An fitar da Jadawalin Gasar Cin Kofin kalubale na Ingila
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

An fitar da Jadawalin Gasar Cin Kofin kalubale na Ingila

A ranar Litinin da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa ta Ingila ta fitar da Jadawalin wasan kusa da na karshe (semi-fainal) na gasar cin kofin kalubale da ake masa lakabi da FA Cup.
Kulob din Chelsea da ya doke na Manchester United da ci 1 mai ban haushi zai kara ne da na Tottenham a yayin da kulob din Arsenal kuma zai kece raini da na Manchester City a wasannin kusa da na karshe (Semi-Fainal).
Wasannin za su gudana ne a ranar 22 ga watan Afrilun 2017 inda daga nan ne za a tantance kungiyoyi biyu da za su kai matakin wasan karshe (Fainal).

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited