… Masu fatan mutuwa ga Buhari makiyan Najeriya ne – Damboa
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

… Masu fatan mutuwa ga Buhari makiyan Najeriya ne – Damboa

Alhaji Adam Shuwa Damboa wanda aka fi sani da Alhaji Adamu Damboa, yana daya daga cikin ’yan siyasar yankin Bwari a Birnin Tarayya, Abuja. A tattaunawarsa da Aminiya, ya ce wadanda suka yi wa Buhari fatan mutuwa lokacin da yake jinya a Ingila makiya Najeriya ne. Kuma ya ce ba Buhari ne ya kawo kuncin da Najeriya take ciki a yanzu ba: 

Aminiya: Bayan dawowar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kara sadaukar da kai wajen bauta wa ’yan Najeriya saboda kaunar da suka nuna masa. Me za ka ce kan haka?
Adamu Damboa: Alhamdulillah, a matsayina na dan siyasa wanda ya fara siyasa a 1979, kuma daya daga cikin masoya Shugaba Buhari, na ji dadin bayanin da ya yi. Maganar gyaran kasar nan, abu ne da sai mun koma baya. Tun ranar 27 ga Agustan 1985 da aka hambarar da gwamnatin soja ta Manjo Janar Muhammadu Buhari a daidai lokacin da kasar ta dauki turbar gyara tirya-tiryan, aka ce bai iya ba aka kwace mulki daga hannunsa, tun ranar aka fara ruguza kasar nan. Yau Allah Ya sa mutanen Najeriya sun hankalta sun sake dawowa sun ce sai shi.
Sai dai abin ban haushi da takaici, Buhari bai komo gadon mulki ba, sai da aka lalata komai a kasar nan. Ya dawo ne a lokacin da tsarin Jari-Hujja ya gama cin dunun kasar nan ta yadda, hatta maigadi ko mai shara, gwamnati ba ta daukarsa aiki kai-tsaye, sai dai a ba wani kusungurmin dan Jari-Hujja kwangila ana biyansa makudan kudi shi kuma yana dan sam masa. Kai talaka dan Najeriya kasar iyaye da kakanninka maimakon a dauke ka aiki a biya ka Naira dubu 50 zuwa dubu 70, sai dai a ba wani wannan kudi da sunan kwantaragi, ya rika biyanka Naira dubu 10 ko dubu 20. A wannan hali Shugaba Buhari ya dawo gadon mulki, an sace dukiyar kasa, an lalata kamfanoni da hukumomin gwamnati, an rugza masana’antu, an rusa tattalin arziki, an ruguza tsaro, komai yana lalace. Akwai bayanan da suka ce gwamnatin da Buhari ya karbi mulki daga hannunta ta shafe kusan wata takwas, tana ciwo bashi kafin ta iya biyan albashi a karshen mulkinta.
Gaskiya kasar nan a ganina ta yi lalacewar da sai mai kishi kasa irin Buhari ne kawai zai sadaukar da kansa wajen gudanar da mulkinta. Mun san Shugaba Buhari yana mulkin Najeriya ne saboda jama’a, saboda azzalumai da ’yan Mafiya da ’yan luwadi sun lalata ta. Sannan sun sanya mana kabilanci da bangaranci da rikicin addini domin kawar da hankulanmu daga irin tabargazar da suke tafkawa.
Dubi mu jihohin Borno da Yobe wadanda sansanin magoya bayan Shugaba Buhari ne, inda aka dasa mana wani bala’i wai Boko Haram. Wannan matsala ta Boko Haram, akwai hadin baki a tsakanin wadansu ’yan Najeriya da kasashen rainon Faransa domin a dakile hako man fetur da aka gano a yankin Arewa maso Gabas.
Aminiya: Me za ka ce kan wadanda suka yi ta fata Shugaba Buhari ya mutu ko suke cewa ya mutu a Ingila?
Adamu Damboa: Mun rika jin labarai iri-iri kan wannan mugun fata daga wadansu, hatta a cikin wadanda suke da’awar su Musulmi ne. Akwai ma wadanda aka ce sun ce sun sadaukar da dukiyarsu idan Buhari ya dawo Najeriya da rai. Irin wadannan mutane, makiya Najeriya ne, makiya jama’ar Najeriya ne. Kuma mai fatan Buhari ya mutu idan Buhari ya mutu, a tambaye shi, shin ubansa zai hau mulkin ne? Mutane sun manta cewa kafin zuwan Buhari barci ma yana neman gagarar jama’a, kowa na firgice kamar muna fagen daga. Mutum yana tsoron sanya jallabiya ko doguwar riga, mata na tsoron sanya hijabi. dan Arewa Kirista ma yana tsoron sanya doguwar riga. Domin a wurin mutumin Kudu, duk dan Arewa Hausa-Fulani ne, ba ruwansu da kai Bakatafe ne ko Banufe ko Babarbare ko Jukun ko kowane yare. Ba ruwansu da addininka, kai Hausa-Fulani ne, kuma kai dan Boko Haram ne. Abin da nake fata daga ’yan Arewa mu cire kabilanci da rikicin addini a tsakaninmu. Na sha fadi Allah ba zai zabi gonar Kirista ya yi masa ruwa Ya ware na Musulmi ba, kamar yadda ba zai zabi gonar Musulmi Ya ware ta Ya yi masa ruwa Ya hana gonar Kirista ba. Don haka wajibi ne mu mutanen Arewa mu tashi tsaye mu hada kai, mu bunkasa yankinmu mu guji fada da tashe-tashen hankula a tsakaninmu.  
Aminiya: Mutane suna kuka kan kuncin da ake ciki a kasar nan, tare da dora wa gwamnatin Buhari alhakin hakan, me za ka ce?
Adamu Damboa: Alhakin gyaran kasar nan ba yana kan Buhari ko gwamnatinsa kadai ba ne, aiki ne da ke kan kowanenmu. A ce Buhari kadai zai iya gyara bai taso ba. Mu taya shi da addu’a, kamar yadda muka yi ta yin addu’a ya dawo lafiya, alhamdu lillahi muna rokon Allah Ya kara masa lafiya. Su kuma azzalumai da kangararru da fandararru masu cewa, Buhari ya kawo yunwa, su tambayi kawunansu su dubi baya, za su ga ba Buhari ne ya kawo yunwa ba, ba gwamnatinsa ce ta kawo yunwa ko kunci ba. Mu ne za mu hadu mu gyara kasar nan, kowa ya koma ga neman halal, a guji tara dukiya ta haram. Yanzu mu dubi yadda talakawa masu neman na halal suke biyan kudin kujerar Hajji, a baya ’yan siyasa da barayin gwamnati ne ke mamaye kujerun su saye.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited