A dawo da Hukumar Kayyade Farashi
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

A dawo da Hukumar Kayyade Farashi

Edita, ina so ka ba ni dama a cikin jaridar Aminiya da muke yi wa take da “leka gidan kowa,” don in yi tsokaci a kan yadda farashin kayayyaki suke tashin gwauron zabo a kasar nan.

  Abin mamaki da takaici shi ne sai ka ga ka sayi abu da safe amma kafin rana ko maraice sai ka ji kudinsa ya karu.  A mafi yawan lokuta ba wani kwakkwaran dalilin yin wannan kari amma ’yan kasuwar kan ci karensu babu babbaka ne saboda rashin hukumar da za ta taka musu birki.  Kowa na yin abin da ya ga dama.
In ba haka ba, mai sayar da karas da albasa da kayan miya da wasu kayayyakin da a nan kasar ake yin su sai ya kara musu farashi, da ka tambaya sai ya ce maka wai Dala ce ta fadi.  Edita don Allah a taimaka a tambaye su me ya hada tashin Dala da wadannan kayayyaki da na lissafa?  Hausawa na cewa me ya hada biri da gada?
A ganina rashin samun wata hukuma da za ta rika sanya ido wajen sayar da kayayyaki a kasuwanninmu ne ya janyo haka.
A lokacin da Hukumar kayyade Farashi ta yi aiki, komai yana tafiya bisa ka’ida ne, kuma kafin a kara wa wani kaya farashi sai an bi ka’ida.  Hasali ma hukumar ce take sanar wa jama’a halin da kasuwa take ciki, ba daidaiku ba.
Don haka ina kira ga Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ta duba yiwuwar sake farfado da Hukumar kayyade Farashin Kayayyaki a kasar nan ko talakawa sa samu sa’ida.
Sako daga Usaina Ahmad Bauchi 07054133970 ko 09082368611

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited