Musulmin ’yan kwallon da ke buga gasar firimiyar Ingila (1)
Tuesday 27 June 2017     2 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Musulmin ’yan kwallon da ke buga gasar firimiyar Ingila (1)

Gasar firimiyar Ingila da ake mata lakabi da English Prmier League EPL) tana da armashi. Bincike ya nuna ita ce gasar da masoya kwallon kafa suka fi kallo a duk fadin duniya ciki har da Nahiyar Afirka da kuma gida Najeriya.  Akan haka ne wakilinmu ya ci karo da wani bayani da ya zakulo ’yan kwallo 54 da Musulmi ne kuma suka buga gasar a kakar wasa ta bana. Bincike ya nuna ana samu karuwar ’yan kwallo da suka kasance Musulmi ne da ke yin tururuwar zuwa Ingila don yin kwallo a gasar firimiya.  Akan haka ne wakilinmu ya ci karo da ’yan kwallo 54 da Musulmi ne kuma suke yin kwallo a gasar. Muna fata makaranta Aminiya musamman na wannan shafin wasanni za su karu da wannan bincike da muka yi.  A sha karatu lafiya:

 

1.  Mesut Ozil:  Ozil da yanzu haka yake buga wa kulob din Arsenal na Ingila kwallo,  an tabbatar Musulmi ne.  Ya taba zuwa aikin Hajji don sauke farali, kuma dan kwallo ne da aka shaide shi wajen daga hannuwansa sama yana addu’a kafin a fara wasa.
2.    Granit dhaka:  dan kimanin shekara 24 dan asalin Switzerland ne, yana kwallo ne a kulob din Arsenal na Ingila kwallo, shi ma Musulmi ne.
3.    Ismael Bennacer:  Shi ma Musulmi ne da ya fito daga kasar Aljeriya inda yake buga wa kulob din Arsenal kwallo.  dan kimanin shekara 19, kulob din Arsenal ya tura shi wani kulob da ke Faransa mai suna Tours a matsayin aro:
4. Mohammed Nasir Elsayed Elneny:  Yanzu haka yana da shekara 24 kuma dan asalin Masar ne.  Shi ma Musulmi ne da ke buga wa kulob din Arsenal kwallo.
5. Shkodran Mustafi:  dan shekara 24, ya fito ne daga Jamus.  Shi ma yana buga wa kulob din Arsenal na Ingila kwallo, Musulmi ne.
6. Yaya Sonogo: dan asalin Faransa da yanzu haka yake buga wa kulob din Arsenal, shi ma Musulmi ne.
7.    Lewis Grabban:  dan asalin Jamaika, yanzu haka yana buga kwallo ne a kulob din Reading na Ingila ne daga  Bournemout bayan sun bayar da shi a matsayin aro.  Shi ma Musulmi ne.
8. Asmir Begobic dan asalin Bosnia, gola ne a kulob din Chelsea.  Yanzu haka shekarunsa 29 kuma shi ma Musulmi ne.
9. Eden Hazard, mai kimanin shekara 25 dan asalin Beljiyam, yanzu haka yana haskakawa a kulob din Chelsea, shi ma Musulmin dan kwallo ne.
10. Kurt Zouma, dan asalin Faransa, mai kimanin shekara 24, yanzu haka yana buga wa kulob din Chelsea ne a Ingila, kuma shi ma Musulmi ne.
11. N’golo Kante: dan kwallon tsakiya a kulob din Faransa, yanzu haka yana buga wa kulob din Chelsea kwallo, shi ma Musulmi ne.
12. Bakary Sako, dan asalin Mali da ya canza kasa ya koma Faransa, yanzu haka yana buga wa kulob din Crystal Palace na Ingila kwallo, shi ma Musulmi ne kuma yana da shekara 28 da haihuwa.
13. Arouna Konte:  Mai kimanin shekara 32, yana buga wa kulob din Eberton kwallo ne a halin yanzu, kuma shi ma Musulmi ne.  dan asalin Kwaddebuwa.
14.  Idrissa Gana Gueye:  Shi ma dan asalin Senegal dan kimanin shekara 26, yanzu haka yana kwallo ne a kulob din Eberton na Ingila, shi ma Musulmi ne
15. Muhammed Besic:  dan asalin Bosnia da ya canza asali zuwa Jamus, dan kimanin shekara 23, yanzu haka yana yi wa kulob din Eberton kwallo ne, shi ma Musulmi ne.
16.    Oumar Niasse:  dan asalin Senegal, yana da shekara 24, shi ma dan kwallon Eberton ne kuma Musulmi.
17.     Yannick Bolasie, shi ma dan kwallon Eberton da ya fito daga Kongo, Musulmi ne.
18.    Ahmed Elmohamody dan kwallon Hull City ya fito ne daga Masar.  dan shekara 28, Musulmi ne.
19. Adama Diomande, dan asalin Norway shi ma dan kwallo ne a kulob din Hull City.  Shi ma Musulmi ne.
20. Ahmed Musa:  Haifaffen Najeriya da yanzu haka yake buga wa kulob din Leicesty City na Ingila, yanzu haka yana da shekara 23 shi ma Musulmi ne.
21. Islam Slimani:  dan asalin Aljeriya, shi ma Musulmi ne da yanzu haka yake buga kwallo a kulob din Leicesty City na Ingila
22.    Riyad Mahrez:  dan kimanin shekara 25 dam asalin Aljeriya, shi ma Musulmin dan kwallon ne da ke buga wa kulob din Leicester City na Ingila.
23. Emre Can:  dan asalin  Jamus dan kimanin shekara 22, yanzu haka yana buga wa kulob din Liberpool kwallo, shi ma Musulmi ne.
24. Mamadou Sakho dan asalin Faransa, dan shekara 26 yanzu haka yana buga wa kulob din Liberpool kwallo, shi ma Musulmi ne.
25. Sadio Mane:  dan asalin Senegal, yana da shekara 24 kuma yanzu haka yana yi wa kulob din Liberpool kwallo, shi ma Musulmi ne.
26. Bacary Sagna:  dan kimanin shekara 33 dan asalin Faransa, yanzu haka yana buga kwallo ne a kulob din Manchester City na Ingila, shi ma Musulmi ne.

Za mu cigaba

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited