka wannan wata kaddara ce, don haka su yi hakuri su kuma guji daukar hukunci a hannunsu. Ya ce a baya ba a taba samun rikici makamancin haka ba a Ile-ife domin garin ya shahara da zaman lafiya.
Wani mazaunin garin da ake kira Malam Shehu ya shaida wa Aminiya cewa karancin jami’an tsaro ne da rashin zuwansu a kan kari ne ya tsananta rikicin, ya ce a kone Unguwar Hausawa ta Sabo Ile-Ife tare da tarin dukiyarsu na miliyoyin nairori . “Da bindigogi ’yan iskan suka shigo suna ta harbe-harbe, sun kashe akalla mutum takwas wadanda muka ga gawarsu ban da wadanda ke can a gefen gari, fatanmu shi ne a samu isassun jami’an tsaro musanmman ma sojoji,” inji shi.  
A baya dai Ile-Ife wadda cibiya ce ta cinikin goro daga Kudu zuwa Arewa ta shahara ta fuskar zaman lafiya a tsakanin kabilu daban-daban na garin.
A shekarun baya wadansu ’yan asalin garin Ile-Ife sun yi yunkurin korar Hausawa daga Unguwar Sabo bisa ikirarin cewa, unguwar baki dayanta mallakar kakanninsu ce. Marigayi Ooni na Ife, Oba Okunade Sijuwade shi ne ya kwantar da matsalar a wancan lokaci.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited