dan PSG ya kashe dan Barcelona saboda ya yi masa gwalo
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

dan PSG ya kashe dan Barcelona saboda ya yi masa gwalo

Wani abu mai kama da almara ya faru a kasar Gabon a karshen makon jiya bayan wani matashi dan kimanin shekara 18 da yake goyon bayan kulob din PSG na Faransa ya kashe abokinsa da ke goyon bayan FC Barcelona na Sifen ta hanyar daba masa wuka a makogwaro.
Rahoton da kafar watsa labarai ta UK Sun na Ingila ta kalato ya nuna cewa matasan abokan juna ne, kuma sun kalli yadda wasa ya kaya a tsakanin kulob din biyu ne a wani gidan kallon kwallo a ranar Larabar makon jiya a gasar cin kofin zakarun kulob na Turai (Champions League).
Jim kadan bayan an tashi daga wasan ne, bayan FC Barcelona ta fitar da PSG da ci 6-1 sai mai goya wa Barcelona baya ya rika yi wa abokinsa dan PSG dariya da kuma yi masa gwalo.  Hakan ce ta harzuka shi, inda nan take ya zaro wuka a kugunsa kuma ya daba wa abokinsa a wuya, inda nan take ya fadi kasa warwas inda kafin a garzaya da shi asibiti rai ya yi halinsa.
Daga nan ne jami’an ’yan sanda suka kama wanda ya yi kisan kuma suka ci gaba da yin bincike.  Sai dai wani rahoto ya ce matashin da ya yi kisan kan ya aikata haka ne bayan ya yi tatil da barasa.  Jami’an tsaro sun ce za su tasa keyar matashin zuwa kotu don a yanke masa hukunci idan sun kammala bincike.
Idan za a tuna, kulob din FC Barcelona dai ya fitar da na PSG daga gasar ce da ci 6-1 a wasa karo na biyu al’amarin da ya ba masoya kwallon kafa da dama mamaki.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited