Tsohon dan kwallon Green Eagles yana cikin mawuyacin hali
Tuesday 27 June 2017     2 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Tsohon dan kwallon Green Eagles yana cikin mawuyacin hali

Rahotannin da ke fitowa sun nuna tsohon dan kwallon Green Eagles Kelechi Emeteole yana cikin mawuyacin hali bayan ya kamu da wata cuta da ake kyautata zaton kansa ce inda ta shafi makogoronsa da hakan ta sa ba ya iya yin magana ko cin abinci sosai.
Kelechi, wanda ya taba zama dan kungiyar kwallon kafa ta Green Eagles a shekarun baya, ya horar da kulob da dama a Najeriya da suka hada da Enyimba na Aba da Lobi Stars na Makurdi da Heartland na Owerri da El-Kanemi Warriors na Maiduguri da kuma Enugu Rangers na Enugu.
Kamar yadda mai dakinsa Lolo Emeteole ta shaida wa manema labarai, ta ce tun cikin watan Disambar 2015 ne mijinta ya kamu da wannan cuta da hakan ta sa yanzu ba ya iya yin magana ko cin abinci yadda ya dace sai da taimakon wata na’ura da aka makala masa a makogwaro.
Ta ce bayan sun ziyarci asibitoci da dama amma abin ba sauki sai suka yanke shawarar kai  shi wani asibiti a kasar waje, sai dai babbar matsalar ita ce ana bukatar a kashe Dala dubu 11 ne kwatankwacin Naira miliyan 5 da hakan ta sa suke neman taimakon gaggawa daga gwamnati musamman Hukumar NFF da kuma masu hannu da shuni.
Kelechi, wanda yake bin kulob da dama da ya horar basussukan albashi da alawus-alawus ya sha rubuta musu wasika game da kudinsa amma har yanzu shiru kake ji kamar an shuka dusa.
Sai dai wani rahoto ya ce Keneth Omerou dan kwallon Super Eagles da yanzu haka yake kwallo a kulob din Alayanspor na Turkiyya ya ba tsohon kocinsa Kelechi tallafin Naira miliyan biyu don a yi masa magani.  Kelechi dai ya horar da Omerou ne a kulob din Enugu Rangers da kuma El-Kanemi Warriors na Maiduguri kafin ya samu damar fita waje don yin kwallo.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited