Mu ci gaba da yi wa Buhari addu’a
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Mu ci gaba da yi wa Buhari addu’a

Aminiya ina fata za ku ba ni fili domin in yi kira ga al’ummar Najeriya cewa ya wajaba mu ci gaba da yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’o’in alheri na Allah Ya ba shi ikon tafiyar da mulkin kasar nan lami lafiya tare da samun nasara kan kyawawan manufofinsa na dora kasar nan a kan turba ta kwarai.

Sannan mu yi ta yi masa addu’o’in Allah Ya yi maganin munafukan da ba su son kasar nan da suke yi masa zagon kasa. Sannan mu kara hakuri kan halin matsin da muke ciki, domin ba a rana daya Shugaba Buhari zai gyara komai ba, sannan a karshe muna rokon Allah Ya ba mu damina mai albarka a bana.
Daga Yusha’u Musa Katsina Alkalin ’Yan Fanteka, Mpape, Abuja. 08050441373

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited