Yaki da cin hanci: Rashin tabbatar da ni ba zai karya min gwiwa ba – Magu
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Yaki da cin hanci: Rashin tabbatar da ni ba zai karya min gwiwa ba – Magu

Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Malam Ibrahim Magu, ya ce rashin tabbatar da shi a kan mukaminsa ba zai karya masa gwiwa ba a yaki da almundahana da cin hanci da rashawa da yake yi.
Malam Ibrahim Magu, ya bayyana haka ne a kofar Majalisar Dokoki ta kasa a lokacin da yake ganawa da masu fafutikar kare hakkin dan Adam bayan an ki tabbatar da shi a kan mukaminsa, ya ce zai ci gaba da yakin ko an tabbatar da shi ko ba a tabbatar da shi ba.
Ya ce babu take hakkin dan Adam da ya kai cin hanci da rashawa, inda ya ce alhakin yaki da cin hanci da rashawar ya rataya ne a kan kowa da kowa.
Shugaban ya ce zarge-zargen da aka yi masa ba za a iya tabbatar da su ba, kuma ya ce ba a ba shi damar kare kansa ba.
A shekaranjiya Laraba, Majalisar Dattawa ta sake watsi da bukatar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari na neman tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin Shugaban Hukumar (EFCC) din. Wannan ne karo na biyu da majalisar ta ki amincewa da Magu a matsayin shugaban hukumar.
A yayin zaman majalisar, akasarin sanatoci sun ki yarda a tabbatar da Magu a matsayin ta hanyar kada kuri’a.
Majalisar ta ki tabbatar da Magu a kan mukamin ne bisa wani rahoton da Hukumar Tsaron kasa (DSS), ta bayar a kansa.
Sai dai tsohon Shugaban Masu Rinjaye na Majalaisar, Sanata Ali Ndume ya nuna rashin jin dadi da kin tabbatar da Magu, inda ya ce majalisar ta karbi wasiku biyu masu karo da juna a kansa. Ya dai amince cewa mafiya rinjaye ke da galaba, amma duk da haka akwai bukatar a saurari marasa rinjaye.
Sanata Ali Ndume, ya kuma ce majalisar ba ta da hurumin cire Magu daga mukaminsa saboda babu dokar da ta hana Shugaban kasa ba wa mutum aiki na riko kuma babu wa’adin yaushe zai iya yin aiki a kan haka. Sanata Ndume ya ce Magu ya riga ya kare kansa kan dukan zarge-zargen da aka yi masa a cikin rahoton na DSS.
Shugaban Majalisar, Sanata Bukola Saraki ya ce: “Bai kamata mu tozarta daukacin hukuma ba, saboda wani mutum guda.” Yana nufin ba za su yi watsi da rahoton Hukumar DSS domin wanke Magu ba. Kuma a lokacin rufe sauraren bahasin, Sanata Saraki ya ce, daga yanzu Magu ya rasa kujerarsa ta mukaddasancin shugabancin hukumar. Sai ya bukaci Shugaban kasa ya tura sunan wani don maye shi.
Fadar Shugaban kasa ta ki cewa komai a kan batun lokacin da aka tuntube ta a shekaranjiya Laraba, kan mataki na gaba da Shugaban kasa zai dauka ganin an ki amincewa da Magu har sau biyu. Kakakin Shugaban kasa Femi Adesina ya shaida wa wakilinmu cewa ba ya da wani bayani da zai iya yi a kan batun.
Tun farko a jawabinsa gaban majalisar Magu ya ce: “Na dauki matakan kawo sababbin dabarun yaki da cin hanci da almundahana. Kuma muna duba hanyoyin sake fasalin hukumar ta hanyar fadada aikinta zuwa Ibadan da Maiduguri da inganta ma’aikatanta.”
Mataimakin Shugaban Majalisar, Ike Ekweremadu ya yi masa tambayoyi kan dalilan da suka sa Hukumar EFCC ke kin bin umarnin kotuna da tauye hakkin jama’a da yadda EFCC a karkashinsa za ta yi yaki da cin hanci. Sannan Sanata Atai Aidoko ya tambaye shi kan hanyoyin gudanar da aiki na hukumar wajen tsare wadanda ake bincika a karkashinsa. Ya ce, yayin da Magu ya ce wani dan rajin kare hakkin ya ce wurin tsare mutane na EFCC kamar otel ne kuma ana jin dadi sosai, amma rahoton Hukumar DSS, ya yi da’awar bai kamata a zuba ido kan gallaza wa wadanda ake zargi a hannun EFCC ba.
Wasikar da Hukumar DSS ta aike wa majalisar dai bayan dogon bayani, ta ce: “Lura da abubuwan da suka gabata, Magu ya gaza a fannin gaskiya da rikon amana.”
Game da zargin da ake yi kan gidan da ya saya ba tare da bin ka’ida ba, Magu ya ce, ya zauna ne kawai a gidan saboda kusancinsa da wurin aikinsa tare da kauce wa fita cikin dare.
Sanatocin sun kuma tambayi Magu ya bayyana abin da ya gano a binciken da hukumar ta yi kan kudin bashin Kulob Paris da aka mayar wa jihohi da kuma nawa hukumar ta kwato zuwa yanzu.
A amsar da ya bayar, Magu ya ce, “Yana da wuya ka bayar da rahoto kan nawa aka kwato a shirin yaki da cin hancin.” Kuma ya ce duk da cewa ba koyaushe EFCC ke yin daidai a ayyukanta ba, amma hukumar tana bakin kokari wajen yin abin da ya dace.
A watan Disamban bara, majalisar ta ki amincewa da Magu a matsayin Shugaban Hukumar EFCC bayan da ta ce rahoton sirri, bai amince a tabbatar masa da wannan mukami ba, don haka ta bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya zabo shi ya hanzarta musanya shi da wani.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited