Saqonnin waya
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Saqonnin waya

Buhari bai kyauta ba

Edita, don Allah ka ba ni dama a wannan jarida ta Aminiya don na yi tsokaci a kan shugaban kasa Muhammadu Buhari.  Ya sani mu talakawa mun zabe shi ne don mu samu saukin rayuwa, ba don ya muzguna mana ba. Mun kori PDP ne daga mulki don mu samu sauki amma sai muka ga har yanzu abubuwa ba su canza ba.  
Daga Umar Walawa karamar Hukumar Mani ta Jihar Katsina 08033651479.

Karin kudin fetur bai dace ba

Edita ka ba ni dama in yi kira ga Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari cewa karin kudin mai bai dace ba a wannan lokaci musamman ganin yadda talaka ke cikin ukuba.  Da wanne zai ji, da karin kudin wuta, ko na abinci ko kuma na man fetur.  Ya sani talakawa suna cikin bala’i don haka a saukaka musu.  
Daga Bashmar D. Sabo.

Ina labarin Stella Odua?

Salam Edita, wai shin ina labarin Stella Odua, tsohuwar Ministar kula da jiragen sama musamman a kan tabargazar da ta takfa wajen yin sama da fadi da kudaden hukumar kula da jirgin sama.  Bai kamata a kyaleta ba ya kamata a hukunta ta.  
Daga Yahaya Ahmed Jabo, Apapa Legas 08128286038.

Ga karamin Ministan Fetur Kachikwu

Ina mamakin yadda karamin Ministan Albarkatun Man Fetur Kachikwu yake bada sanarwa mara dadi ga ’yan Najeriya.  Sau biyu kenan yake bayar da irin sanarwa mara dadi.  Abin tambaya a nan ita ce, shin ya fi kowane shugaba ne iya sanar da mummunan labari ga talakawan kasar nan.  Wayyo rayuwa ta yi wa talakan Najeriya zafi.  
Daga Muhammad Nazifi Adam a Kano.

Ga Manjo Al-Mustapha

Manjo Hamza Al-Mustapha na ji ka yi shiru game da shiga harkokin Najeriya, inda ka dauki lokaci mai tsawo ba tare da ka tofa albarkacin bakinka a game da gwamnati ba.  Don Allah kada ka yi fushi, kuma mai gaskiya yana tare da Allah.  
Daga Zuwaira Zariya 07067698970.

Neman karin bayani

Edita don Allah ina son a amsa mini wannan tambaya tawa:  Mene ne bambanci a tsakanin firaminista da shugaban kasa?  
Daga Tukur M. Sani Kwasara 08079572161.

Talakawa suna cikin tasku a Katsina

Salam, Edita don Allah Ka isar da sakona zuwa ga Gwamnatin Jihar Katsina cewa yaushe za ta motsa ne, talakawa sun fara gajiya da tsadar rayuwa.  Allah Ka dafawa Jihar Katsina da kuma Najeriya baki daya.  
Sako daga Mustapha Ibrahim Kahutu 08054666874.

Addu’a ga Aminiya

Edita ni mai karanta jaridar Aminiya ne mai farin jini, Ubangiji Allah Ya kare ku daga masharranta, amin.  
Daga Mista Molta Dickautal Maiduguri.
Martani ga Aminu Abdu Ba Ka Noma

Edita ina yi wa daukacin ma’aikatan jaridar Aminiya fatan alheri.  Da fatan kuna cikin koshin lafiya.  Ga martani ko amsa ga Aminu Abdu Ba Ka Noma da ya yi rubutu a jaridar Aminiya da ya yi a kan talakawan Najeriya da tsarin mulkin PMB.  Amsa ta farko, idan gaya muke so dole sai mun jure su ma masu yin gyaran sai sun jure.. Na biyu, hana hada-hadar Dalar Amurka ga ’yan kasuwa, dole sai da darajar kudi kasa take samun cigaba.  Uku, ka ce talakawa mun kosa, in dai mun jure za mu more.  
Daga danladi Abdulmumini Ba Ka Hutun Noma, Fulata, karamar Hukumar Maigatari, Jihar Jigawa.

Ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal

Kamar yadda ka yi kokari wajen biyan hakkokin tsofaffin ma’aikata da marayu da kuma malaman sakandare, ya dace ya duba halin da malaman firamare suke ciki don ganin ya biya musu hakkokinsu su ma.  
Daga Bello Garba Iya Shuni Mannir.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited