Yau za a yi jadawalin Kwata-Fainal a Gasar Zakarun Kulob na Turai
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Yau za a yi jadawalin Kwata-Fainal a Gasar Zakarun Kulob na Turai

A yau Juma’a ne za a gudanar da jadawalin wasannin Kwata-Fainal na Gasar Zakarun Kulob na Turai (Champions League).  Jadawalin zai gudana ne da misalin karfe 12 na rana agogon Najeriya a hedkwatar Hukumar UEFA da ke Nyon a Suwizilan.
kungiyoyi takwas ne za su fafata a wannan jadawali bayan sun kai wannan mataki.   kungiyoyin su ne Borussia Dortmund daga Jamus da Real Madrid daga Sifen da Bayern Munich daga Jamus da FC Barcelona daga Sifen.  Sai Leicester City na Ingila da Jubentus na Italiya da Monaco ta Faransa sai cikin na takwas Atletico Madrid na Sifen.
A jadawalin, kowace kungiya za ta iya haduwa da ’yar uwarta ba tare da an kebance ba, ma’ana ko da sun fito daga kasa daya ne.  Alal misali kulob din Real Madrid zai iya haduwa da na FC Barcelona a wannan mataki ko Borussia Dortmund za ta iya haduwa da Bayern Munich a wannan mataki da sauransu.
A ranakun 11 da 12 ga watan Afrilun 2017 ne za a gudanar da wasannin zagayen farko sai a yi wasanni zagaye na biyu a ranakun 18 da 19 ga watan Afrilun 2017 daga nan ne za a tantance kungiyoyi hudun da za su haye matakin kusa da na karshe (Semi-Fainal).
 Dubban masoya kwallon kafa ne ake sa ran za su kalli yadda jadawalin zai kaya a yau, a akwatunan talabijin da na yanar gizo a sassan duniya.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited