Watakila Hukumar FA ta dage Marcos Rojo
Tuesday 27 June 2017     2 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Watakila Hukumar FA ta dage Marcos Rojo

Watakila Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta dage dan wasan baya a kulob din Manchester United Marcos Rojo bayan wani hoton bidiyo ya nuna yadda dan kwallon ya taka dan kwallon Chelsea Eden Hazard a yayin da yake kwance a kasa, a wasan da kulob din biyu suka yi a ranar Litinin da ta wuce a gasar cin kofin kalubale na Ingila (FA Cup).
Hoton bidiyon ya nuna yadda Rojo ya yi tsalle ya taka Hazard da ke kwance a kasa al’amarin da ake ganin ya yi ne da gangan ba bisa kuskure ba.  Hukumar za ta gudanar da cikakken bincike game da wannan al’amari, kuma idan ta same shi da laifi za ta ci tarar Rojo sannan ta dage shi daga yin wadansu wasanni akalla biyu zuwa biyar.
Idan za a tuna, dan kwallon gaba a kulob din Manchester United Zlatan Ibrahimobic an dage shi daga yin wasanni uku saboda ketar da ya yi wa wani dan kwallo a gasar firimiyar Ingila a makon jiya.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited