Za a sallami Rohr idan bai haye da Super Eagles gasar cin kofin duniya ba – NFF
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Za a sallami Rohr idan bai haye da Super Eagles gasar cin kofin duniya ba – NFF

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta nanata cewa yarjejeniyar da ta kulla a tsakaninta da kocin kungiyar kwallon kafa na Super Eagles Gernot Rohr tana nan daram. A  kwamtaragin an nuna idan kocin bai haye da kungiyar zuwa gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za a yi a Rasha a shekarar 2018 ba, to aikinsa ya kare kuma ba za a sabunta masa kwantaragi ba.
NFF ta ce yarjejeniyar da kocin ya kulla da Super Eagles ta nuna idan bai haye da kungiyar gasar cin kofin duniya na 2018 ba, to aikinsa zai kare a kungiyar ba tare da wani ka-ce-na-ce ba.
Kawo yanzu dai kungiyar Super Eagles ce take saman teburi a rukunin B a jadawalin neman hayewa gasar cin kofin duniya bayan ta samu nasara a wasanni biyu da ta yi.
A ranar 28 ga watan Agusta, 2017 ne ake sa ran Super Eagles za ta kara da kasar Kamaru a filin wasa na Uyo da ke Akwa Ibom a cigaba da wasannin neman hayewa gasar cin kofin duniya.  Idan Najeriya ta samu nasara a wasan, za ta cigaba da jan ragamar teburin, amma idan Kamaru ce ta samu nasara ita ce za ta haye teburin da maki bakwai kenan yayin da Najeriya za ta kasance da maki 6.
Mai magana da yawun Super Eagles Toyin Ibitoye ya ce, abu ne mai matukar wahala a sabunta wa Rohr kwantaragi idan bai haye da Super Eagles gasar cin kofin duniya ba.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited