Saqonnin waya
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Saqonnin waya

Yadda za a ceto PDP  

Tun bayan faduwar Jam’iyyar  PDP a zaben 2015 wasu jiga-jigan jam’iyyar suka sha alwashin farfado da martabarta a idon duniya.  An sha gudanar  da tarurruka na masu ruwa-da-tsaki a jam’iyyance don ganin an daidaita wajen samun sahihin shugaban da zai ciyar da jam’iyyar gaba.  Sai dai wasu na cewa taron yakan zama tamkar zaman shan shayi. Ana zauna ne kawai a yi hira a watse. Baya ga nan a kwanan baya,  an nada shugaban jam’iyyar na wucin-gadi,  wanda hakan ya dada haifar da ce-ce- ku- ce ga ‘ya’yan jam’iyyar a sassan kasar nan,  za mu iya cewa PDP za ta dawo da tagomashinta, amma idan ta gyara wasu kura-kurai da suka yi mata dabaibayi, wanda kuma da wuya hakan ta samu.  Abubuwan da ya kamata a ce ta gyara sun ne:
1. Daina kakaba wa mabiyanta shugabannin ko ’yan takarar dole,  musamman a jihohi da kananan hukumomi.
2. Daina amfani da wakilai (delegates) a matsayin wakilan zabe don su ne ummul haba’isin rusa jam’iyyar.
Da fatan shugabannin Jam’iyyar PDP za ku gyara saboda adawarku ta yi kyau.
Daga Mudassir Mai Shayi Bakin Tasha Ningi, Shugaban Muryar Talaka Reshen Ningi, Jihar Bauchi

A rika gina masana’antu

Salam Edita, don Allah ka ba ni fili don in yi tsokaci a kan rashin aikin yi da ke addabar mutanen kasarmu musamman matasa.  Da fatan masu hannu da shuni za su ba da gudunmawa wajen gina masana’antu manya da kanana.  Domin yin haka ne kadai zai samar wa jama’a dimbin aikin yi.  Sannan kafa masana’antu zai magance masu yawon maula wurin masu hannu da shuni a gida ko ofis ko wuraren kasuwanci ko wurin shakatawa. Wasu kuma idan suka je yawon maula idan ba a ba su ba sai su rika ci musu mutunci ta hanyar gaya musu bakaken maganganu.
 Saboda haka nake kira da a bai wa duk wani mai hannu da shuni shawara a duk inda yake ya bai wa jama’arsa  gudumawa ta hanyar samar da masana’anta. Kazalika masana’antun za su rika samar masu da kudaden shiga.
Da fatan Allah Ya ba su ikon yin haka.
Daga Haruna Muhammad Katsina, Shugaban Muryar Jama’a Reshen Jihar Katsina,  07039205659 07057491050

Gano ’yan matan Chibok nasara ce

Assalamu alaikum. Hakika gano wasu daga cikin ‘yan matan Chibok wata nasara ce babba a yunkurin sojoji da gwamnati na tabbatar da sun kubutar da ‘yan matan baki daya.  Wannan zai kara karfin gwiwa na tabbatar da samun nasarar dawo d a su baki daya.
Daga Hafizu Balarabe Gusau 07035304499

An yi watsi da ’yan gudun hijira

Don Allah Aminiya ina ‘yan kasuwarmu da masu hannu da shuni suka shige ne a Najeriya? Dubi irin bakar wahalar da ‘yan gudun hijirarmu suke ciki a Najeriya domin kuwa a gaskiya suna bukatar taimakon gaggawa, musamman al’ummar Jihar Borno da Yobe da kuma Adamawa, ganin yadda azumin watan Ramadan na kara kusantowa, amma an yi watsi da su.   
Ga zafi ga rana ga ruwan sama ga iska, an bar su a yashe.   Kai wallahi ba zan iya lissafa irin yanayin da ‘yan gudun hijirarmu suke ciki a daidai wannan lokacin ba.   Abin tausayi ma shi ne mata da kananan yara ne suke fi shan wuya.  Kai jama’a duk da Allah Ya azurtamu da manyan masu dukiya a wannan kasa tamu wadanda ba sai na kama suna ba, amma an bar su a cikin irin wannan yanayi an sa masu ido.
A karshe ina kara tunatar da gwamnatin Najeriya da na jihohi da na kananan hukumomi su dubi girman Allah domin tallafa wa wadannan bayin Allah a kan yanayin da suka samu kansu a ciki na rashin tabbas.
Daga Kwamared Sanin Shaga kofar kaura Katsina 08039433111

’Yan matan Chibok na raye

Salam Edita, samun biyu daga cikin ‘yan matan Chibok da aka yi, ya nuna har yanzu ‘yan matan na raye. Kuma wannan abin farin ciki ne ga iyaye da ‘yan uwan dukkan ’yan matan. Muna rokon Allah Ta’ala Ya bai wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari damar ceto su da kuma damka su ga iyayensu.
Daga Abdulmalik Sa’idu Mai Burodi Tashar Bagu Gusau. 08069807496

Kira ga Sarkin Daura

Zuwa ga Edita, bayan haka ina so a ba ni dama don in mika kukanmu ga Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk Umar, don ya kafa wa direboin mota dokar hana gudu a tsakanin titin GRA da Gurjiya.  Yadda direbobin ke tukin ganganci da kuma gudu a kan wannan hanya kan janyo asarar rayuwa da ta dukiya.  Za ka ga direba ya ware mota kamar yana hanyar Legas.  Na san Mai martaba ya fi ni sanin wannan hanya da nake fada don haka akwai bukatar ya kafa dokar don ganin an samu sauki.  Mun yi imani kai kadai za ka iya yi mana maganin wannan abu.
Daga Hadi Tsohon Sarki Daura  08148442241 ko 08085127726

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited