Aure a tsakanin dalibai: Ainihin abin da ya faru a sakandaren Bauchi
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Aure a tsakanin dalibai: Ainihin abin da ya faru a sakandaren Bauchi

Makarantar Sa’adu Zungur na daya daga cikin dadaddun makarantu masu tarihi a Jihar Bauchi, musamman a fagen kwazo da samun ilimi mai nagarta.
Sai dai abin da aka rika yadawa cewa ya faru a makon jiya na aukuwar wata fitsara da rashin tarbiyya a tsakanin daliban bangaren sakandare na makarantar da aka yi zargin sun yi bikin daura aure a tsakaninsu ba bisa ka’ida ba, ya jawo damuwa mai tsanani da ce-ce ku-ce a tsakanin jama’a.
Hakan ya sa Gwamnatin Jihar ta rufe makarantar, ta kuma kafa wani kwamitin da zai gudanar da bincike domin gano gaskiyar batun da kuma duk wasu miyagun dabi’u da ake zargin suna aukuwa a makarantar.
Labarin daurin auren dai wata majiya ta ce ya fara bayyana ne a shafin faceboo, lamarin da ya say a watsu kamar wutar daji.
A lokacin da wakilinmu ya tuntubi daya daga cikin malaman makarantar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa: “Gaskiyar abin da ya faru shi ne akwai wani aji na biyu na babbar sakandare da wani dalibi wanda yake da tsantseni kuma ba ya son kula mata ko magana ma ba ya yi da su, wanda hakan ya sa suke masa ganin Ustaz. Kimanin wata guda da ya wuce sai daliban suka yi wani abu kamar wasa a tsakaninsu, inda daya daga cikin daliban ajin ta ce ita fa Ustaz take so kuma yau sai an daura musu aure. Shi dai sai ya yi zugum bai ce komai ba, sai wadansu daga cikin daliban suka ce ai ba a yin aure sai da sadaki, sai ta ciro Naira 500 ta ce ga sadakinta, sai dalibai suka rika shewa suka karbi kudin suka je suka sayo cingam da minti suka raba wa ’yan uwansu suna yin raha.”
Malamin ya ce: “Sai daliban suka ce sun daura musu aure ana cikin haka sai wata daliba ta dauka a wayarta kuma ta jefa shi a yanar gizo, da mutane suka gani sai aka rika maganganu, har batun ya je kunnen Shugaban Makarantar wanda shi kuma bai yi wata- wata ba, ya dauki mataki a kai, inda ya kafa kwamitin bincike, kuma kwamitin binciken ya yi aikinsa ya mika rahoto inda cikin rahotonsa ya fadi bayanan da na yi muku.”
Ya ce da aka samu rahoton sai aka dakatar da daliban biyu saboda dukkansu sun amsa laifinsu, ya ce zai iya tunawa ma har yarinyar ta a kuka tana da na sani tana kuma zargin kanta da cewa ita ce ta jawo duk wannan fitina. Shi kuma Ustaz an hukunta shi ne saboda lokacin da abin ya faru bai fada wa hukumar makarantar ba.
Malamin ya ce gwamnati ta kafa kwamiti amma wadanda ake tambaya kan abin da ya faru, sai ana tambayar malaman firaramare ko na karamar sakandare da suke zaune tare a makarantar wadanda su kuma ba su ba da bayanin ainihin abin da ya faru domin ba su nan aka yi, su suna zuwa da safe ne yayin da su kuma daliban babbar sakandaren ke zuwa da rana.
Ya ce wani abin bakin ciki shi ne hoton dalibai da ake yadawa ta yanar gizo suna rawa ban a daliban makarantar ba ce, ya ce ko rigunan makaranta da ke jikinsu ba irin na makarantar ba ce sannan wajen da suke rawa babu irin wannan ajin a makarantar Sa’adu Zungiur.
Malamin ya ce wani abin da yake rura wutar rikicin kuma shi ne karan-tsana da wadansu daga cikin daraktocin Ma’aikatar Ilimi ke yi wa shugaban makarantan saboda gwamnatin da ta shude ce ta nada shi, saboda haka dama suna jirar wata dama ce yanzu kuma sun samu, shi ya sa suke kokarin ganin sai an cire shi kuma an kwashe malaman makarantar baki daya an musu sauyin wurin aiki.
Sai dai wadansu daga cikin malamai da daliban makarantar sun yi zargin cewa, dama can ana samun zarge-zarge na mu’amalar da ba ta dace ba a tsakanin samari da ’yan mata da ke makarantar dama wadansu makarantu a jihar, musamman a lokacin da aka tashi shan iska ko cin abinci a makaranta.
daliban sun ce duk da cewa a makarantar ajin dalibai mata da maza daban-daban ne, wani lokaci daliban sukan shirya aure ba bisa ka’ida ba a tsakaninsu, musamman a lokacin da aka tashi cin abinci, ko lokacin shan iska ko kuma in ana jarrabawa. Suka ce ana farawa ne da  auren wasa ne, inda dalibi zai biya sadakin Naira 150 ko 200 ko 500 don a daura musu aure da wata daliba kuma abokansu dalibai suke tara gudunmawar kudi su sayi abincin da abin da za a sha a wajen bikin.
Suka ce lokacin da Allah Ya tashi fallasa abin shi ne “Akwai wata rana da malamai suka ji shewa da hayaniya ta kaure a cikin makarantar kamar ana biki, sai suka garzaya wajen ajin da suka ji shewar. Lokacin da malamai suka je ajin da ake bikin sai suka tarar da wani dalibi ne dan ajin babban saita a babban sakandaren, wannan abu shi ya jawo rudani daga bisani kuma aka kai su ofishin Shugaban Makaranta.
Saboda girgiza da abin da ya faru Shugaban Makarantar sai ya kai rahoto Ma’aikatar Ilimi domin sanin irin horon da ya kamata a dauka a kan wadannan dalibai wanda hakan ya jawo Ma’aikatar Ilimin ta rufe makarantar baki daya,” inji wata majiyarmu.
A wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi kuma Kwamishinan Ilimi, Injiniya Nuhu Gidado ya ba da umarnin rufe makarantar firamare da sakandare na Sa’adu Zungur, kuma ya kafa kwamiti mai karfi da zai binciki alamarin.
Mataimakin Gwamnan ya kai ziyarar ba-zata a makarantar, saboda rahotanni biyu da ma’aikatar ta samu na zargin cewa sau biyu a karo daban-daban caliban makarantar suka daura a tsakanin junansu ba bisa ka’ida ba.
Sanarwar da Mai taimaka wa Mataimakin Gwamnan kan Harkokin Sadarwa, Yakubu Adamu ya sanya hannu a kai ta ce, “yin aure ba bisa ka’ida ba da daliban sakandaren ke yi, alama ce da ke barazana da nuna gurbacewar tarbiyya cikin al’umma.”
Sai ya sanar da cewa gwamnati ta rufe makarantar daga ranar Juma’a 10 ga Maris, kuma Kwamishinan ya ki amicewa da rahotannin kwamiti da a baya ya kafa domin ya binciki wannan zargi da ake yi,
Kwamishina Gidado, ya ce an kafa kwamiti mai karfin gaske in da ya umarci dukkan daraktocin Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Makarantar da Malaman Makarantar da kuma Wakilan kungiyar Iyaye da Malamai (PTA) su binciki wannan lamari da ya faru su kuma fito da rahoto na gaskiya kafin a bude makarantar.
Ya yi alkawarin hukunta duk wanda aka same shi da laifi kan wannan lamari, kuma ya yi alkawarin kawo karshen duk wani abu da zai iya gurbata tarbiyyar dalibai a makarantun jihar.
Jami’an Ma’aikatar Ilimi da na makarantar sun ki su ce uffan game da faruwar lamarin lokacin da wakilinmu ya tuntube su, inda suka ce ba za su ce komai ba sai bayan an kammala bincike, kuma a yanzu gwamnati ce kawai za ta iya magana kan batun.
Wani kwararre kan harkar ilimi Dokta Muhammad Sogiji ya shaida wa Aminiya cewa faruwar irin wannan lamari abin takaici ne, kuma akwai bukatar malaman makaranta da iyaye su kara kula da tarbiyyar yara.
Ya ce dole ne iyaye su rika ilimantar da ’ya’yansu hadarin kusatar jinsin maza ko mata idan sun girma, haka kuma a rika raba tsakanin yara mata da maza idan suka balaga. “Uwa-uba a makaranta kuma malamai su kara kokari wajen mai da makaranta gidan koyar da ilimi cike da tarbiyya,” inji shi.
Malamin ya ce abin da ke faruwa shi ne yanzu malamai na karantarwa amma wajen ba da tarbiyya ba kowane malami ne ke ba shi muhimmanci ba, ya ce matsalar ta al’umma ce gaba daya sai an hada hannu tukuna za a iya gyarawa.
Sai dai kuma gwamnati ta sake bude makarantar a wata sanarwa da ta fito daga ofsihin Mataimakin Gwamnan a shekaranjiya Laraba.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited