An kashe dan uwan Marcos Rojo na Manchester United
Tuesday 27 June 2017     2 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

An kashe dan uwan Marcos Rojo na Manchester United

A ranar Lahadin da ta wuce ne aka samu rahoto daga Ajantina yadda wani jami’in tsaro ya kashe Geronino Rojo, dan uwan Marcos Rojo da ke buga kwallo a kulob din Manchester United da ke Ingila tare da wani abokinsa mai suna Barbosa.
Rahoton ya ce, Geronino dan kimanin shekara 17 ya gamu da alajinsa ne tare da wani abokinsa dan kimanin shekara 26 mai suna Barbora bayan sun yi yunkurin yi wa wani tsohon jami’in dan sanda fashi a kusa da wani banki.
Kamar yadda jaridar The Sun ta Ingila ta kalato, ta ce matasan sun yi yunkurin yi wa tsohon jami’in dan sanda dan kimanin shekara 26 Raul Anibal fashi ne da misalin karfe 10 na dare agogon Najeriya a lokacin da suke kan babur inda suka yi yunkurin fisge kudin da ya ciro daga na’urar cire kudi (ATM) a wani banki shi kuma ya shammace su inda ya zaro bindiga a aljihunsa kuma nan take ya bude musu wuta suka zube kasa warwas.
Nan take Barbora ya ce ga garinku yayin da Geronino kuma ya rasu bayan an garzaya da shi asibiti.
Tuni jami’an ’yan sanda suka tabbatar da aukuwar lamarin kuma sun ce suna cigaba da yin bincike.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited