An cafke wanda ya yi kutse cikin fili a lokacin wasan Pillars
Tuesday 27 June 2017     2 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

An cafke wanda ya yi kutse cikin fili a lokacin wasan Pillars

Kwamitin tsaro na magoya bayan kungiyar  Wasan kwallon kafa ta Kano Pillars ta cafke wani mutum mai suna Ibrahim Muhammad Panshekara bisa
yin kutse cikin filin wasa da ya yi a daidai lokacin da kungiyar ta Pillars ke buga wasa da takwararta ta Enyimba a ci gaba da wasan ajin kwararru na kasa wanda aka buga a ranar Lahadin da ta gabata a filin wasanni na Sani Abacha da ke Kano.
A wannan wasa dai kungiyar Wasan kwallon kafa ta Kano Pillars ce ta lallasa takwararta ta Enyimba da ci uku da  daya. Tunda farko dan wasa Kabiru Balogun ne ya sanya wa kungiyar kwallo guda biyu yayin daga baya Gambo Mohammed ya sama mata kwallo a uku a mintuna 92 da aka
dauka ana gudnaar da wasan. Ibrahim Bello Panshekara ya yi wa filin wasan tsinke ne a daidai lokacin da Gambo Mohammed ya ci wa kungiyar kwallo na uku.
A cewar Kakakin kungiyar ta Kano Pillars Lurwanu Idris Malikawa, tuni aka danka mutumin ga rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano, haka kuma a cewarsa Hukumar Pillars za ta tabbatar da an gurfanar da mutumin gaban kuliya don ya zama darasi ga saura. Malikawa ya yi kira ga magoya bayan Pillars da su kasance masu bin doka da oda a duk lokacin da kungiyar ke wasa a gida ko a wajen jihar.
Malikawa ya jaddada cewa hukumar ta Pillars ba za ta nade hannu ta zura ido wasu marasa kishin kasa su ci gaba da bata sunan kungiyar da kuma Jihar Kano a idon duniya ba.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited