✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

Saura kiris ta zama bazawaratin! Wani saurayi ne ya yi amarya, bayan kwana biyu suka gamu da abokansa, suka tambaye shi “Ango yaya amarya?” Sai…

Saura kiris ta zama bazawaratin!

Wani saurayi ne ya yi amarya, bayan kwana biyu suka gamu da abokansa, suka tambaye shi “Ango yaya amarya?” Sai ya ce “Kai ai ana cewa mata tara suke ba su cika goma ba, to ni tawa matar ta cika goma cif, domin ita muslimatin ce, muminatin, kanitatin, sadikatin, sa’imatin kai har zuwa karshe.” Sai suka ce  “Kai ango ka yi sa’a, Allah Ya ba da zaman lafiya.” Bayan ’yan watanni sai suka hadu da abokan nan, sai suka ce “Ango yaya muslimatin?” Sai ya ce “Ai yanzu ta zama muguwatin, munafukatin, kazamiyatin, makiratin, shegiyatin, azzalumatin.” Kuma saura kiris ta zama bazawaratin!

 

Ai Bega ne ba su hura ba!

Wani ne ya je rugar wadansu Fulani a kusa da birnin Abuja da hantsi domin yin wata harka. Yana zuwa ya yi sallama sai ya ga Bafulatanin da ya je wurinsa ya fito daga bukka ko Sallar Asuba bai yi ba. Sai ya ce yaya na ga kamar ba ka yi Sallah ba? Sai Fullo ya ce, “Ai Bega ne ba su hura abin nasu ba. (Yana nufin ba su kunna wata na’urarsu da take kara duk safiya ba).”

 

Ni ne mai yin shuuu din nan!

Wata rana da misalin karfe biyu na dare, ’yan sanda suka kama wani mai shaye-shaye yana yawon dare, sai suka tambaye shi “Kai daga ina ka fito? Kuma ina za ka? Sai ya ce “Gidan rediyo za shi, suka ce wane irin aiki kake yi a gidan rediyo sai da kowa ya kwanta za ka je?” Sai ya ce “Ni ne mai yin shu-shu-shu din nan da rediyo ke yi bayan masu labarai sun tashi!”

Labari daga  09092969381

 

Duk abin da zai faru ya faru!

Wata budurwa ce tana tallar zogale da kuli-kuli daga kauye ta shiga birni, ta zo hucewa ta majalisar samari,sai suka kira ta suka saya, har ta yi gaba sai wani ya ce ni fa sai na tsokani mai zogalen can. Sai ya ce mai zogale! Tana juyowa sai ya ce I Lobe You! Sai ta zaci zaginta ya yi, ta dawo da sauri ta sauke tallar ta cire dankwali ta yi damara ta ce to ni ma I Lobe You din, duk abin da zai faru ya faru! 

Daga 09099886988