Wayyo Talakan Najeriya!
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Wayyo Talakan Najeriya!

Edita, ina so ka ba ni fili don in yi tsokaci a kan halin da talakawan Najeriya ke ciki.  Talakan Najeriya yana cikin mawuyacin hali ne saboda rashin samun shugabanni na kwarai wadanda ba su da imani, ba su da tausayi kullum babu abin da suka sanya a gaba sai zalunci. 

An wayi gari a yau a Najeriya komai babu sauki kama daga kan kayayyakin masarufi zuwa na sufuri.  Ana cikin halin matsi kuma kwatsam sai ga karin kudin man fetur inda kayayyaki suka yi tashin gwauron zabo. Wayyo talakawan Najeriya!!!  Yanzu a kasar ban babu wutar lantarki, ba ruwan famfo, ba kudi, ba abinci, babu, babun ma sun yi yawa.  Sai dai ina kira ga ’yan kasa da mu dage da addu’a, Allah Ya fitar da mu daga cikin wannan kangi.  Kuna ni a nawa tunanin, yajin aiki ba shi ne mafita ba, don idan ma an shiga yajin aikin, matsalolin a kan talaka za su sake fadawa.  Allah Ya kawo mana mafita.
Sako daga Sadiya Me Sona  08036300751

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited