Ba zan tsaya takara da Buhari a 2019 ba – Tinubu
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Ba zan tsaya takara da Buhari a 2019 ba – Tinubu

Asiwaju-Bola-Ahmed-TinubuJagoran Jam’iyyar APC ta Qasa Asiwaju Bola Tinubu ya ce ba ya da niyyar tsayawa takara tare da Shugaban Qasa Muhammadu Buhari kuma ba zai goya wa wanda zai nemi haka a Jam’iyyar APC a zaven shekarar 2019 ba.

Sanata Bola Tinubu ya kuma yi fatali da labaran qarya da kafafen watsa labarai suke yaxawa cewa yana shirin tsayawa takara a zaven na shekarar 2019.
Tsohon Gwamnan na Jihar Legas ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai tallafa masa kan harkokin watsa labarai Mista Tunde Rahman ya raba wa manema labarai a ranar Talatar da ta gabata.
Ya ce: “Wannan shirme zai faxi, Asiwaju yana goyon baya tare da tsayuwa a bayan Shugaban Qasa Muhammadu Buhari. Yana yi wa Shugaban Qasa fatan samun lafiya ta yadda zai dawo cikin sauri. Ya alla Shugaban Qasa yana nan ko yana waje, yana da cikakken goyon bayan Asiwaju Tinubu. Buhari yana da tabbaci a kan haka. Asiwaju Tinubu ba zai tava yin takara tare da shi ba, kuma ba zai goya wa wani baya ya yi haka ba.”
Tinubu ya soki wata jarida kan da’awar da ta yi cewa ya yi watsi da shirinsa na haxa hannu da jam’iyyar adawa ta PDP domin kafa babbar jam’iyya da za ta fuskanci APC a zaven 2019.
Ya ce bai tava shirin shiga PDP ba, wadda ya yaqe ta a tsawon shekara 16.
Sanarwar ta qara da cewa: “Kanun labarin kansa vata sunan Asiwaju ne ta hanyar zargin zai shiga PDP. Wannan abin kunya ne kuma qarya ce. Asiwaju uba ne qwararre kuma jigo ne na gudanar da APC. Rashin hankali ne a ce zai bar jam’iyyar da ya wahala wajen kafa ta domin ya shiga PDP da take rugujewa.”
Bola Tinubu ya ce, shi ba karuwan siyasa ba ne da zai riqa tsalle-tsalle daga wannan jam’iyya zuwa waccan, inda ya ce zai ci gaba da kasancewa xan jam’iyya mai biyayya.
Ya ce masu muguwar manufa sun jirkita bayaninsa a wurin rantsar da Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu a ranar Juma’ar da ta gabata. Ya ce abin da ya ce, shi ne yana da shirin wata rana zai fito takarar muqami da rashin samun gurbin a Fadar Shugaban Qasa. Sanarwar ta ce, duk waxanda suka saurari kalamansa babu inda ya ambaci muqamin da zai tsaya takara ko kuma lokacin tsayawar. Kuma sharaxin da ya gindaya na iya xaukar shekaru kafin ya cika.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited