Masu yi wa Buhari mummunan fata su sake tunani - Akbishop Kaigama
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Masu yi wa Buhari mummunan fata su sake tunani - Akbishop Kaigama

Akbishop Ignatius Kaigama shi ne Akbishop din Cocin Katolika na Jos kuma shugaban Majalisar Bishop-Bishop din darikar Katolika ta Najeriya. A tattaunawarsa da wakilinmu kan dawowar Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga jinyar da ya tafi zuwa Ingila, ya yi kira ga masu yi wa Shugaban kasar mummunan fata su sake tunani, su dawo su ci gaba da yi masa addu’ar alheri, domin Allah ne Ya kawo shi don ya ceto Najeriya: Kuma ya yi kira ga Shugaba Buhari ya rika tantance shawarwarin da wadanda suke kusa da shi suke ba shi, kan shugabancin da yake gudanarwa:

 

Aminiya: Me za ka ce game da dawowar Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga jinyar da ya tafi a Ingila?
Akbishop Kaigama: Muna godiya ga Allah da Ya dawo mana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari gida lafiya, bayan jinyar da ya je. Shugaba Muhammadu Buhari shi ne Shugaban Najeriya kuma addininmu na Kirista ya nuna mana cewa mu rika yi wa shugabanni addu’a. Mu yi musu addu’a don su samu koshin lafiya, mu yi musu addu’a don Allah Ya ba su hikimar da za su gudanar da harkokin mulkin jama’a domin jama’ar su samu jin dadi da ci gaba. Ko mun so ko mun ki, Shugaba Buhari shi ne Shugaban Najeriya, don haka dole mu yi masa addu’a dole ne mu yi masa fatan alheri. Dalilin haka duk masu tunani, ba za su yiwa Shugaban kasa mummunan fata ba. Za su yi masa fatan alheri da addu’ar Allah Ya ba shi lafiya.
Idan Shugaban kasa ya yi rashin lafiya dole  mu damu, dole mu sunkuya mu durkusa mu daga hannu sama mu yi masa addu’a mu roki Allah Ya ba shi lafiya. Dukkanmu za mu iya fadawa cikin ciwo mu yi rashin lafiya.
Aminiya: To me za ka ce kan maganganun da wadansu suka yi ta yi kan rashin lafiyar da Shugaban kasa ya yi?
Akbishop Kaigama: A gaskiya na yi matukar bakin ciki kan yadda na ji wadansu ’yan Najeriya suna cewa Shugaban kasa ya zauna a wajen jinyar da ya tafi,  ko kuma suna cewa ya mutu a can.  Masu irin wadannan maganganu mutane ne wadanda za mu iya cewa ba masu hankali ba ne. Kuma ina jin ba cikakkun masu bin addini  ba ne. Kamar yadda na fadi shugaba, shugaba ne kuma Allah ne Ya nufa mu samu shugaban da zai ceto kasar nan, wannan Shugaban kuwa shi ne Shugaba Muhammadu Buhari. Ko mutum yana sonsa ko ba ya sonsa shi ne Shugaban Najeriya. Don haka hada kai za mu yi, mu ba shi cikakken goyon baya da hadin kai. Saboda haka ina kira ga masu yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari mummunan fata su sake tunani. Domin duk dan Adam da yake cikin damuwa ya cancanci a taimaka masa. Balle kuma a ce Shugaban kasarmu baki daya.
To, ina irin wadannan mutane masu yi wa Shugaban kasa mummunar fata suke?  Ga shi Allah bai karbi mummunan fatansu ba. Maimakon haka Allah Ya ba shi lafiya ya dawo gida Najeriya, zai ci gaba da gudanar da mulkinsa. Muna fata Allah Ya kara masa koshin lafiya, Ya taimake shi ya ci nasara a cikin mulkinsa. Kuma yadda mutane suke cikin wahala muna fata Shugaban kasa ya nemi hanyoyin da zai magance wadannan matsaloli.
Aminiya: Wadanne shawarwari ne za ka bai wa Shugaban kasar kan yadda yake gudanar da shugabancin kasar nan?
Akbishop Kaigama: Ya ci gaba da aiki da tsoron Allah kuma ya rika sauraron jama’a kuma ya tabbatar cewa a cikin sha’anin gudanar da mulki akwai masu son Shugaban akwai kuma wadanda ba sa sonsa. Kada ya damu da wannan, ya ci gaba da gudanar da aikinsa tsakani da Allah. Wadansu ’yan Najeriya suna nuna damuwarsu cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari Musulmi ne, don haka yana son ya mayar da Najeriya kasar Musulmi, wannan ba abin da muka san Shugaba Buhari da shi ba ne.
Domin tun kafin ya zama Shugaban Najeriya mu shugabannin darikar Katolika na Najeriya, mun yi zama da shi a Abuja mun tattauna da shi. Kuma bayan da ya zama Shugaban NAjeriya mun same shi mun yi zama da shi, kuma bai nuna mana yana da irin wannan tunani ba. Don haka muna kira ga irin wadannan mutane kada su ji tsoro domin Shugaba Buhari ya zo ne domin ya shugabanci dukan al’ummar Najeriya, Musulmi da Kirista da masu bin addinin gargajiya.
Bayan haka, Shawarwarina ga Shugaban kasa su ne ya natsu ya bude idanunsa da kunnuwansa domin ya ga abubuwan da suke faruwa da jama’a, kuma ya ji abubuwan da jama’a suke fada, domin ya taimaki mutanen kasar nan. Domin mutane suna cikin wahalar yunwa da wahalar rashin kudi. Shugaban kasa ya lura da wadanda suke kusa da shi. Idan wadanda suke kusa da shi suka ba shi shawara ya tabbatar ya nemi shawarar wadansu na waje, kafin ya yi amfani da shawarar da wadanda suke kusa da shi suka ba shi. Domin wani lokaci akwai son kai da son zuciya da siyasa a cikin shawarar da wadanda suke kusa da shi suke ba shi. Wani yana son kansa da iyalinsa da kabilarsa  ne kawai. Ina jin Shugaban kasa yana da basirar da zai iya gane irin wadannan masu ba shi shawara na kusa da shi. Ya bude idanunsa don ya ga wadanda suka iya aiki kuma suke da kwazo da zuciyar yin aiki don jama’a. Ya lura da wadanda suke son su kwashe dukiyar jama’a. Domin talakawan kasar nan suna cikin wahala. Amma idan aka ba da wani abu domin a taimake su sai ka ga wani ya je ya zauna a kan wannan abu. Akwai irin wadannan mutane suna nan a cikin wannan gwamnati ta Shugaba Buhari. Ba irin wadannan mutane muke so a cikin wannan gwamnati ba. Don haka ina kira ga Shugaban kasa ya sake duba wannan al’amari. Ya duba su wane ne suke aiki da tsoron Allah kuma su wane ne suke yi don su cinye dukiyar talakawa da aka ba su. Ba maganar wannan daga Arewa ko Kudu  ko daga wannan addini yake ba, ba zancen wadannan abokaina ne ba.
Aminiya: Mene ne sakonka ga al’ummar Najeriya?
Akbishop Kaigama: Mu ci gaba da yin hakuri duk da cewa muna cikin mawuyacin hali a kasar nan. Kuma mu dogara ga Allah, shugabanninmu su san cewa wannan amana da aka ba su, su yi abin da ya kamata. Mutane fa sun zabe su ne don su je su yi musu jagoranci nagari. Amma wadansu da dama sun manta da jama’ar da suka zabe su. Don haka ina kira ga shugabanni su rika gudanar da ayyukansu da gaskiya da tsoron Allah. Sauran al’ummar kasa kuma su zauna cikin tsoron Allah domin idan da Musulmi da Kirista muna bin abubuwan da addinanmu suka koyar, ba za mu ji ana kwashe kudaden jama’a da satar mutane da sauran miyagun abubuwa ba. Kowa ya tashi ya yi aiki tsakani da Allah. Kada mu zuba wa Shugaban kasa  ido shi kadai, mu ma mu tashi mu ba da tamu gudunmawar wajen gyara kasarmu Najeriya.  Mu ba Shugaban kasa goyon baya da hadin kai kada mu rika zancen kabila ko Arewa ko Kudu ko zancen addini.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited